WUTA A MASAƘA

2.4K 87 8
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


WUTA A MASAƘA


Page 1




PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* Anda no WITA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

jinjina ta musamman ga

Swt Sisyna (Nanatou) Allah ya bar ƙauna.
Me gayya me aiki shugaba a bar koyi Safna Aliyu Jawabi.
Sa'adatu Abdullahi Madubi (My red)
Anty Asmy Jafar
Mummyna Nafisa Ummu ɗahira
Da dukkan membobin ƙungiyar perfect writer's association

Godiya ta musamman ga, iyayena ƙawayena 'yan uwa da abokan arziki, tare da masoyana a duk inda kuke a faɗin duniya.

Alhamdilillah, ina miƙa Godiya ta ga Ubangiji maɗaukakin sarki, yadda na fara a sa'a Allah yasa in gama a sa'a.


https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

Domin gyara, sharhi ko shawara
07063065680

_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, GASHI YA DIRA DA ZAFINSA, GAJEREN LABARINE ME TARIN ILIMANTARWA DA NISHAƊANTARWA KAFIN ZUWAN LITTAFIN RUƊUN ƘURUCIYA, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, BAZAN DINGA POSTING KULLUM BA, SANNAN BABU LALLAI IK DINGA DOGON PAGE, SANNAN DAN ALLAH BANDA BIYONI PC ANA DAGA FARKO, ZANYI IYA ƘOƘARINA INYI SHARING GROUPS, KUMA KU DINGA TAYANI SHARE PLEASE, COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE BUƘATA, GA WANDA BASU KARANTA LITTAFIN AƘIDATA BA, KARKU BARI A BAKU LABARI, KUZO IN BAKU PART1 KYAUTA KU SAI 2&3 AKAN FARASHI ME SAUƘI, TAKU HAR KULLUM AYSHERCOOL_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Da misalin ƙarfe goma na dare, Gari yayi shiru, wasu daga cikin al'umma sun adana kawunansu a cikin gidajensu, domin hutawa rayukansu hidindimun da akayi da Rana.

Sedai a ɓangare guda kuma sautin kiɗane ke tashi a wani ƙaton ɗakin taro, mutane nata shiga da fita kamar Rana, se kaiwa ake ana komowa da Abinci da abin sha kala kala, da gani base ka tambaya ba kasan bikine ake na masu hannu da shuni, duba da haɗuwa da tsaruwar ɗakin taron, da kuma kalar mutanen dake zarya a gurin, da uwa uba danƙara danƙaran motocin dake fake a harabar gurin taron.

Ango da amarya na kan high table suna kallon wanda suka halarci bikin nasu, Yayin da ƙawayen amarya da abokan ango, dangi 'yan uwa da abikan arziki keta cashewa a filin rawa, anata bajinta gurin zuba musu kuɗi, dj se ƙara zigasu yake suna ɓarin kuɗi yayin da matan keta cashewa.

MC ne ya fara magana ta speaker yace "Masha Allah, gaskiya na yadda wannan bikine na masu arziki, madalla ƙawayen amarya da abokan ango ina godiya da wannan bajinta da ku ka nuna, da kuma kara da ku ka yiwa Amarya da ango, sedai ana tsaka da wannan shagali na samu sanarwar, isowar wasu hamshaƙan jiga jigan baƙi da suka amsa gayyata domin tayamu nishaɗi a wannan biki na 'ya'yan gata, wannan baƙin ba kowanne bane face DJ Sultan, tare da 'yan tawagarsa na rawa, ciki hadda wannan tauraruwar taku, wadda ludayinta ke kan dawo, tauraruwarta ke haskawa a cikin manyan yara da suka yadda da kansu wajen iya cashewa, wato gimbiya Amira, nasani ga dukkan wanda suka saba zuwa guraren taron biki, birthday da makamantan su, da duk wanda yasan dj Sultan da tawagarsu nasan sun san wannan gimbiya, kai ga wanda bema santa ba yau ze santa, zatazo ta baje mana baiwarta ta nishaɗantar damu, ina fatan kuma zaku nuna mana farincikinku ta hanyar nuna bajintarku, DJ idan ka shirya, Sultan da jama'arka muna buƙatar ganinku akan stage"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now