WUTA A MASAƘA 19_20

785 51 3
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.


19_20

Imran yace "Eh ka harbeta idan tayi maka rashin mutunci ka harbeta a ƙafafumta"

Amira ta tsaya tana kallon Imran, aka buɗe mata ƙofar motar ta shiga, Sojan yaja suka fita, seda Imran yaga fitar motar Sannan ya juya ya nufi gidansu Khalid.

Ƙofar wani katafaren gurin gyaran jiki da kwalliya sojan nan yai parking, ya fito ya buɗewa Amira ƙofa, Amira taƙi fitowa ta kalli gurin sannan ta kalli sojan tace "nan kuma ina ne?"

"Eh nan ne yace a kawoki, bari in mata Magana"

Taɓe baki Amira tayi, ta cigaba da kalle kallenta.

Ya koma gefe yai waya, mimtuna kaɗan sega wata farar mata ta leƙo, tai murmushi tace "tana ina?"

Sojan yace "gata nan a cikin mota, ki fito ki shiga'

Seda Amira taja aji sannan ta fito daga motar ta shiga gurin, matar ta bawa Amira guri ta zauna.

Katafaren gurin gyaran jiki ne da guaran kai na mata, gurin ya haɗu sosai.

Matar ta nunawa Amira wata kujera a gaban mudubi tace "zoki zauna a nan mu fara kar lokaci ya ƙure"

Amira tace "wai me zakiyi min ne?"

"Yi haƙuri, ba wani abu zan miki ba, kwalliya ce akace zan miki"

"Kwalliya kuma, waye yace kiyi min?"

"Kai kekam akwai daru da tambayoyi, daga gidan Alhaji Ali ne"

Taɓe baki Amira tayi tace "ki bari inyi salla tukuna, dan idan akayi lokacin salla yayi wanketa zanyi ba ruwana"

Me kwalliyar tai murmushi tace 'to ta salla"

Haka kuwa akayi seda Amira tayi Salla sannan aka fara kwalliyar, harta samu Guri ta saka cajin wayarta.

Se magariba aka gama kwalliyar, sedai Amira ta haɗu tayi kyau sosai, me kwalliyar taita ɗaukarta hotuna, har sukayi musayar lambar waya.

Sojan nan na waje ba inda yaje yana jiran Amira, dan ba ƙaramin warning Imran yai masa a kanta ba.

Dukda haka seda ta saka ya tsaya, ta cire kuɗi a POS, yana yi yana kaffa kaffa karta tsere.

Ihsan ma tana can kai ya ɗau caji, tana gurin kwalliya, tana son ayi a gama kan Imran yazo ɗaukarta, dan baya son jira.

Amira kuwa tuni ta isa gurin dinner ɗin, seda ta tsaya a bakin ƙofa ta ƙarewa ko ina kallo sannan ta shiga, tana ta waige waige, can ta hango Anty Fa'iza da su Amina, da gudu ta ƙarasa inda suke ta rungume Fa'iza tana 'oyoyo"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now