29

1.8K 169 7
                                    

*my wattpad followers, voters and commentators, ina godia sosai da irin kwarin gwiwar da nake samu daga gareku.. AND THIS PAGE DIRECTLY GOES TO YOU*

Tee zarewa
Teeluv
Zahra2597

TANA TARE DAKU.... gaisuwa ta musamman ga marubuciyar KOMIN NISAN DARE...  HAUWA HAMISU MUSA (UMMU SULEIM)...

*
Baqar Abaya basma ta dora akan kayanta..

Cikin kayanta na lefe take, abayar ta hadu, red stone ne suka qayata rigar.. Ta dauko flat bakin takalmi na Versace ta saka.. Ba abinda ta shafa amma data fito saida haneef yaga tayi mai wani kyau da yake tantamar fita da ita a hka..

Ido ya zuba mata kawai yana jinjina irin son daya ke mata..  Har ta qaraso..

Cike da gundurar kallon dayake mata tace ya haneef muje mana..

Dawa zaki fita a haka?  Ya fada looking serious

Baki ta saki tana kallon kayanta..  Ta dan sake dubanshi..  Yaqi yadda ya kalleta..

Basma har fuskarshi ta dan leqa tace ya haneef fadi abu daya da rigata tayi..

Bai tnka ba, haka kuma bai miqe ba..

Tace..  Hmmm dan Allah kar mu fara wannan wasan ya haneef..  Bana son haka nan mu fara jayya akan dressing, inada hnkl bxn taba yin abinda yake haram ba...

Haneef kam jiyai baxai iya mata musu ba, yasan bawai ta bayyanar da surarta bane, kawai dai tayi kyau ne da yake jin kishin kar wani ya gane masa ita..

Tashi yayi yace; bana son bata lokaci..  Mu tafi kawai..

Taso ace sbd bayananta ya amincr bawai ya nuna baya son bata lokaci bane..  Amma hkn ma bai baci ba, dan tasan muddin ta biye mishi to gaba kadan niqab zaisa ta fara sawa..

Suna isa mota yace..  Ai kinyi List ba?

Tace eh..

Yace na one week, sunday zamu tafi kaduna..

Cike da zumudi tace tam..

Har mamaki yayi yadda take murnar tfyr..

Ado bayero mall 🏬 suka shiga.. 

Taga ya ja gefe, yana danna waya da hannunshi dayan kuma ya zira a aljihu..

Wani murmushin takaici tayi, aranta tce..  Ya haneef nikam yaushe zai waye ynxu in tsautsayi yasa naga wanda na sani ai sai kunya ta rufeni......

Aje basket din tayi taje inda ya harde ta karbi wayar ta cilla cikin side bag dinta..  Ta sakalo hannunta cikin nashi ta gefe..

Binta kawai yake da ido ya kasa fahimtar ma me takeyi..

Kamr soko haka yake binta,  gurin basket din ta nufa, ta janyo daya ta mai alamar ya tura su tafi..

Babu musu yayi hakan..

Sai wani fake smile take saki, ita adole irin lovely couple dinnan..

Yadda basma take dramanta saida yasa haneef murmushi da har both sided dimples dinshi suka lotsa..

Yasan basma fitinanniya ce, amma yadda take abubuwanta, wani zubin kamar yarinya, wata ran manyance wata ran tsiwa da taurin kai to yau kam ya qara guda daya harda BASAJA..  Duk suna birgeshi.. Though smartness dinta yayi yawa..

Kamar daga sama taji ance Basma. I haris..

Da sauri ta juya..

Kuwa dai muryar dataji ita ta kirata..

Da iyayi fauza ta qaraso da wani farin slim handsome guy..  Ana tafe ana show casing iphone x..

Basma meet my fiance, abdurra'uf..  Speak english to him pls, he is a half cast..

Tana wani iyayi ita a dole wadda tai excelling

Basma tai murmushi tayi tace ohh da alama qasar yunwa..  Naga kamar zai fadi..

Dakyar haneef ya. Maqale dariyarshi

Fauza tace mene?

Ba komai fa qawalli, abdul hi..  Shima hi yace..

Basma tace ki gaida mijina..

Ta fada tana dan kwantawa a kafadar haneef

Haneef kuwa yana maqale da basma amma gaba daya ta cikashi da dariya..  Sai fara'a yake.. 

Sama sama ya kula fauza dan yaga tana da rawar kai..

Basma ta ciro wayar haneef iphone x max daga side bag dinta tacewa fauza ur digit..

A take yanayinta ya chanza ita adole kar basma ta mallaki wayar data fi tata..

Shiko haneef mamakin basma yake yadda tai fuska ta dauko wayarsa..

Kawo na sa miki..  Nan Gaban basma ya fadi..  Tadan saci kallon haneef wanda guntse dariya kawai yakeyi,  don dik tunaninta da password akai..

Cikin dari dari ta miqa mata, tana bude wayar ta danyi yaqe tace nice couple..

Hotonsu na ranar kamu ne akan wayar ita kanta basman bata sani ba..

Ta saka digit din Tace ki kirani..

Basma tace karki damu..

Sukai sallama..  Fauza najin kishin basma!

Tin ba yau ba ta tsani yarinyar..  Tin suna sch take shigar mata hanci da qudundune...  Gashi yau saukarta daga Abj sukai aran gama..

Sun gama siyayya suka nufi mota..

Kamewa yayi kamar bashi ne yaketa murmushi ba...

Har suka isa gida babu wanda yace qala.. 

Basma kuwa wani sanyin dadi takeji dan ta yadda komai zai mata in sun koma gida ya mata duk masifa dai baxai yanka ta ba..  As far as bazai kunyatata ba cikin mutane to wlh gaba ta kaita..

Dan ita kanta tasan haneef miji ne na nunawa ko cikin duk duniya..

Bayan yayi parking, bai kashe motar ba yasa lock..

Waigowa tayi tana mai kallon ya haka?

Murmushi yayi aranshi yace basma er rainin hnkl ce..

Ita dinma abinda take ayya nawa kenan..

Yace ina wayata, dariya tayi tace..  Ohh ya haneef yau ai ka birgeni gaban wannan fauzan..  Er adawata ce, tin muna sch.  Ta liqewa suhail time din saurayi nane.. Har fda muka tabayi..

Hade rai yayi kmr bai taba dry ba..  Yace akan namiji kikai fada tin kina qarama?

Sai sannan tasan wautar da tayi, dagowa tayi tace mene?

Shi yasa kikai qaryar waya? 

No bakaga sai wani bragging take da wayarta ba, niko gwara in nuna mata babu tsiya a tare dani..

Hmm

To ai qarya ba kyau basma..

Ya haneef hassada ma ba kyau..

Na sani, amma karki qara, in baki da abu don't pretend u have it..

And that freaking boy!  Ki manta shi daga yanxu...

Tace wlh wlh banma san inda yake ba, itama fauzan tazo da rainin hnkl ne..

Mamaki kawai basma take bashi sam hade ranshi baisa bakinta ya mutu ba..

Horn sukaji..

A tare suka daga kai motar..  Alamin ce..

Ai da sauri basma ta waigo ta marairaice fuska akan ya bude kofar plz..

Ba musu ya bude, aguje ta fita ta rungume noor..  Suka shige suka bar mazajen da kallonsu..

Al-amin yadan yi gunguni ynxu inda er ajiya ma sai wannan basman ta ma mutum sila..

Haneef yace kaba basma ajiya?

Da sauri ya dago a dan tsorace yace mefa?

Haneef yace Mu shiga ciki

Ba musu suka shiga, basma sai santin yadda noor tayi kyau take yi..  Suna ta murnar ganin juna..


Teeluv loves u

Vote nd comment

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now