53_54

1.3K 56 4
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

*_Assalamu alaikum warahmatullah, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukacin dangi na bisa ga rashi da mukayi na Kakana, ina fatan Ubangiji Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa. Ina miƙa saƙon godiya ta ga wanda suka kirani a waya, da wanda suka turamin saƙonnin ta'aziyya, na gani Nagode sosai Ubangiji Allah ya bar zumunci ya bada lada, Nagode sosai_*

53-54

Rawa jikin Amira ya fara yi, ta matsa gefe daga kusa da Yadikko tana bin ta da ido kamar ta ga wata aba daban.

Baba yace "dan Allah Amira kiyi haƙuri, ki yafewa mahaifiyata, tabbas nasan mun biye mata gurin muzgunawa rayuwarki da tsangwamar ki, wanda haka kakarki ta fuskanta daga gare mu zuwa mahaifinki da ke kanki, amma ban zaci Yadikko zata iya yi miki Aisiri haka ba, amma dan girman Allah ki yafewa Yadikko Amira"

Amira kam kasa magana tayi, se fashewa da wani irin kuka na tausayin kanta, Yadikko ta cutar da ita cuta me munin gaske, ba dan Allah ya temake ta ba da yanzu tana can tana hauka.

Imran da yake tsaye a bakin ƙofa ya ji komai, ya tako cikin ɗakin ya kalli Yadikko yace "da yawa abun da mu bayi ke mantawa da shi shine, ita duniyar ba matabbata bace ba, ita wadda ki kai kishin da ita yau tana ina? Shi wanda ki kai kishin akansa yana ina? Shi mahaifin Amiran shina da kika azabtar yana ina? Tunaninki ke kiyi gadin Duniyar kenan? Meye a cikin duniyar gaba ɗayanta, meye laifin da Amira tai miki a rayuwa? Ba ita ta tsarawa kanta irin ratuwar da za tai ba, Allah ne ya tsara mata dan me zaki ce se an canza? Ke da Allah dan ƙarshen cutarwa kin mata, tunda kika so haukata ta, kuma ko da Amira ta rasa hankalinta ba zan taɓa yadda in auri jikokokin ki ba, saboda na gane duk abunda kike faɗa akanta sharri ne kawai da makirci Amira ba mutuniyar banza bace, wahala ce ta maida ita haka, kuma insha Allah in har ina numfashi, Amira ba zata tagayyara ba, zan zame mata uwa uba ɗan uwa sannan kuma miji, insha Allah wahalarta ta zo ƙarshe, ba zata sake kukan maraici ba"

Yana gama maganar yasa hannu ya ɗago ta tana ta uban kuka, ya janyo hannunta za su fita daga ɗakin.

Baffa Salahu ya riƙe ƙafar Imran yace "dan girman Allah Imran kuyi haƙuri, kasa baki ta yafewa Yadikko"

Imran yace "wannan ba hurumi na bane, ruwanta ne ta yafe mata, ruwanta ne ta ƙyaleta, amma da kasan iya wahalar da ta sha tsayin watanni uku zuwa huɗu akan larurar da tayi ta isa Allah ya kamata, banda azabtar da ita da ku kai tun ƙuruciyarta banda yarfe da ƙage da kuka dinga mata, dan kawai marainiya ce, mahaifiyar ta ta auri mahaifinku, ni ba zan tulasta mata ba, tana da damar yin abunda ta ga shine dai-dai"

Ya ja hannun Amira suka fito, Sadiya ta taho da sauri gaban su Amira tana kuka tace "Amira dan Allah ki yafemin, kar inje abun da ya samu su Yadikko nima ya sameni, dan Allah ki yafemin Amira"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now