46

284 8 0
                                    

Koda suka Isa an amsheta inda Akai emergency da ita, yayin da hankalin As in yayi dubu ya tashi, gaba daya yana cikin wani matsanacin hali sai kaiwa da komowa yake, Zainab itama tunda suka zo take tsaye tana fargaban abunda zai faru, tausayin As dinne ya kamata kallo daya zaka mishi ka gane hankalinsa a tashe yake, Kuma a lokacin daya dauko Afrah taga tsabaragen son Afrah din a tattare dashi, tabbas yana son Afrah sosai....... Fitowan Dr yasa su duka biyun suka nufeshi inda Dr yace su bishi office koda suka je office din Dr ya musu umarnin zama, bayan sun zauna Dr ya kalli As yace shi waye dinta ne?? Yace mijinta ne and wannan Kuma sister dinta ce

Dr ya gyara glass din dake manne a idonsa yace matarka jininta yahau sosai, tana cikin damuwa, wanda mace mai ciki ba'a sonta cikin wannan hali na damuwa, na gano tana da damuwa saboda mugun hawan da jininta ya hau, sannan magana na biyu tayi miscarriage ma'ana cikin dake jikinta ya zube..... Aida sauri As ya tashi tare da fadin what?? Dr kana nufin cikin ya fita kenan

Dr yace eh sai dai zan baka shawara kuyi kokarin ganin ta fita daga halin da take ciki na damuwa, saboda gidan Hakan a nan gaba

Sannan zaku iya tafiya da ita nasa an Bata magani saiku kiyaye, fita sukayi su duka jiki a sanyaye As ko kallon Dakin da Afrah take baiyi ba yace ma Zainab taje ta fito da ita yana jiransu a waje, jiki a sanyaye ta nufi dakin inda ta samu Afrah din a zaune tana kuka wanda ba kukan komai take ba saina zubewan wannan cikin nata tayi bakin ciki matuka sai dai babu yanda ta iya kana naka Allah na nashi

Zainab ta dafata tare da fadin hakuri zakiyi Afrah..... Rungume Zainab tayi tare da fadin ina As yake??

Zainab tace yana waje yace inzo in fito dake yana jiranki, bata kuma cewa komai ba sai tashin da tayi domin su tafi, Zainab ta dauki ledan maganin suka fita, a haraban asibitin suka ganshi inda ake ajiye motoci suka shiga Afrah na gaba Zainab na baya, As ko kallonta baiyi ba yaja motar sukai gida

Bayan sun karasa yana faka motar bai jira komai ba ya fita inda ya nufi dakinsa cikin matsanancin bacin rai, Afrah binshi tayi da kallo jiki a sanyaye tare da fita itama tayi cikin gidan, Zainab Kam kasa fita tayi daga motar domin gaba daya jikinta yayi sanyi, tabbas tasan As Yana jin haushin Afrah sosai zama tayi a motar tana hawaye domin bata son shiga cikin gidan taji mai zai faru tsakaninsu, a hankali ta furta lallai aure kalubalansa nada yawa, sai yasa idan mutum yayi aure iyaye suke cemai sai yayi hakuri tabbas wannan shine hakurin dama aure ibada ne kuma ibada sai an jure, koda Afrah ba yar uwarta bace ba zata so ace yau tana gidan wasu ba taga mijinta na fushi da ita, balle ace yar uwarta ce

Afrah koda ta shiga dakin As din ta nufa domin ta rasa mai yasa yake fushi haka, ai ko ba komai ya kamata ya mata ya jiki, koda bai jajanta mata rashin da tayi ba duk da taga yana kokarin nuna mata ya fita son cikin, koda ta bude kofar ganinsa tayi a kwance yayi ruf da ciki

Nufansa tayi ta fara magana kaman haka haba banyi zaton haka daga gareka ba, nayi miscarriage har saida Akai mun wankin ciki Amma ko sannu babu kana......... Shut up ya furta cikin daga murya tare da fadin fitar mun a daki

Cikin firgici da tsoro tace bazan fita ba saika fadamun mai yasa kamun haka???

Tashi yayi ya nufeta Afrah Kam ganin idonsa ya kade yayi ja yasa gabanta ya fara fadi tare da kara rudewa....

Yace dalili kike son sani? Let me tell you Afrah bana son ganinki inda da hali da nasa ma zuciya ta tsanarki, Amma ina zuciyata taki mun adalci da tasa mun sonki Amma ina son ki sani daga rana irin ta yau zanyi kokarin in sama zuciyata tsananki, Afrah muninki nake gani maina miki haka? Ko Allah muna masa laifi ya yafe mana balle ke, sannan aurenki da nayi a haka karki mance tun kafin kizo duniya Allah ya tsara Hakan, ban isa in ketare abunda Allah ya tsara mun ba, Afrah kin cutar dani kin kuma tabbatar mun da bakya kaunata iya wannan ya isheni insan cewa inda zaki Samu dama zaki iya kasheni..... Cikin kuka take fadin Dan Allah ka daina fadin haka ka daina fushi dani akan abunda ban san na aikata ba..... Murmushi yayi tare da fadin saboda tunanin wancan arnen kin kasa samun nutsuwa duk da nayi miki alkawarin rabuwa da zarar kin haiyu Amma Hakan baiyi miki ba, saida kika yi abunda ya kuntata mun, kin kashe mun yaro..... Da sauri ta kalleshi tare da fadin what.....

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now