The unassailable 153

375 18 5
                                    

Har jiri_jiri gadanga yake gani ganin zahra a tsakiyar wayannan kartin mazan numfashinsa sai sama da kasa ke yi , he can't believed it that zahran sa ce wannan , wani kato rike da hannunta ita koma tana kokarin kwacewa saman kanta kowa bindiga ce wanda har baya yayi sakamakon jirin dake dibansa idress yayi saurin tare shi ,

kafin su ankare mutanen boss suyi musu kawanya da bindiga sama_da_kasa kusan kowanne sashi na jikin gadanga da aka san makasa ce mutanan boss sun auna bindiga a wajen, idress daman already an janye shi daga kusa da gadanga da alamar daman target dinsu shine

Wani dan tattaki boss yayi da dingisassiyar kafarsa hade da nakashshen idonsa yana mai kallon gadanga kallo na musamman tare da fadin
"Here come the haidar or gadanga bansan wayye a ciki ba"
Yana mai karasa maganarsa da sakin wata irin mahaukaciyar dariya ta farin ciki mai hade da takaici tashi daya , yayinda mukarrabansa suka take masa baya da
"HaHaHaHa!"

"Finally gadanga mun san ba alien bane nor ghost talkless of holy spirit!,
Hahahaha!"
#mr.lee ya fada wata irin dariya keta da mugunta wanda yasan dole ran gadangan zai baci musamman duba da shine wanda ke rike da wrist din zahra

Aikowa ran nasa yayi mugun baci babu abinda yake ji da gani sai ganin da yake yiwa zahra wacca wani kato ke rike da hannunta bai tunanin wannan hoton abun zai fita daga zuciyarsa

Yayinda su kowa boss da mukarrabansa Sosai suka tsaya suka dinga shakiyancin su , son rai tamkar basu daina ba sai chan suka turbune fuska suna masu tsuke baki kai baka ce sune ke dariya dake barazanar dolewa mutum kunne ba , dai_dai da kwakkwaran motsi babu wanda yake a cikin su grans, appa, harun, lady saudat, hacker talkless of detective adam da mukarabbansa wanda suka gama tsorata saboda sun san tabbas! Boss shida mutanen sa suka yi wani single crazy move saidai uwarsu ta haifi wani ba su ba wannan ba wani abu bane

Bayan boss, mr.lee, cheif judge , barrister zubair da sauran manyan masu fada a ji a cikin kungiyar sun gama maganganunsu na tsantsar bacin rai hade da nuna lalle sai bacin ransu ya tabbata a kanshi(gadanga) , , ,
Wannan karon mr.jack (hacker) ne yayi magana yayinda yake yin dan tattaki daga inda yake zuwa wajen gadangan
"Lalle ka cika night courier tunda har ka iya gano location din mu cikin abinda bai wuce 30 minutes ba Whoa!"
Ya karasa maganar da fadin "whoa!" Na tsabar bacin rai da takaici

Sannan ya sake matsuwa wajen gadanga wanda in bacin numfashinsa da idonsa babu inda ke motsi a jikinsa tsabar yanda aka tsare shi da bindiga
"Finally yau gani ga ka face to face without any mask, , , the invisible night courier, , , the unbelievable hacker..."

Cike da shakiyanci mai hade da tantiranci mr.lee ya katse mr.jack da fadin
"Oops! Ka manta mr.jack ba shi kadai yake aiki ba!, , ,"
Kamar an basu umarni gaba dayansu suka saki dariya "Hahahaha!"

Cikin nasa salon shakiyanci shima mr.lee bayan ya gama dariyarsa yace
"Oh wow!,
you are right mr.lee!,
Ina hacker din tasa take?"
Wasu Yan kalle_kallen shakiyanci mr.jack yayi kamar irin yana neman wani abu sannan ya maida kallonsa kan hacker yana mai dan yin tattaki daga gaban gadanga zuwa wajen hacker
"Aigoo! Here is she!,
What a cyberpunk,
Whoa!"
Da alamar shi nasa salon shakiyancin ne cewa "Whoa!" Koma daman yasan wacce hacker din already

"Wannan itace hacker data gagareni over 20 years, mace !, , , mace ce!...oh wow what a shame"
Tashi daya koma ya saki Wani tafi da baifi a kirga ba yana fadin
"Oh wow!, splendid"
Ya karasa maganar da komawa matsayarsa da alamar ya gama nashi shakiyancin ne

Kamar masu rawar nanaye boss ya sake fitowa tsakiyar wajen yana wani rangaji da shakiyanci da dingisassiyar kafarsa
"A karo na ba adadi daka samu nasara a kaina , kada kayi alfahari da yawa akasi ne na sa'a dake juyawa a kodayaushe kamar yanda ka gani a yau ta juyo kaina"

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now