WUTA A MASAƘA 4

706 66 5
                                    


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

SADAUKARWA GA ƘUNGIYAR PERFECT WRITERS ASSOCIATION, DOMIN TAYA MURNAR CIKA SHEKARU BIYU DA KAFUWA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

4

Imran ya miƙe ya koma ɗakinsa yana sake tunanin Amira, duk da anyi shekaru rabon daya ganta, amma yasan ba babba bace ba yarinya ce ƙarama, amma ace wai harta san ta fara yawon banza, ta bar gida taje tayi kwanaki a wani guri, lallai zamanin nan ya zama se Addu'a kawai.

Amira ta na kwance akan doguwar kujera tana game a wayarta, Sultan ya kirata a waya.
Seda ta ɗanyi tsaki sannan ta ɗaga tace "kiran me kake min haka?"

Yace "na turo miki kuɗinki, Amma kinƙi zuwa ki karɓi wayarki, kuma satin nan muna da aiki fa, akwai bukukuwa hadda dinner"

"Tom naji, se kuma me?"

"Ko zaki zo ki bada training ne? Ina son a baje basira sosai, ga wanda ya baki wayar nan yana ta min tuni, yana nanata min zuwa Abujan nan gurin bikinsa fa"

"Kai ka rabu dani da wannan Abujan"

"Amira meyasa?"

"Ina tsoron inje wani abu ya sameni a hanya fa"

"Insha Allah babu abunda ze sameki Amira, dan Allah ki yadda muje, zamu samo kuɗi sosai fa"

"Gaskiya zuwan nan nawa Abuja ƙila wa ƙala ne, babu tabbas sedai insha Allah gobe in Allah ya kaimu zan shigo, zan bada training"

Sultan yace "Dan Allah Amira kiyi tunanin, ina jiranki".

Tace "abunda na yanke zakaji, karka damu"

Sukayi Sallama ta ajiye wayar, Fa'iza ta kalleta tace "Amira, wai har yanzu baki bar maganar zuwa Abujan nan ba? So kike ki ƙarawa kanki abun faɗa ko?"

Amira tace "An daɗe ba'a faɗa ba, ko naje ko banje ba baza'a fasa faɗa ba, dan haka ni be dameni ba"

"Amira ba yanzu nake jiye miki ba, gaba akeji musamman idan Allah ya baki miji, ko bayan kin haihu a dinga faɗin abunda kikayi"

"To waini kinji nace miki zani ne, bafa zuwa zanyi ba"

"Gaskiya ce dai, ko ba kyaso dole in gaya miki ita"

Amira ta miƙe tace "Ni tafiya ma zanyi"

"Allah ya kiyaye hanya" Fa'iza ta bata amsa

Khairat tace "Anty Amira dan Allah ki zauna karki tafi"

Amira tace "Sorry daughter na, ai zan dawo insha Allah, ina son nima naje gidanmu ne, amma ina dawowa"

"To ki dawo da wuri"

"To Shikenan, Insha Allah zan dawo da wuri, ki gaishemin da Abbanku"

Fa'iza bata kulasu ba, Amira ta fice ta kama hanyar gidansu.

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now