45_46

983 59 10
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.







45_46

Amira ta cigaba da cewa "tun daga lokacin da na fara iya hawa kan stage, a gaban dubun dubatar jama'a inyi rawa, kunya ta ƙauracewa idona, mussaman da Ni nake ɗaukar ɗawainiyar kaina, ni nake wa kaina komai, dan haka na dinga ganin nafi ƙarfin kowa, ba wanda ze taka ni in saurara masa.

Sultan ya dinga goyon bayana, yana tafiya dani guraren raye raye, sedai ya kan cemin 'Amira ba'a son raina nake zuwa dake gurin rawa ba, ina fatan Ubangiji Allah ya baki miji me sonki, wanda ze riƙeki da amana"

Ya yadda yaje dani ko ina, in dai fannin rawa ne ba zan ba shi kunya ba, sedai be yadda wani yaci mutuncina ba, Mutane na zaton mutuniyar banza ce ni, sedai duk wanda ya raɓeni da maganar banza, sena masa ƙaramin hauka, dan tabbas har da ƙaramar wuƙa nake yawo saboda tsaro.

Idan aka ɓatamin rai a gidan, gidan Anty Fa'iza nake tafiya, saboda tun tasowa ta ban san wani abu wai shi rarrashi ko ja a jiki ba, amma ba dangin iya ba na Baba, mijinta Bashir yake mutuntani, yake girmamani kamar ƙanwarsa.

Shiyasa nake tafiya gidan inyi kwanaki, tunda aka gane ina zuwa raye raye, Yadikko ta laƙaba min kalmar Karuwanci, ni kuma na karɓa na hau kai na zauna, na nuna mata na amince itan ce, saboda ba abunda zanyi wanda zesa ta janye abunda take faɗa a kaina.

Wannan shine dalilin da yasa nake rashin ji, nima ba son raina bane rashin gata ne, mata da yawa suna lalacewa ne saboda rashin gata, wata da ta rasa breziar da zata saka gara ta bada jikinta ta sam kuɗi, amma ni bana aikata zina ni ba karuwa bace.

Tai maganar tana rushewa da wani irin kula me Ratsa zuciya.

Imran yai ajiyar zuciya, ya rungumeta tana dukan bayanta a hankali da sigar rarrashi yace "Am so sorry Amira, tabbas an miki ba daidai ba, an cutar dake sosai mussaman da munanan kalamai, daga gareni amma dan Allah ina neman afuwarki Amira, dan Allah kiyi haƙuri ki yafemin"

Ba ta iya cewa Komai ba , se cigaba da kukan ta da tayi, ya rungume ta yana shafa bayanta.

Tun daga ranar Imran ya shiga matsananciyar Nadama, yake nan nan da Amira, duk a ƙoƙarin sa na wanke laifinsa, dan tabbas yasan abunda mahaifiyarsa ma tayi ba ta kyauta ba, na nunawa Amira tsana tun tana ƙarama, ba zata taɓa mantawa da abunda tai mata ba, da wanda take mata a yanzu ba.

Amira ta nuna kamar ba abun ɓaci rai da Imran ya taɓa yi mata, hakan ba ƙaramin ƙara mata kima yai a idon sa ba, duk da wasu lokutan idan taso tsiya, rashin mutunci take masa, amma baya duba hakan dan shi be zaci ma za ta iya saurarsa ba haka da wuri, saboda yadda ya dinga mata a baya.

Tana kula dashi sosai, ba ƙorafi da yawan kawo matsala, sedai in kishin ya motsa ko Ihsan ta kira ta yayyaɓa masa Magana son ranta.

Basu ƙara raba gurin kwana ba, daren da yake idan ya fita ya dena, kullum yana manne da Amira (maza manya, ya manta da kashedin Ammi 😂😂😂)

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now