WUTA A MASAƘA 13_14

824 60 8
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

Afuwan banyi Editing ba

KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI

13_14

Abba yai shiru yana nazarin
maganganun Alhaji Hashim sannan yace
"banƙi maganar ka ba Hashim, amma duk da ni na haifi Imran, idan na tursasa masa ya auri Amira, kamar ban masa adalci ba, da ita yarinyar daze aura da fari ba, kuma ina gudun ya wahalar da ita tunda ba sonta yake ba"

"Eh to, da wannan dan wannan, amma ka sani, da kai da kaya mallakar wuyane, zaka iya tursasa shibya kyautata mata, kuma koba komai ka isa dashi, saɓanin ka aurawa bare ita, wanda baka isa dashi ba, ni da ina da ɗa babba wanda ya isa aure, ba abunda ze hana in sa ya auri Amira, hakan Jijadi ne se Allah yai maka Rahama, ya goge maka laifin watsi da zumunci da kayi a sanadin hakan"

Alhaji Ali yace "hakane maganarka, amma yadda zan tunkari Imran da wannan maganar nake tunani, da kuma mahaifiyarsa, kasan Yarinyar daze aura ɗin yarinyar ƙawartace, kar inje shiya amince, su kuma su ɗagamin hankali"

"Da ita da ɗanta a ƙarƙashinka suke, dan haka ka tunkare shi da maganar kaji me zece, nasan baze baka kunya bama"

Alhaji Ali yai ajiyar zuciya yace "shikenan Ubangiji Allah ya wuce mana gaba"

"Ameen"

Ammi na zaune suna hira da Minal, akan yadda Abba ya fita harkarta shima, gashi bata san meyake shiryawa game da Amira ba, tana ta mita tana wassafawa Minal, wayarta ta fara ringing, Minal ta ɗakko wayar ta miƙa mata.

Maman Ilham ce take kiranta, ta karɓi wayar ta ɗaga "Hajiya Jamila, maganar kajin nan nayi magana da me kajin, yace 50 pieces zamu samu kawai a gurinsa"

"Maman Ihsan a sake dubawa, mu samu su cika ɗari mana, bana son muyi bikin da za'a tafi damu a baki, sonake ayi biki na kece raini, naji Babansa ma ze sai mana sa, wanda za'a saka a Abinci, wannan kaji na dinner ne, ina son sake masa magana, amma kwana biyun nan bama jituwa, shiyasa na ƙyaleshi, amma tun yanzu yakamata a sai san a ajiye"

Maman Ihsan tace "Subhanallah, lafiya dai ko?"

"Barni kawai Laɗifa, Magana ce akan wata Yarinya, 'yar ƙanwarsa, ƙanwar fa ta mutu yace ze ɗakkota in riƙe nace bazan iya ba, shine yanzu ta girma yarinyar ta zama fitinanniya shine yaketa take taken, wai ze kawomin ita gida, gani da yarinya mace, salon ta ɓatamin ita, shiyasa na ɗauke masa wuta inga iya gudun ruwansa"

Maman Ihsan tace "gaskiya idan yayi haka be miki adalci ba, ya zaki zauna da ƙatuwar budurwa karuwa a gida, kina mata kallon biri tana miki na Ayaba, gasky idan yai haka be kyauta ba, amma gara ki lallaɓashi ayi auren yaran nan ba Tare da wata matsala ba"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now