38

1.9K 156 4
                                    

Washe gari major bai yiwa basama bayanin komai ba, illah iyaka yace zaije zaria, akwai abinda zaiyi.. Itama bata tsananta ba, ya shirya shida yaranshi uku suka nufi inda akai masa kwatance...

*
Sir, a irin rayuwar da muke ciki, ba kowane dan boko bane ke zama ma'aikacin gomnati amma duk wani ma'aikacin gomnati dan boko ne!

Munada ilimin da qasar mu ke buqata, na kware ne a software programming, abokin aikina emeka kwararre ne a fannin video clipping, Photoshop etc. ..

Mun buga har mun gaji amma aiki ya gagara.. 

Na nemi aiki a wani company, chairman din ya yaba da kwarewata, amma duk sanda nazo secretary nashi ne kemin manaqisa..

A qarshe dai ban samu aikin nan ba!

Mahaifiyata tana kwance a asibiti ko kudin magani bamu dashi bare na aikin da za'ai mata...

Auren qanwata an dagashi yafi sau ba iyaka..  Har mijin na barazanar janyewa..

Ko sisi babu ajikina, ga ilimin fal kaina!

Kwatsam sai wani abokina a lagos yake min bayani game da wannan harkar.. 

Shiya min komai, shiya sai min computer da komai...  Har shagon da nake aiki aciki shiya kama min... Da sharadin rage bashin daya bani duk wata!

Da farko kamar bazan iya ba, amma dana fara sai da na zama kwararre a harkar!

Ynxu haka da nake bayanin nan, wlh nafi qarfin duk wata matsala, har kanwata dake gidan miji tana samun na kashewa bare mahaifiyata..

Takai ta kawo ba da kowa nake business dina ba sai da manyan en siyasa da masu fada aji..

Duk wani qaramin aiki emeka nake barwa, ni wlh bansan ya sukai da matar ba, illah iyaka na hadasu suyi ciniki tinda naji tana ambaton dubu hamsin nace kuyi magana da yarona..

Iyakar gskyta kenan yallabai..  Nazifi ya fada tare da hade hannayensa biyu yana sharar kwallah...

Tamau haneef ya kuma hade rai yace qila in munje barrack za kufi bayani..

Emeka da tuni ya ski fitsari a wando yace, yallabai, wlh zan fada maka komai..

Tazo ne 3days kafin na turo maka wannan saqon..

Ta bani dubu hamsin akan daga baya zata qaro min inna saki video din..  Ta bani hotunan madam har guda bakwai da video selfie guda biyu tace na zabi wanda zaifi hawa yadda babu wanda zai gane..

Ta tabbatar min zata fiso ace ka saki madam ne bawai yaduwar video din kadai ba...

Sannan koda ka saketa din to fa zata qramin kudi sosai na saki video a vidmate, YouTube, Facebook, Instagram, da dai sauran kafafen yada labarai akan matar major H. A. Haris fasiqa ce!

Wani zaranannen qara haneef yayi ya naushi emeka a fuska a take haqorinshi daya ya fado..

Ya dunkule hannun zai kai masa wani naushin, sai kuma ya fasa..

Fuskarshi taji jaa, tsabar bacin rai da kunar zuciya ke damunshi..

Wata zazzafar iska ya furzar!

Emeka kuwa tuni ya baje agun yana kuka...

A razane haneef yace..

Miye sunanta nace maka!!!!

Emeka jiki na rawa yace

*KHALTHUM*

KHALTHUM?  haneef ya maimaita...

Who is this bunch of shit!

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now