24

1.8K 139 11
                                    

Safna ce zaune cikin er runfar gidan inda fahad ya nemi ganinta..  Tayi nisa cikin tunani, zuwa ynxu kam ta qarbi qaddararta sbd ita bada maqiyinta aka hada ta ba, bata taba qin ya fahad ba kamar yadda bata taba sonshi ba..

Ya fahad tin bayan meeting  wata hira mai tsayi bata taba shiga tsakaninsu ba, iyakaci nasiha da ban baki akan yarda da qaddara, yau kuma ko kiran me ya mata?  Ita dai tayi jimm tana jiranshi..

Saida ya dan kalleta, yaga sam hnklnta baya jikinta..  Yace hmm

Sallama ya sake maimaita mata, a hnkl ta dago ta kalleshi kadan, ta amsa ta kauda kai..

Kujera ya samu ya zauna, yana fskantar ta.. Yayi kyau abinshi, shadda ce getzner milk sae sheqi take ksncewar ranar juma'ane yana dawowa daga sallah ya kirata akan su hadu anan...

Sunkuyar da kanta tayi, zuciyarta blank, empty feelings..  Ta amsa sallamar..

Atamfa ce a jikinta riga da zani ta jar Hollan,  a kai ta yafo gyalenta yadda ya rufe kusan rabin fuskarta ta gefe...

Fahad ne yace amarya bako gaisuwa ne, ki dago ki dubi kwalliyar angonki mana ki bashi marks..  Ke kam yau na vaki 80% sae kin zama matar zaki sami 100%... 

Dagowa tai da mamaki tana dubanshi..  Yau kuma?  Namiji!  Hmm a take zuciyarta ta raya mata qarya yake mata so yake ya ladabtar da zuciyarta da kalaman bakinshi....

Har anyi nisan da zae manta da basma ya fara mata kalamai haka...

Yadda ta tsura mai ido ysn ba kallonshi take ba, kamar ya laqanci me take nazari yace

Safna ba duk so bane samu...  Zuwa yaushe kike tunanin zamuyi facing reality?  Zuwa yaushe zamu zubda maka man yaqin mu?  Ki fahimci wani abu safna, qaddara ta riga fata, ana mutuwa, ana jinya, ana haukacewa, ana faduwa jarabawa, ana bata, kiga bat mutum an nemeshi an rasa, ana nakashewa, kiga mutum ya kurumce ko ya makance ko kuma ya rasa kafafu ko kuma wani sashi na jikinshi.. Ana mutuwar aure da mutuwar yara!
  Kenan in haka ta faru baza'a sake dariya ba?  Baza'a ci gaba da farin ciki ba ko kuma baza'a karbi qaddara va? 

Kai safna ta girgiza a hnkl, kalamshi suna ratsa ta..

Sbd hk ki cire komai aranki, mu karbi qaddarar mu kinji uwar gidan fahad?

Dagowa tai vata ce komai ba

Yayi dry yace wannan harara?  Tuba nake, uwargida kuma amarya a gdn fahad.. 

Murmushi safna tai, tana jinjinawa barkwancin fahad..

Hira suka danyi, harta saki jiki sunata dry..  Hira tai hira harda su selfie...

~nace gsky ne fahad~

****

Ya saleem ina yinunku..  Basma ta gaishe da haneef da saleem..

Haneef ne ya kalli saleem, irin frnd can u see it..

Saleem ne yamai alama akan he shld be patient...

Guri ta samu ta zauna, gaba daya vata jin dadin zamanta a gun, da qarfi zuciyarta take bugawa, dan ma saleem yana gun..

Malama basma, ya hutu? 

A hnkl ta furta lfy yasu anty asiya da baby..

Lfy kalau ya amsa..

Tun dama can sun dan saba sbd dadewar amincinsu da haneef ya zama kamar dan gida...

Basma nsn dai zuwa ynxu yaci ace kin rungumi qaddararki kin bada kai bori ya hau, gani mukai ga biki ya matso amma vabu wani yunkuri dakike yi, kuma sanin kanki ne, bikin er gata irinki ya buqatar shagulgula..

Murmushi tayi ta dago, saleem ta kalla tace, ya saleem auren soyayya akewa wannan hidimar..  Ko zan tara mutane ne aga ango da amarya babu me fara'a?

Ka gaishe da anty asiya, zan shiga ciki.. 

Kafin ya bude tabar dakin..

Haneef ne yai kasa da kanshi cike da disappointment!

Saleem kuwa murmushi yayi, dan yadda basma tae magna tana dan haki ya nuna a tsorace take..  To tsoro kuma?

Ta gwammaci kar ta hada shagali sbd kr agansu suna fushi!  Hmm

Kenan da zasuyi annuri zata amince?...

Hmmm

Haneef kaine kake wasa da damar ka..

Saleem ne yaja haneef zuwa part dinshi yace ya zauna mgn zasuyi..

Haneef kamar soko haka ya zauna yana sauraron saleem..

Major ina jarumtarka?  Ina dakiya da kawaicinka?  Ina hakuri da juriyarka?  Ina kakaisu?  Nan ne inda zasuyi aiki!

Nan ne inda zasu tallafa maka!
Allah ya baka basma cikin sauqi da taimakon addua, ynxu kaine zaka dage ka janyo ra'ayinta...  Dole ka aje girmanka agefe, kaima ka zama dan kwalisa!

Dole ka zama me wasa da sakin fuska a gareta.. Ni banga qiyayyarka a idon basma ba, she is soft hearted zakai saurin shawo kanta inka dage..

Dagiya kuwa na nufin, nuna mata tsantsar soyayya da kulawa tare da shanye duk wani abu da zatai muddin bai tsaurara ba...  Ka yawaita uziri a gareta tare da nuna mata qauna da tausayi..   Don't  be too judgemental, sbd naga baka fuskantar ta ma kake judging duk abinda yazo ranka,  So nake ka zamo very soft nd kind to her...  Shawara ce ko ba ynzu ba zatai maka amfani!

haneef ya dago yace..  Wo angon asiya malamin soyayya, ai baka sani ba, duk wata jarumtaka da juriya qarewa suke inna ganni gaban basma, daurewa kawai nake ina yin ta maza amma in dai muna tare pulse rate dina mugun raising yake, har wata er zufa zufa nake fa, shiyasa bana sakewa..  Amma inshaAllah zan jajirce in tunkareta..

Saleem ne ya zubawa haneef ido ganin yadda yake zuba sbd an tabo ruhinshi, mutumin da ba'a wata doguwar hira dashi amma yau so ya maidashi wani soko soko!

Kallonfa mallam?  Haneef ya fada cike da tsarguwa..

Dariya saleem ya saka yace yo ai naji major ne zuba kawai yake an tabo mai inda yake mai kaikayi..

Ohh hakane?  Tanan zaka bullo dan kaji cikina...  To anyi an gama..  Baka san ma haushinka nakeji ba, dazu memakon kana wa basma mgn ka kalli qasa har wani kalle min fuskar mata kake..

Baki salim ya toshe yana dariya yace bala'i!  Major anya basma bada niqab zata fara yawo ba nan gaba, ni ynxu yaushe na wani kalleta dahar ake qoqarin jefani a black list..

Bata rai haneef ya kumayi yace, dan iska ai ka gama zuwa wlh..

Saleem dai dry harda hawaye ganin yadda haneef yai kicin kicin wai kishi!

Cikin dariya yace aiko nima baka qara zuwar min gida sai dai mu hadu a kofar gida...

A ran haneef yace ai asiya bata kai basmata ba, a fili kuwa yace..  Ka hana mana, dadin abin nima by nxt month na zama angon sai dai wani zancen!

Saleem yace dakyau man, ai na maka yaqin neman zabe, kayi ydda kake so..

Dariya suka danyi a tare..

*masoyana, masoyan basma, me kuke gani?  Yanxu labarin ya fara!  Basma da haneef zasu shiga cikin wata rayuwa, saga?  Puzzle? Simple?  Hard?  Romantic? Ku biyoni sannu a hnkl kuji me zai faru*

Taku har kullum

Teeluv

Vote nd comment!

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now