47_48

662 42 0
                                    

Gaba ɗaya suka maida hankalinsu kanta, ta yunƙura zata bar falon amma abun yaci ƙarfinta, haka ta tsaya ta yi shi a falon.

"La'ila ha ilalla la, Muhammad rasulillah Sallallahu alaihi Wasallama, Imran me nake gani haka? Ba dai ciki ne da Yarinyar nan ba?"

Gaba ɗaya Imran ya dirirce yace 'Amm, mm dama, dama fa bata da lafiya Ammi, ba ta jin daɗi jiya har Asibiti muka je aka ce typhoid ne da ulcer ke damunta"

"Zan ɗura maka ashar ka kuma nema ka rainamin hankali, uwar typhoid ɗin da uban ulcer, kalli yadda yarinya ta ɗashe, tai haske amma kace min ulcer"

"Allah Ammi ba su cemin ta na da ciki ba"

"Rufemin baki, ni zaka rainawa hankali, wannan uban aman da tai ne za ka ce wai ma malaria ne, ka kyauta ds tsallake umarnina Imran, amma ka tabattar ka nemwa ɗan da zata haifa wata kakar ba ni ba, dan ba zan karɓi ɗan da ya fito daga tsatson karuwai ba, dan bani da tabbas na ka ne ko ba naka ba"

Duk da Amira na fama da kanta, dan a inda ta gama amana, ta kwanta akan kujera, gaba ɗaya jikinta yai sanyi, gaɓoɓin ta na mata ciwo, ga wani irin azababben ciwon kai da jiri da ke damunta.

Ihsan kuwa ɓangaren ta tayi da sauri, tana kuka yanzu Dagaske Amira ciki ne da ita, shikenan ta tabbata Imran ya zama nata, dan yadda yake ƙawazucin ta samu ciki ba ta samu b, Amira ta samu ze sake tattare wa ne a gurinta.

Nan ta sake jinjinawa ƙarya da rashin alƙawarin maza, yanzu duk daɗin bakin nan da yai ta mata, da alwashinsa akan ba ze kusanci Amira ba, katsam se aka haihu a ragaya, wai Amira da ciki.

Ta sake rushewa da kuka hadda sheshsheƙa.

Shikuwa Imran cigaba da lallaɓa Ammi yayi da rantse rantse, "Ammi dan Allah karki sheganta abunda take ɗauke da shi, wallahi Ammi Amira ba karuwa bace ba, na rantse miki"

"Eh tunda dama taje ta maka surkullen da zatayi dole ka zo gabana kana gayamin haka, kana nufin duk gantalin da ta dinga yi, har wasu garuruwan da'awa ta tafi ko jihadi? Ina ce nan hotunan ta suka dinga yawo tana rawar gala, wace 'yar mutuncin ce za tai abunda tayi?"

"Na sani Ammi, amma maraici ne da rashin gata ya sa ta tashi a haka, amma ba karuwa bace"

"Wallahi ka kuma cemin ba karuwa bace, zan zabga maka mari, shashasha dama tunda ka saki labule da ita ai dole ka faɗi haka, kar idan ka koma ta hanaka, ka kyautawa ranka, kuma bari in naka kashedi, billahilazi duk ranar da ka kuma dukar min yarinya saboda kilaki seta bar gidanka a ranar, kuma yanzu ma ba ƙyale ku nai ba, ba zan bari a haifi wannan cikin a gidan nan ba, dan ina tantama a kansa, ka bani mamaki ka bani kunya idan har kai ke da alhakin cikin nan Imran, kuma zan maka kashedi da gargaɗi idan harka kusakura ka canzawa Ihsan, ko kai mata wani abu mara daɗi naji labari, wallahi zamu gauraya da kai.

Ta juya ta nufi paet  ɗin Ihsan.

Da sauri Imran ya nufi in da Amira ke kwance, ke ta zubar da hawayw jiki ba ƙwari.

Ya sa hannu ya ɗagata cak ya shiga da ita parr ɗinta, a gurguje ya ɗakko duster ya goge aman, dan kar ma Ammi ta fito ta ganshi yana aikin aman da Amira tayi.

"Ihsan dan Allah ki dena wannan kukan, ki zuba ido zan ɗau tsatsuran mataki akansu, wannan cikin baza'a haife shi a gidan nan ba, ban taɓa tsammanin Imran ze kaucewa magana ta ba, yaje ya aikata abunda ya ga dama ba, amma kiyi haƙuri dan Allah"

Ihsan dai kasa magana tai, saboda batun cikin nan ya girgiza ta, Amma ta gama rarrashin ta, sannan ta tashi ta tafi, a harabar gidan ta tarar da Imran, yace "Ammi kin fito?"

"Bam sani ba, sakarai wanda ya rako maza duniya, har kake rawar kai akan karuwa, ka mari ƙanwarka Saboda ita, kake wulaƙanta matar da take sonka saboda Allah, nutsatstiya kamila duk saboda karuwa ko Imran? Ka kyauta nima ka saurari matakin da zan ɗauka, saboda gaza cika umarnin da na baka"

Ya sunkuyar da kai yai shiru, tayi ta gama sannan ta tafi.

Tana tafiya Imran ya koma part ɗin Amira da sauri, ya tarar tana nan in da ya kwantar da ita.

Da hanzari ya kulle ƙofar part ɗin ya haɗa ruwan zafi, ya cire mata kayan da tai aman a jiki, ya ɗauke ta zuwa banɗaki.

Wanka ya taya ta tayi, sannan ya kamo hannunta zuwa bedroom, ya zaunar da ita a bakin gado ya shiga share mata hawayenta yace "Amran, dan Allah ki dena kukan nan haka, insha Allah komai ze wuce, kinga Amm tazo ta ɗagamin hankali, ga rashin lafiyarki ga kuka kina yi, da wanne zanji? Dan Allah ki dena kuka Amira"

Ya dinga share mata hawaye, yaje fridge ya ɗakko tuffa, ya zauna ya yayanka mata ya bata, ya samu ta karɓa ta ci sosai.

Ya bata wasu kayan ta saka sannan ya rungumota zuwa mota.

Ihsan na jin ƙarara motar Imran, ta tashi da sauri ta leƙa, ga hango ya saka Amira a gaban motar sun fita.

Kuka ta fashe da shi tace "wallahi da ni kake zancen Imran, za ka gane ba ka da wayo, zaku ga abunda zan muku, daga kai har ita se na ga baya Wannan cikin, Allah ya isa tsakani na da kai Imran!"

Tai maganar tana dukan bango, ta zube ta cigaba da kuka a gurin.

Imran ya kalli Amira yace "Amran, ko Asibitin su Anty zamu?"

Amira tace "A'a"

'saboda me"

"Gaskiya kunya nake ji, kar inje cikin ne da gaske"

Imran yace "to da da wasa ne? Ai tun da kika ji Ammi ta faɗa cikin ne Amira, ni dai Allah ya tabattar"

Ajiyar zuciya tayi, ta tuno da kalaman Ammi, na ba zata karɓi duk wani jika da ga tsatson karuwa ba.

Gaba ɗaya jikinta yai sanyi, rai shiruu ba ta kuma cewa komai ba.

Wani Asibitin kuɗi sukaje, suka ga likita aka rubutawa Amira teses, Sedai sakamakon ya nuna tana ɗauke da juna biyu na watanni biyu.

Imran ya dinga washe baki yana murna, yace "Allah ya raba lafiya ya in ganta mana my Wife"

Murmushi tai kawai ta sunkuyar da kai, dan ba wani murna take da cikin ba, mussaman idan ta tuna da kalaman mahaifiyar Imran.

Aka basu magunguna, aka ƙara mata ruwa da allurai, sannan suka nufi gida

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now