WUTA A MASAƘA 23-24

784 58 4
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.





(INA WA INNALILLAHI RAJI'UN, NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE GA YARAN DA AKA SACE AKA MUSU KISAN GILLA A KANO DA KUMA ZARIYA, UBANGIJI ALLAH YAI MUSU RAHAMA YA KAWO MANA TSARO A ƘASAR NAN, ALLAH YA BAWA IYAYENSU HAƘURIN JURE RASHIN SU)

*_Masha Allah, gaskiya ina jin daɗin yadda kuke Comment da nuna soyayyar ku ga littafin WUTA A MASAƘA, nagode sosai Ubangiji Allah ya bar ƙauna, ina jin daɗin sharhin da kuke akan labarin_*

22_23

A fusace Amira ta sake cewa "inji ubanwa? Ke waye ya gaya miki wannan shirmen dan Allah bana son wasan banza, ni mu tafi kawai"

Haɗe rai Fa'iza tayi tace "duk wasan da muke dake na taɓa miki irin wannan ne? Ni karɓi wayoyinki da sauran kayanki, suna waje suna jirana zamu tafi"

"Can ta matse musu su da wanda suka ɗaurawa Auren ba dai Amira b, kuma wallahi bazan kwana a garin nan ba"

Kan Fa'iza tai magana tuni Amira tai waje abunta, Anty dake Falo ta tashi da sauri tace "A'a, Amira ya haka? Ina zakije kuma?"

Amira tace "gida zamu koma, an gama biki ga mota can a waje zamu tafi gida"

Anty tace "wani gida kuma Amira? Ai babu ke ba komawa gida baki san an ɗaura miki Aure bane? Kiyi haƙuri ki koma ki kwanta kin san baki da lafiya"

Aikuwa Amira ta ɗora hannu a ka tace "Na shiga uku ni Amira, wai dama dagaske An ɗauramin Aure da wannan Mugun? Meyasa za'amin haka? Dan anga ni marainiya ce shine za'a Auran wanda ya kusa kasheni? Wato idan ya kasheni ba wanda yake da Asara? Meyasa za'amin Auren dole? Ni wallahi gida zan tafi, gara zaman gidanmu da zama da wannan Mugun mara imani, wallahi ni gida zan koma"

Ta rirriƙe Fa'iza tana rusa kuka, tuni hawaye ya wanke mata fuska, Alhaji Hashim ya sakko daga kan benensa, jin kukan Amira da yayi.

Yana zuwa ya tarar Amira ta riƙe Fa'iza tana kuka, itama Fa'iza seta saka Kuka ta rungume Amira tace "Amira kiyi haƙuri, ki rungumi ƙaddara kinji, dan Allah karki kuma aikata wani abun daze rusa rayuwarki, ina miki fatan Alkhairi da fatan Imran ya zame miki Mijin marainiya"

"Wane mijin marainiya Anty Fa'iza? Kalli jikina fa kalli dukan da yaimin, babu tausayi ba imani, ni wallahi bana sonsa, meyasa za'amin Auren dole dan babana ya mutu, Fa'iza kinfi kowa sanin wahalar dana sha, yanzu na cancanci sake faɗawa wata wahalar? Meyasa kuka bari akamin wannan Auren? Meyasa?"

Kasa magana Anty Fa'iza tayi, ita kanta Anty jikinta sanyi yayi dan Amira ta bata tausayi sosai.

Alhaji Hashim ya ƙarason inda suke, yace "Amira cikata su tafi kar suyi yamma a hanya"

"Dan Allah ku barni in koma gidanmu, wallahi niba matar Aure bace bana son wannan Auren, karku rabani da 'yan uwana alhalin bani da kowa a nan se Allah, wanda kuka saka ya Aureni baya ƙaunar ko ganina, ku dubi maraicina ku rabu dani dan Allah"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now