Mallam harisu mijin aishatu, malamim makaranta ne, yayi ilimi daidai gwargwdo yana koyarwa..
Matarshi aysha mace ce mai hakuri da kawaici, sam bata son magana bata da rikici ko hayaniya inda halinsu ya banbanta kenan, shi mutum ne mai tsauri da fada...
Yaranta hudu Abubakar babba sai da tai shekara 12 cip sannan ta sake haihuwa ta samu ibrahim sai idris da auta aysha...
Bayan ta yaye aysha ne diabetes ya sata agaba har yai silar ajalinta...Rasuwarta ta girgiza illahirin family, sbd kirkinta da kawaicinta.....
bayan rasuwarta da shekara biyu hajia wato Abokiyar aikin mallam harisu ta nace mai akan ya auri diyarta sbd zaman haka babu ddi.. Da farko yaqi daga baya kuma ya amince inda ya auri harira goggo kenan...
Baba yana matuqar son yaranshi kuma baya daukan hauka, hakan yasa goggo bata samu nasarar cutar dasu ba... Ga shi abubakar ma baya daga mata qafa, baya bari a taba masa qannai wannan qauna aysha ce ta gina ta da hannunta, ta nuna musu muhinmancin junansu tun suna qanana....
******
Bayan shkera da auren baba shima abubakar ya kammala HND Dinshi a fannin electrical engineering a kano poly.....
Ya sami aikiki da wuri a wani company., ba laifi yana samun kudi, nan fa ya fara ragewa baba dawainiya... Ya dau nauyin mkrntar aysha idris da Ibrahim kuma yabasu 10k each su kama karamin kswanci yadda zasu rufawa kansu asiri su kammala krtunsu, sbd baba ya yi retire ba abinda yake buqata kamar hutu.. Gashi har tsufa ya fara mai wasan da ba'a dariya...Bayan shekara daya Abubakar yayi aure anan cikin gdnsu yai part dinshi, dan gidan babba ne sosai.... Baifi wata da yin aure ba goggo ta haifi haris, me sunan baba kuma fir baba yaqi yadda a sauya mai suna.
Bayan wata biyara da aure, anty salma matar Abubakar laulayi ya sata a gaba, gashi baya zama sosai a gida sbd ga aiki kuma ya koma mkrnta... Nan fa abu ya dameta, ga goggo bata taimaka mata sai baqi sunzo ko kuma in taga abubakar tai ta mata sannun munafurci.....
Abu ya taru yaima salma yawa... Gashi aisha daga yaye inna lami qanwar umma taqi dawo da ita.
Ba shiri ta nemi a bata qanwarta fatima, babansu dakyar ya yadda danshi baya ra'ayin kwashe kwasge sbd shi mutum ne mai gudun magana...
Zuwan fatima saida ya zama babban sauqi ga salma, komai na gidan ita takeyi, gashi tana debe mata kewa, and bata yin shiru akan duk wanda ya kawo wa yayarta hauka...
Goggo kuwa da ta riga ta maida salma kishiyarta, zuwan fatima ya daga mata hnkl, lta kafa qahon zuga tana ta bijiro da fitina iri iri amma bata samu shiga ba.. Shine ba shiri itama ta dauko qannenta surayya dake shekara 9- 10 da kalthum da bata wuce biyar 7,da sunan wai hajia ta tsufa kula da yaraa zai bata wahala... (Kuma ta haifesu)
Wannan lokacin baba shima yana fama da girma, kota kanta baibi ba.. Yace indai abinci ne suzo sui taci...
Tin zuwansu surayya gdn ta tsani fatima.. Itama ko ba kyaleta tai ba dan haka basa zama inuwa daya...
*******
Kukan baby kawai kakeji ba sassauci.. A firgice fatima ta miqe daga baccin da take.... Me zata gani anty salma ta haihu... Duka su biyun babu wanda ya iya gyara baby, andaiyi sa'a anty tayi qoqarin raba cibi da mabiyya...
Da gudu fatee tai ban garen su goggo... Tana kwalla musu Kira iya qarfinta babu wanda ya amsa kuma sarai tasan sunji.. Sai baba ne ua fito daga nashi dakin duk da ba lfy gareshi ba yace mamana meya faru ne... Sai taji nauyin sanar mishi.. Da kyar yace anty salma ce kuma bamu san ya zamuyi da baby ba....
Murmushi yayi yace alhmdlh.. Kije kiyi kaza kiyi kaza.. Haka yai mata bayani dalla dallah.. Aiko da gudu ta antaya dakin ta fra kamr yadda ya sanar mata...
Ita dai salma ido ta zuba mata, byn ta gyara ko ina ta hada ruwan zafi tasa anty taje tai wanka, sannan taiwa babyn ta samai kaya ta kunna turare... Tana kwantar dashi ya fara kuka yn neman nono... Byn anty tai wanka tae feeding baby, tuni bacci yai gaba dasu....
Sai da gari ya waye tas saega goggo sum sum wae tazo su gaisa fatima tai wuf tace, ai da kin bari munxo da knmu yadda muka saba...
Haka dai rayuwa ta ci gaba da wakana, baby yaci sunan baba ake ce mishi haneef..
****
Daga ibrahim har idris ba zaman gida suke ba sbd tare suka samu admission a ilorin kuma basa waiwayan gida sai shekra ta zagayo, can suke neman kudinsu suke kuma krtu...*******
Akwana a tashi baba jiki yaqi dadi haka ya kwanta dama, ba tare da yayi shawara ba... Haka Allah yake lmrinshi..Kowa na gdn ya shiga matsananciyar damuwa... To amma ya zasuyi. haka Abubakr yana gani girma ya kamashi.... Shi yake kula da komai na gdn...
Idris da Ibrahim ma sun girgiza da rasuwar baba, bama kamr Ibrahim daba mgn yake ba sosai duk yafi lalacewa...
Bayan wata biyu da rasuwa ba goggo ta haifi auta hadiza
******* agurguje***"***
Ba'a dau lokaci ba Ibrahim da fatima suka sasnta kansu, idris ya nemo aminarshi, aysha ma ta fidda suleiman.. Aka sha biki..
Fadar kalar baqin cikin da surayya ta shiga bata lokaci ne dan ita tin zuwanshi hutun farko ya kwanta mata arai, amma ya rasa wazai so sai wannan bnxar... (Er 17yrs ke zancen nan hmm)
Shekara goma kenan;
Abubakar yana da yara 4, haneef, Alamin, safna da muhd.
Idris nada biyu fahad da noor.
Aisha nada biyu da cikin na uku, amir da minalAllah ya kawo wa Ibrahim.
****************
Back to storyAnya ba ciki gareta ba, duba kiga yadda tai wani fari, ga uban gashi kmr wata baturiya... Wlh nima bn sani ba hajiya kawai dai ta zama wata iri, amma gsky bana tunanin ciki ne sbd d ta jima tana jinya kuma bnga wani alamu na ciki ba.....
Haka sukai ta gulmarsu... Daya wannan sai wancan!
**"""""**
Fatima wen last kiga period dinki.. Saida gbnta ya fadi sbd tmbyr da anty salma tai mata...
Naam? Tace..
Maimata tmbyr anty tayi
Tace anty tin kafin nai aure kin mnta my period is not stable.....Shit! This ia true.. Ina dai zargin ko ciki gareki, tashi ki shirya muje asibiti...
Anty dan Allah ki bar.. Bata qarasa ba anty tace
Ke, bana son sokonci tashi muje!...
Jiki a snyaye ta dau abaya, ta zura flat takalmi ta bita...
