3

2.5K 164 0
                                    

Babaaa..  Naam fateen baba, kawai sai ta fashe da kuka..  Nasiha baba Abubakar ya mata sosai har saida taji haushin kukan da tayi...

Rana bata qarya, baby taci sunan umma wato Aisha..  Atake idanyi baby su anty aysha da anty fatima suka mata laqanin suna NOOR....

Gida ya rinchabe anata shagalin suna fatima ta shigo da ta zauna a dakin me jego inda su goggo suke, ta dauko jaka ta ciro dan kunne da sarqa na gold me shegen kyau na yara tace to mudai ga gudun mawar mu ta iyaye... Cikin wasa tace Goggo me kika kawo mana ne na jikalle..  Kar kishi ya hanaki fa...  Nasan dai manager da biyayya duk yadda akai ya cika miki jaka danyin gudun maya...

Ba goggo ba hatta hajia zufa take dan basu taba zaton fatima zata ci musu fuska acikin mutane ba haka..  Surayya tai kwafa tace bala'eeee amma fatima baki da mutunci...
Murmushi fatima tayi tace meyai zafi?  Kika san tsakanina da goggo da zaki shiga?  Ita ai tasan wasa nake..  Ko ba haka goggs...

Ran goggo ya gama baci ta rasa yadda zatai tama fara magana bare kare kai don mgnr gsky shine manager ya bata kudi amma atamfa daya riga daya ta siyo....  Chaii takaici tsotsar skirt!

Dadai fatima ta tabbatar ta gasa musu..  Sai ta miqe tace bara na kawo muku alale karta huce, ta fita tana smiling.

***********

Amma Abubakar inaso kasani ko bani na haifeka ba, na haifi goggo kuma ita uwace agunku, duk abinda babba ya hngo yaro bazai hngo ba, ynxu sbd fatima tamu ce qanwar matarka ce shike nan dan tana da lalura kuma ibrahim baxai qara aure ba?  Shekara goma ana neman 11 ko batan wata bata taba yi ba?  Anya munyi wa Ibrahim adalci?  Kasan halinshi bame yawan magana bane bazaka taba fuskantar damuwar da yake ciki ba..  Gadai idris da aysha da suke qannanshi duk sun hayayyafa..  Yau da umma tana da rai aganinka zatai farin ciki da haka?
Abubakar kai nazari akan abin nan...  Cewar hajiya cikin dabara da kissa ta dattijan mata.

Amm hajia bawai naqi taki bane amma Ibrahim bai nuna yana soba mu zamu yi gaban kanmu ne?  Idan ya furta min da bakinshi to ko aranar yace sai a daura auren ai sunna ce me kyau....  Amma bxn iya takura mai akan abinda baya so ba, sbd hka hajiya ki barshi kawai qila kalar tashi qaddarar kenan!

Kai wanna ya fiya tsinannan taurin kai ta fada a ranta..  Amma batai qasa a gwiwa ba tace..
Kasan in zamu zuba wa ibrahim ido bazai taba furtawa ba, me zai hana ka gwada tuntubarshi in ya nuna baya so sai a kyaleshi...

Hajiya kenan, ta fadi hakan ne don tasn Ibrahim vaxai taba musa ma yayanshi ba...

Abubakar yace to naji zan duba na gani...  Kafin ya kufula ya fara rashin m, tuni ta ta miqe tace to Allah yasa mu dace sarki habu...  Sai da safe..  Allah ya kaimu yace...
Da dare yake bawa anty salma labarin yadda sukai da hajia, ya qara da cewa gasky salma ina tausayin fatima, anya kuwa hajia bata da wani plan na kuntatawa fateena?
Anty salma da jikinta duk yai sanyi tace,  a haba ai hajia gsky ta fada da umma tana raye zata so ganin jikanta daga Ibrahim, to miye in anyiwa fatee kishiya ai qadarartace ahaka...  Ka gwada tmbyr Ibrahim din kar a cutar da bawan Allah..
Abubakar kurama salma ido yayi tna da hnkl da kawaici if not fater jininta ce....  She is selfless.

Ya kuduri niyyar yiwa Ibrahim maganar kafin ya koma zaria,  to amma sabgoginshi na kano ya qaranta haduwarshi da Ibrahim har sai ranar dazai tfi..
Goggo kuwa taxo sau ba iyaka amma bata same shi ba, saidai ta hadu da anty salma..

Da hajiya tamai waya byn ya tafi sai ya shaida mata December zai dawo kano domin family meeting anan zaiyi maganar auren Ibrahim din kamar zaifi ayi a idon kowa... 
Wayyo dadi duk da ba hka taso ba amma amsarshi tayi nuni da yayi na'am da batun....
Farin ciki gun surry ba'a magana har ta maida user name dinta MRS. Ibrahim (nace kin zaqe)

****
Tin washe garin suna fatima take fama da zazzabi me naci ga yawan kasala kuma bakinta ya mutu ko dogon hira bata so bare har akiga hayaniya, kamar wasa dai gashi yau sati biyu amma sam babu chanji..  Manager yayi nacin har ya gaji taqi zuwa asibiti, saidai yaje chemist ya danyi bayanin ciwon a hada mata en magungunanta...
Abin mamkin fatima kullum gaba yake yi ta zama wata ruwan sanyi tsakaninta da mutanen nata ma sai dai murmushi..  Ko kuma tace kuyi tayi zaku gaji!

Haka aka lallaba yau lfy gobe babu har takai wata hudu da suna,  noor har tayi wayo..

*********
December

Ana zaune a meeting hall..  Bayan gaishe gaishe, da duk wasu abubuwan daya kamata agudanar,  baba abubakar ya tashi ya fara magana kamar haka

Idan magana zamuyi akan gsky da adalci bama buqatar nuna sanayya...  Ibrahim qanin nane kuma kowa yasan haquri da kawaicin dake gareshi,  fatima yata ce, qanwatace kuma mafi soyuwar suruka a gareni amma Allah ya jarabcesu da rashin haihuwa yau 10yrs kenan...
Idan bazasu damu ba zamuso muji ra'ayinsu akan qarin aure ko za'a dace..  Fatima ta dauka mafarki take a razane tace aure!!!
Kwarai fatee aure!  Qasa tai da kanta bata qara magana ba...  Gggo da hadiza kuwa ba'a maganar farin ciki agunsu..

Ibrahim ne ya dago a hnkl yace yaya ba musu zan muku ba, amma fatima bata da lfy da zarar ta warke sosai zamuyi shawara kuma zamu sanar daku inshaAllah...
Goggo tai charaf tace Ibrahim har ynxu bakasan makircin mata ba da zaka ce saita warke da alama zata shekara bata warke ba kenan...
Ran Abubakar bace yace kamar ya ta shekara da jinya?  Sbd me zatai qaryar jinya?  Goggo me kike nufi..   Shiru tamai gudun kar ta jazawa surayya a soke batun auren baki daya....  Haka aka watse meeting duk zuciyoyin mutane ba ddi sbd in banda su goggo fatima bata da abokin rikici..  Kowa sonta yake, aysha ma duk abin ya dame ta...

Mafarin labari......

Teeluv

Vote nd comment.

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now