36

1.9K 142 0
                                    

Sweet sojana..  Kanaji ba..

Sai kuma tai shiru..

Kallonta yayi bai mgn ba yana so ta fadi abinda takeson fada..

Kallonshi ta danyi ta marairaice fuska kamar zatai kuka tace..

Sojana banason kishiya..

Zan iya mutuwa innaga wata dakai..

Aranshi yai hamdala, lallai ya yadda basma ta fara sonshi amma yayi imani bata ko kama kafar yadda yake jinta ba...

Murmushi yayi ya janyota jikinshi... Yace anya idan na qara aure zan Iya adalci?  Hmm babyna Ban  iyawa..

amma fa in kina dadewa bakizo min weekend ba qila na qara ya fada with a wink 😉 ... Har ranshi zaulayanta yake..

Jikinta ne yayi sanyi tace ko dai zan hakura to da krtun ne?

Dariya yayi sosai har tana mamaki, yace ashe dai basman nada tsoro...  Wasa nake miki baby, in har naga kin dade bakizo ba sai dai ki ganni a ABU nazo daukar amaryata...

Yaqe tayi amma har ranta tana tsoron kar fa dadi krtu yasa amata kishiya...

***

An shirya taron suna.. Na musamman, a cikin gida zasuyi taronsu su gama..  Mijin hadizan ma ya bada hadin kai, duk da en uwanshi sunso su kawo tangarda amma kuma dole suka hkr sbd gidanta baida girman da kowa zai sake..

An rada suna aka sanyawa jaririya aysha..

Tin asubahi da akai radin suna goggo ke surfa zagi.. 

Hadiza amma baki da zuciya!  Har ki rasa wa zakiyawa takwara sai uwar wasu ba taki ba!  In banda kare ya lashe zuciyarki me aysha da ahalinta sukai miki?  Me suka tsinana miki?

Nidai wlh baki gado halina ba, nida a asubiti na haifeki zance tabbas musanya ya akaimin, da fari kin taso yadda nake so..  Sai kuma ki rikide kamar wadda akaiwa asiri?

Anty sury da khaltum ne suke ta dannarta gudun kar zancen ya karade gidan dan ynzu kam isu isu suke hayaniyarsu..

Banda kuka babu abinda hadiza takeyi..  Sun ma kasa bata lokaci tai mgn..

Sai da sury tace ke munafuka miye hadinki da sunan ummah da aka sanya miki?

Saida ta share hawayenta tace goggo aysha sunan mariqiyar sani ce, wlh baida alaqa da ummah, amma kun rufe ido kunata surfa min bala'i..

Kunya ce ta rufe goggon..  Tace yo kunyi abu a dukunkune wazai gane?

Aslm..

Anty autah jego da kumburin ido?

Ba sury ba hatta goggo jitai gaban ta ya fadi..

Me idonsu yake gani?

Basma ce tai kyau haka?  Haneef tare da ita?  Idan ba gizau idon sury yayi ba, gani tayi kamar ma riqe da hannunta yake!

Hadiza ce ta qaqalo murmushi tace woo amaryar soja, bame kirana da wannan sunan saike, saukar yaushe?

Yanzun nan, kinga yaya ko daki baije ba na dage sai munzo munga me sunan kaka, ta fada tana qarasawa da dariya..

Haneef ne yai hnklin gaishe da goggo da sury da sukai mutuwar zaune...

Suka amsa tare da hadiye wani mugun yawu..

Basma tace nayi missing naki kakus, ni wlh nayi zaton ke za'aiwa takwara, ashe kaka babba aka farayiwa..

Goggo dai tsabar takaici bata tanka ba...

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now