28

1.8K 152 12
                                    

Bayan sati daya Mamie tai wa duka en matan biyu waya akan su fara girki ta gama nata, su noor kuwa da ma tfy zasuyi...  Su haneef kuwa hutu harda wuce iyaka, shidin ma ranar sunday yake sa ran tfy....

..

Da safe da mazajen suka shigo gaidasu Mamie, tace Lallai suje suyi shopping din kayan girki da matansu dan ita kam ta gama nata,

mama tace ai ba laifi anty salma kin shagwaba amare da angwayen nan..

Fahad ne yai dariya yace haba mama, muna tunanin kuyi swapping, kema ki mana na sati shine zaki ce haka..

Dariya alamin yayi yace amma baka da mutunci..

Murmushi kadai haneef yayi...

Mamie kuwa so take su kebe taji yaya diyarta?  Duk da tasan ba lalai ya fada mata yadda takeson ji ba, ita kuma basman mamie tasan halinta na boye damuwa shiyasa taqi yarda da yanayinta...

anan su haneef sukejin gobe al-amin zai wuce gun aiki,

fahad yace aiko sai kazo har gida kai mana sallama, al-amin yai dariya yace ba dole ba....

haneef ne ya miqe kamar zai fita sai kuma ya nufi dakin mamie,

mamie taji ddin yadda ya gane tana son mai mgn, ta danyi excusing kanta...

alamin ne yasa dariya yace, babban yaya shifa munyi kadan muji matsalarsa saidai mamie...

fahad ne yasa dariya yace ai haneef kam gwra daya shiga aikin soja, dama can dasu yai kama

mama tace duk ku qare mai gulma, yana fitowa zan fada masa..

Dariya sukai a tare suka ce to mukam sai anjima, dan da haneef ya harari mutum gwara baba ya kamashi da laifi...

Mama dariya sosai tayi tana jin dadin yadda matasan suka qara kyau da hnkl,

alamim dake da jikin qiba har yaso yafi fahad kumari..

Noor kam tin bayan da aka kaita, part dinsu sau biyu ta taba leqo cikin gida sbd kunya, gashi qawayen nata basa nan...

°°°
Ina basma fa?  Hope dai tana lfy, ka fadamin inda matsala..

Murmushi haneef yayi..  Yace ma mie ita kam basma baiwar me gareta haka?  Ita kam bata da maqiyi ne?  Kowa sonta yake da yawa..

Hmm ba tmbyrka azncin magana nayi ba haneef, so nake naji yaya autata take?  Kafi kowa sanin basma er amana ce, ko ba aure qanwarka ce sannan ko babu alaqa marainiya ce, kuma kasan hukuncin quntatawa maraya, kuma kasan ladan qautata musu..

Ta qare mgnr kamar zatai hawaye, duk sai jikin haneef yai sanyi..

Hannunshi ya sanya ya riqe hannun mamminshi, yace mamie kece abinda na fara so a matan dunia, kuma basma ita na fara so a en matan dunia..

Daga haka bai sake magana ba, ya miqe ya tafi...

Da sauri mamie ta dago tana kallon bayanshi harya fita, a hnkl ta shafa fiskarta, taji hawaye, tace lallai wannan hawayen farin ciki ne...  Nima ina qaunarka dana..

Yana fita yaiwa mama sallama, ya fada mata akwai kaya mal. Yahya zai shigo dasu ynzu..  Tace to Allah yayi albarka soja..

Kayane niqi niqi haneef ya kawo ko wane part saida aka kai, har goggo, hatta gidan hadiza da mama aysha saida aka aika,  ko wace leda, turmin zani ne super, da getzner ta iyaye maza, sai turaruka, anty sury, hadiza da mama aysha sukam har da packet din swt na yara a nasu..  Wai duk kayan ban gajiya ne..  Hatta basma bata san sanda yai wannan bajintar ba...

Mamie taji dadin abinda haneef yayi yau kam fes ya wanke mata zuciya...

Su goggo kuwa duk an rude,  tace ke surayya duba min yaron nan rabon super yai mana?

Sury tace bar tsofin munafukai, bayan an tura mana aniyarmu agun biki sai an biyo mu da super dan a nuna bamu da sutura kome?

Goggo tace hmm nidai koma miye dai na gode, tinda ku da kuke nawan kun kasa tara min su..

Sury ce ta kalli goggo galala..  Lallai goggo in dage in miki leshin shiga taro, amma yau akan atamfa zaki juyan baya?  Gsky ne ba laifin ki bane tsufa ne..

Takaici ne ya tirniqe goggo taita mita, sury kuwa ta barta anan ta koma part dinta..

***

Sallama haneef yayi..  Shiru babu kowa a parlon

Kai tsaye ya nufi dakinta,

Shigarshi yayi dai dai da fitowarta daga wanka daga ita sai towel half way..

A tare zuciyarsu ta buga... Ta qame a bakin kofar kamar soja, ita bata koma ba ita bata fito ba..

Murya tana rawa yace ki shirya ina parlor..

Yana fita tai ajiyar zuciya..

Shikuwa yanayin daya riske ta dakewa kawai yakeyi, ya fiso saita fara sonshi wani abu zai faru tsakaninsu, to amma zuwa ynxu ya fara tantamar haka..

Pencil jeans baqi ta saka da light brown top me kyau..  Tayi kyau sosai, ita ta gaji da sanya native wears ne yasa kawai ta sanya wannan kayan badan wani abu ba..

Fitowa tayi hnklinta kwance tace. Ya haneef gani..

Kura mata ido yayi yaga ita fa ko ajikinta.. Kayan sun mata kyau sosai.. 

Yace autar mamie waya sai miki kayan nan..

Kallon kayan tayi ta kalleshi..., sai kuma tadanji kunya yadda ainihin shape dinta ya bayyana,

Fuska tayi tace, mammie ce..

Zamuje shopping, mamie ta gama aiko da abinci, kin iya girki ba?
Mamaki ma ya bata, a yaran gidan nan babu wanda bai iya girki ba, sai dai koshi amma hatta siyama in tazo gida mamie ko mama na shiga kitchen da ita..

Duk irin snacks da girke girken da sukeyi agidan nan wai ya haneef dan wulaqanci tmbyrt yake ta iya ko bata iya ba..

Yitai kmr bata jishi ba....

Sarai yasan taji, yau tsiwan ne ya motsa..

Tasowa yai, bata ankara ba ta ganshi a gabanta..

Da karfi kirjinta ya buga, gashi ya mata kwarjini ya cike ko ina..  Babu abinda takeji sai kamshin turarenshi daya dabaibaye ko Ina, kallonta yake dab da tab..

Ido kawai basma take rabawa tayi tsilli tsilli..  Lips dinta sai motsi suke tana so tace mai ta iya girkin amman yadda yai mata ta kasa nutsuwa..

Runtse ido tayi ta gama tsorata jira kawai take ya dau matakin dayake ganin ya mishi daidai..

A hnkl yakai saitin kunnenta, yace tsiwa ko?  Rufe idon kuma me kike jira?..

Har kwakwalta saida taji wani yarrr..

A hnkl ta bude idon taga ya miqe tsaye yana kallon wayarshi kamar bai yi komai ba..,

A hnkl tace ya hneef na fa iya, taya zaka  tmbyeni na iya girki bayan kaima ksn duk mun iya..

Yace ohh da gske nasn kun iya?  Ai ban taba cin abincin autar mamie ba..

Takaici yasa ta turo baki ta miqe a fusace zatai daki ya riqo hannunta, ya dan janyota jikinshi

yace,  kinaji ba? I will tke care of this lips ok?  Ki sauya kaya kizo mu fita..


Teeluv

Love u all❤

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now