150

284 20 8
                                    

     Cikin sanyin jiki lady saudat ta kalli zahra sannan ta kalli su grans da suma alamar damuwa ya nuna a fuskarsu , ganin yanda gaba dayansu suka yi sanyi ya sanya lady saudat basarwa da fadin
   "Hush! Thats satan har yanzu bai saduda bane huh!?"
Ta karasa maganar a wata irin fusace da karaji kamar irin zata tashi taje ta nemo duk inda boss din yake tayi ta dukansa har saita ga bai motsi

   "Ki bari pah doctor!, that man he sure issa satan"
#maryam alamar she's more than dumbfound now duk wata basirarta koma ta kare tana mai kara gyara zaman hadin gyaran jiki na amare dake jikin ta

  Da sauri lady saudat ta amsa mata da
"Absolutely "
Sannan ta saki wata irin zazzafar ajiyar zuciyar tana mai dauke cucumber dake saman idonta ta sanya a baki
  "Hush! Ya Allah...Ni yanzu ya daina turo min about a week kenan"
Tana mai kara daukar wata cucumber dake manne a fuskarta ta lankwama a baki cikin yanayi na karshen takaici something like "i can't kill myself"

Bakin ciki kamar zainab zata rufeta da duka ganin yanda take tauna cucumber kanta kasan don ta basu haushi ne, koma tabbas sunji haushi din
  "What a dirty girl!,
Daman ance babu wanda yakai doctors kazanta...mtsew! So disgust"
Ta karasa maganar da dauketa kallonta akan lady saudat da yanzu ne ma ta sauya taunar cucumber na asalin shakiyanci da tsokana

 
  Cikin rashin damuwa da abinda lady saudat tayi hacker ta sake gyara zaman rounded slide cucumber dake manne a fatar saman idonta cos tasan abinda lady saudat sarai! Tsokana da son tada zaune tsaye
"Nima haka bai turo ba ai"

  Murza yatsun hannunta maryam tayi cike da tabbatarwa irin na"yeah you are right nama tuna nima"
"Exactly Nima babyn sultana, then mai yasa koma yake turowa zahra?"
    Ta karasa da kallon zahra wacca ke zaune tsumu! Kamar an cilla tsumma a randa damuwa fal! Fuskarta, yayinda grans suke take mata baya cos suma sun bada wata irin emotional faces kamar masu xaman makoki har abun dariya ma abun ,
Sannan ta maida kallonta kan lady saudat wacca ta sake daukar wata cucumber dake fuskarta tasa a baki , ta kalli zainab ta dire kallonta kan hacker da alamar amsar tambayar nata a wajen hacker take nema

   Yar mika hacker tayi tana fadin
"Goodness grecious!,
Come to see of it ina ganin zahra is they target"
  Sannan ta daidaita kanta tana mai kallon zahra wacca ta koma abun tausayi abun dariya "but amma zahra about last week shima ya turo miki messages din?"

   Kamar zahra zata fashe da kuka ta amsa mata da fadin
"Tunda ya faRa turowa bai taba daina turowa ba"

    Dan siririn tsaki zainab taja ciki_ciki tana fadin
   "What a shit!,
That bitch har yanzu bai saduda ba kenan?"

    "Yaushe zai saduda tunda ba'a kamashi ba an yanke masa hukunci, it seems like har yanzu that lunatic jerk yana da sauran hope na sake jefa mu cikin wani mummunan hali kamar yanda yayi 20, & 30 years back, har yanzu yana da sauran hope na zai sake kubcewa hukuma da hukunci"

   "Imagine!"

    Kukan da zahra  take rikewa ne ya kubce mata tana mai kwanciya jikin Dr.aisha hannunta na rike dana dr.sa'adatu
  "No please,
Ni bana son a sake samun wata matsala , grans!"

  A hankali dr.aisha take dan bubbuga bayanta alamar rarrashi tana fadin
  "Kada kiyi kuka kyakkyawa kedai kiyi ta addu'a Allah ya rabamu dasu lafiya ,
Amma Tunda kika ga boss yayi haka lalle wani mugun tugu yake kullawa cos mun san sharrin sa kamar yanda muka san layin tafin hannun mu"

  Ajiyar zuciya deeja (maman tanim) ta saki cikin sanyin jiki tana fadin
  "Haka ne Aisha abinda nayi hasashe a dan karamin tunani akan wannan sabon salo na boss ina ganin kamar so yake idan wani a cikin wanda yake turowa message yayi respond musamman ita zahran daya ke yawan turowa  yayi amfani da ita wajen wanke kansa kamar yanda ya saba a kodayaushe!,
In some cases rishe zai iya juyewa da mujiya kamar yanda yayi a baya laifin ya dawo kanmu

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now