7_8

644 46 1
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.



Afuwan banyi Editing ba

6_7




A gigice Abba ya farka daga baccin da yake cikin tashin hankali, mafarki yake da mahaifiyar Amira, ta riƙe rigarsa tana kuka akan ya temaka kar 'yarta ta lalace.

Ya dafe kansa yai shiru yana tunani, can ya miƙe yaje ya ɗakko wayarsa, ya nemo lambar Imran ya kirashi, sedai wayar taƙi shiga sam.

Ya duba lambar Ammi ya kirata, a ɗan firgice ta farka daga baccin, jin wayarta tana vibrating, ta duba screen ɗin wayar ta kalli agogo, dare yayi sosai ta ɗaga wayar tace "Hello, Abba lafiya kake kira a wannan daren haka?"

Abba yai ajiyar zuciya yace "ina Imran yake?"

Cikin Rashin fahimta tace "Imran kuma? Me Imran ze maka a wannan daren?"

"Ya kike tambayata ne? Yana nan ko baya nan?"

"Ai Imran tun safe ya koma Maiduguri, an masa kiran gaggawa"

"Yasalam"

"Amma Abba lafiya, nifa ka tayarmin da hankali"

Abba yace "Bari kawai, mafarki nayi da Zahra'u"

"Wace ce kuma Zahra'u?"

Abba yace "'yar uwata mana, nai mafarki da ita tana kuka, tana in kula mata da 'yarta karta lalace, na tsorata ƙwarai ina ga tunda Imran baya nan, ni zan dawo gari zanje inga meya kamata inyi akan yarinyar nan"

Ji tayi kamar ta zagi Abba dan takaici, a hasale tace "yanzun Dan Allah akam wannan abun ka nemi ka tayarmin da hankali, a wannan uban daren ina bacci? Mafarki ne fa kayi ba gaske ba, kawai ka ɗagamin hankali ka hanani bacci"

"Kinga ba kowane mafarki ne kawai ba, wannan mafarkin da nayi ba kawai bane, an nusar dani kuskure na ne ta mafarki, wanda yakamata in gyara tabbas"

"To yanzu me kake nufi?"

"Duk yadda ake ciki gobe in Allah ya kaimu zan dawo, zuwa jibi insha Allah zanje inga yarinyar nan da kaina, something is not wrong, seda Safe kawai"

Ya kashe wayarsa ya ajiye, ƙirjinsa na cigaba da bugawa da sauri da sauri, Ammi kuwa tsaki tayi, ta jefa wayar bayanta, tace "Aikin banza, kawai ze ɗagamin hankali akan wata banzar yarinya, sekace nina saka ta yawon banzan"

Tai tsaki ta juya ta cigaba da baccinta, tana takaicin Yadda Abba ya tashe ta ya ɗaga mata hankali a wannan Uban daren.

Ana idar da salar Asuba, Amira ta ƙarasa tattare duk abunda take buƙata tai waje, su Sadiya na kallonta amma ba wanda ya iya ce mata wsni abu, dan yadda tske cika tans batsewar nan, duk wanda ya tanka mata zata iya sauke masa rashin mutunci.
Haka ta fita zuwa Office ɗinsu na rawa, ta tarar dasu Sultan sun shirya tsaf, ana jiran mutum biyu, seda suka karya wajen ƙarfe goma sannan suka tafi airport.
Sultan yana kula da yadda Amiran bata walwala sam, yaso yai mata magana amma ya fasa, saboda wani lokacin halin Amira se a hankali, tana da sauƙin kai, amma bata fiye son a shiga lamuranta ba.

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now