6

2.1K 152 0
                                    

Am very sorry sir, we couldn't save her.. We lost her.... She was profusely bleeding which result to hypovolamic shock, we set I.V line... Bhu it keeps blocking instantly....
We couldn't help it! We lost her!!

Baba Abubakar yaji likitan ne bawai yana gane me yace ba.... Innalillahi kawai yake maimaitawa

**********
Ka sani Ibrahim yadda fatima ta tafi kaima zaka tafi, kuma ba shawara nake baka akan kayi hkr ba, dolene kayi! Baba ya tafi, umma ta tafi meya same mu?

Yaya duba kaga yadda BASMA ke neman abinci.. Ynwa take ji, kaga fa ita fa bata taba ganin mamanta ba, yaya irin kukan da BASMA keyi yafi komai daga min hnkl...

Basma bata da uwa ne bayan fatima? Ina salma, amina da aysha? Idan duk basa nan sai kace min Basma zatai kukan maraici!
Kayi hkr Ibrahim kayiwa fatee addua....

####
Fadar irin halin da familyn baba suka shiga bazai misaltu ba... Sun shiga rudani da fargaba ga tsananin tsoro... Kuka aysha takeyi ta kasa sabawa dacewa wai fatee ta rasu..

To ya zasuyi qaddara ta riga fata, gadai buri ya cika ta haihu amma ta bar musu duniyar!

Goggo dai jiki yai sanyi amma tana taya surayya murnar samun miji.. Ko ba komai gani suke an bar musu fili su wala

Gashi an gama gyaran gidan tass wai za'ai suna, toh qila gyran zaman surayya ne... Rabo kenan cewar hajia...

Hmmmm!

***********
Anyi suna ansawa yarinya BASMA, aka dora da zaman makoki.. Yayinda anty salma ke bata madara, yarinya kyakkyawa kamar yar larabawa...

Kwana a tashi asarar mai rai, yau akai arbain din fatee, Alhmdlh yanayin Ibrahim yayi sauki.. Toya zaiyi? Dole ne sai radadin rabuwa ya ragu.. Allah ya riga ya halicci mantuwa a kwalwar dan adam duk radadin abu yanayin sauqi kwana 21 ya isa ya samai nutsuwa a ruhi....

*********
Ibrahim an doshi shekara kenan da rasuwar matarka ya kamata ka nutsu ka fidda mata kai aure, zamanka haka bxai yiwu ba, da na zuba maka ido naga baka da niyya to ka sani dole ne kayi aure.. Dududu nawa kake? Don't tell me you gave up for love nd marriage! Baba Abubakar ne yake mgn in a serious tune!

Yaya.. InshaAllah zan duba..

Wane dubawa Ibrahim ga er uwarka surayya.. Ai sai gd ya qoshi ake kaiwa dawa.. Nidai dazaka dauke ni kmar umma zan baka shawara ka auri er gd wadda aka san halinta..

Mamakine yasashi yai shiru, kenan mutanen nan bazasu kyaleshi da zancen surayyan nan ba?

Shirunka ya nuna ka aminta ne ko kuwa kana da option? Yaya ya katse mai nazari..

Maganarce tamai nauyi ko qala baice ba..

Murmushi goggo tayi tace Allah aarki Ibrahim sarkin kunya...

Baba abubakar ne yace shikenan Allab ya sa mu dace tinda abu yazo da sauqi basai an bata lokaci ba!.......

Murna dai gurin surayya aranar ba'a mgn kmr ance mata an daura,
shiko manager baida lokacin soyayya sbd yasn wahala zai sha kmin ya samu kamar fatee.. Koma dawaye su daura auren chan ta gane amaryar!

******""""*******

Kaiii anty diba kiga yadda ya haneef yake hararar basma kamar tasan me yakeyi... Ni wlh kome tayi birgeni take, er kubula sai shegen kwadayi..

Ai kai baka da hnkl yarinya tana barna kana mata dariya duba kaga duk ta dame jikinta da nutella, ace qaramar yarinya tasan kwadayi kamr yr mayu! Cewar haneef

Mune mayun ai, mara mutunci, wlh wlh kabi duniya a sannu marainiya ma sai tasan kai mugu ne? ..
Fahad dauke ta plz, bara nazo na mata wanka....

Tinda suka dawo cikin gd gaba dayansu fahad yai sallama da part dinsu kullum yana gun anty salma yana wasa da basma.. School ke rabashi da ita, abinda yake bashi dariya shine yadda noor ke tsoron basma sbd yakushi, daga zaune in bakai mata daidai ba zata sa qara ta kai yakushi kamar wata zakanya!

Shiko haneef dama can bame wasa bane, ko safna bai fiye kulawa ba, har gara noor sbd bata da hayaniya.. Amma basma kallon me tsiwa da fitina yake mata.. Sam baya daukanta!

**********
An daura auren Ibrahim haris da Surayya ilyas akan sadaki dubu hamsin... Abinda ya doki kunnenta kenan saida gabanta ya fadi, ta rasa dalili gashi ai an daura auren amma wani iri takeji, gashi ta gama zuzutawa frnds dinta biki... Tunowa tayi da saqon manager...

_Don't try to involve me in ur mess... Da sunan biki, ni na gama biki!_

Jikinta ne duk yai sanyi gadai aure an daura.. Zuwan frnds dinta yfi komai sata frnciki kowa so yake yaga Ibrahim amma ta fake da baya son hyniya ne gashi yana fama da headache.. Zainab tace niko baban amra ranar bikin mu bakiga murna ba harda rawa duk da shima miskili ne...

Ran sury ya dan baci dan tasan zee da biyu tayi mgnr, dama tin tali tali haka suke ba sa wani jituwa!

Haka suka sha sha'aninsu ko keyar abokan ango ba wanda aka gani bare ango....

Yo rabin shagulgulan ma ba'a gida aka yisu ba, suko su aysha, anty salma, amina da sauran en uwa sunce bazasu iya yawo ba.. Sbd hk cikin gd sukai nasu budurin...

Haneef barin gidan yayi dan ya tsani hayaniya da hrgowa... Shiko en uwa ma ba'a abin arziki dashi bare taron dangi.. Fahad ko ina zashi Basma ina ya dawo basma, ko abinci in za'a bata saidai a nemi fahad, gaba daya she is excited taga gida fal, sai harba hannaye takeyi kamar er dambe... Noor kuwa tana maqale da ummanta sbd taga an cika gd.......

Anyi an qare ankai sury dakinta adar irin kyau da gidan yayi bata lokaci ne, to kayan daki ne amfi 5yrs ana tarasu har saida sukai yawa... Komai na sury designer ne...
****
Wannan wace irin mata ce? Wai auren ma acuci take masa? Aranshi yai murmushi yace i missed foreva! Kallonta kawai yake tana yauqi ita babu ya ita, irin her first night was perfect dinnan..

Waih first ko me? Hmm lallai kam first qila dai first a gidan aure amma ba a zahiri ba!

*******
Mama maaaama da gudu ta shigo gun anty amina, mama aiina ya faaaad???
Ohhh Basma ya fahad yana makaranta.. Zo ki karbi chocolates din daya bar miki.. Memakon tai murna kuka ta saka ita dai sai ya dawo...

Teeluv

Vote and comment

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now