ZAHRA TAWA CE 30

489 36 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖




💞💞💞
*ZAHRA TAWA CE*
💞💞💞





*FATIMA ZOIS*




Dedicated to *BABBAR YAYAH*
(ramby *011*)




Page3⃣0⃣




"Wannan shine kadai abinda kake bukata yallabai boss?." @journalist ldress cikin wata sabuwar rudewar irinta yaga abun duniya

Wata irin dariya boss ya saki wacca babu abinda zai hana kace tsawa ake,daga jin wannan dariyar irinta mashahuran azzalumai ce da suka Dade suna zalunci, sannan ya cigaba da fadar abinda ke ransa cike da fal! Da tsanannacin farin ciki samun nasara farat! Daya haka _shegiya naira!_

"HHHHH! Wannan shine kadai abinda nake bukata a tare da kai ya kai wannan babban bakon namu,
sannan koma idan da dama kungiya tana bukatar kwararran dan jarida da aka yarda dashi irinka,da fatan zaka karbi wannan tayin namu da hannu bibbiyu."

Saurin sake tarar numfashinsa journalist idress yayi cike da kwadayi irin na masu son abun duniya koda zasu saida ransu ne"Haba dai yallabai! inga wannan uwar dukiya haka har kake tambayata idan da dama in shigo ina ga nine ai ya kamata na roki wannan damar."

"Kamar hadin bakin, Ko ince kamar daman abinda suke jira kenan,gaba daya wajen suka hautsine! Da wannan mahaukaciyar dariyar idan ka dauke alhaji harun da sai faman cika yake yana batsewa ga tsananin tashin hankali nan kwance a fuskarsa."

Cikin dariyar isgixi da farin cikin samun nasara boss yace"maraba da kai wannan babban bakon cikin *aljannar. Duniya* wacca baa fita har abada saidai ko idan mutuwa kayi!."


Numfasawa journalist idress yayi sannan ya fara maganah cike da tararradi!"To amma boss kasan ni mutum ne na mutane!,sannan al'umma sun gama saka rai da taimakona akan wannan shari'ar da ake shirin gabatarwa, ya kake ganin abun zai kasance idan har aka San da sa hannuna a cikin wannan bakin aikin!?."

"HHHHH! Journalist Kar kasa wannan kwata_kwata a ranka bare har ya da me ka,ba komai bane wannan idan kayi laakari da manyan mutanan da alu'ummar suka yarda dasu a cikinmu,"

"Wanda komah al'umma suka yarda dasu a kodayaushe a koma kowanne hali na dadi da akasin haka fiye da kai dinnan!."

"Ina mai kara tabbatar maka da cewar yanda wasu mutanan suka yarda dani basu yarda mah da Kansu ba,Wanda da yanxu xaka cewa wasu da suka sanni ina wannan harkar ina ga wanin sai inda karfinsa ya kare wajen musanta wannan zargin mai kama da almara a wajensu ba abun mamaki bane ba idan wani a cikinsu ya kaika kotu domin a wanke ni daga wannan bakin zargin,Wanda har kai ina tsammanin zaka iy yin haka."

"Bayan ni dinma journalist idress idonka ya gane maka many a_manyan kasar nan da al'umma suka yarda dasu ciki kowa harda kai,"

"Eesh! Ina ganin wannan ba wani sabon Abu bane da zaka tashi hankalinka a kai ba, abinda muke bukata dakai shine kawai ka bada hadin kai akan komai aka baka umarni HHHHH!."ya karasa da wannan dariyar tasa ta boss din asali Wanda journalist yaga alama kamar abun ya zame mishi jiki

"Amma boss kana nufin wannan zargin da ake muku na safarar mata ta hanyoyi daban_daban da gaske ne hakan?." @journalist ya tambaya cike da son karin bayani

"HHHHH! Lalle na yarda dan jarida ya shigo cikinmu,journalist idress kana mamaki akan wannan dan karamin al'amari ne? Toh wannan kar ya zamto wani Abu da har xaka dinga mamaki akai,da sannu daxaka San fiye da haka mah idan har xaka bada hadin kai HHHHH!." @boss ya karasa wannan muguwar dariyar da gaba daya ta gama Isar journalist

Rausayar da kai journalist yayi cike da gamsuwar abinda boss yace wannan shima ya daura da tasa tambayar"Yallabai ko xan iya ganinka in person?."

"Kambo! Ai gaba daya mutanan wajen a millions suka yi wata irin muguwar juyuwa zuwa kallon journalist idress kamar sunga wani abun tsoro ko journalist idress ya juye musu xuwa wata sabuwar halittar,"

"A millions suka sake maida wannan faka_faka kunnuwansu mai yanayi da funkason la'asar daya kara budewa domin suji abinda boss zaice."😆

"HHHHH! Lalle ka cika dan jarida journalist idress abubakar haruna, Indai har ganina ne ba wani Abu bane da zaka damu kanka akai,da sannu idan harka ta cigava zaka ganni duk da cewar nidin sananne a gareka da kowa mah daka sani."@boss ya bata journalist amsa Wanda basu yi tsammanin haka daga gareshi ba

Rausayar da kai journalist idress ya sake yi na alamar gamsuwa Sannan ya sake antayo masa wata tambayar


"Yallabai baka ganin wannan zuwan nawa mah da nayi nan da koma tarowar wayannan many a_manyan bakin hadari ne duba da irin yanxu yanda hackers suka yi yawa hade da koma dagewa da wasu mutanan suka yi wajen bincikowah gaskiar wannan al'amari?."


"Wannan ba wani Abu bane a garemu gaba daya cos da da akwai matsala babu abinda zai Sanya muyi wannan haduwar kamar yanda kowanne shashi ya cigaba muma haka muka cigaba."@boss

"Amma boss akwai wani tantirin mutum Wanda naji ance ya gagari kowah wato *gadanga* har kudin mah naji ance ya gagareku, kana ganin baxai iya kawo mana farmaki ba tunda ance a halin yanxu babu Wanda ya kaishi hacking skills ciki da wajen kasar nan!?."@journalist idress


Saida boss yayi shiru nadan lokaci tukunna ya magantu,maganar tasa mah ba kamar da ba,ko wannan yar munafukar dariyar da yake yi ya daina🤣

"Mu kanmu mun rasa yanda zamuyi da wannan tantirin yaron wallahi journalist,kana kallo daya bayan daya yake bin mutane na yana yi musu duka da rashin mutunci na wuce tsammani gashi har yanxu banxanyen nan sun kasa ganin koda fuskarsa ce;"

"Wallahi boss gadanga ya wuce yanda kake jinsa a baki." @mazah da najib kamar Wanda aka fusge maganar daga bakinsu

"Dallas! Kuyi min shiru banzaye daku kawai! Ku yanxu idan ana maganar kirki mah a saka daku ne!?,kaf! Cikin Ku babu Wanda gadanga yayiwa duka biyu gaba dayanku Hugo dai_dai ya biko dashi amma kallin yanda kuka koma."@boss a fusace

"Boss wancan karon mah don bamu shirya bane shiyasa."@mazah kamar da gaske😅

Banxa boss yyi mishi sannan ya cigaba da kora wannan bakin bayanin
"Nasha gayyatar dan iskan yaron nan zuwa wajena ta E_mail address nashi amma har yau ko replying bai taba maido min ba,"


"Ni koda baxai dinga aiki a karkashina ba,mu sasanta ya daina bincike a cikin al'amurana da koma shisshigi akan abinda nike aikatawa."


Wata zazzafar iska ta fusata boss ya fitar Sannan ya Dora akan inda ya tsaya

"Na alamar dole saina shiga cikin wannan al'amari dake kawo mana rudu a cikin harkokinmu sannan komai zai daidaita;"

"Amma journalist idress naji ance *gadanga* yana bayyana a duk sanda wani Abu ya same reporter ZAHRA abubakar sadeeq miye gaskiyar maganar tunda ance yanxu Kuna aiki a waje daya." @boss


"Don Allah pah yallabai kaga koni da nike wajen ban taba jin wannan maganar ba." @journalist idress cike da son Karin bayani

"HHHHH! Ai sau biyu yaron nan yana bayyana koma duk akan wannan yarinyar ne,aiki ya same ka tun daga yau journalist idress ina son ka bugi cikin reporter ZAHRA din kaji mi zata ce akan ,gadanga din!?." @boss cike da farin cikin samun mafita

"An gama ranka ya Dade..............."journalist idress ya kasa karasa maganarsa sakamakon jin maganah amma basu San ko daga ina bane


"Mu fice!, Mu fice!!, Mu fice!!!, Bil'lahil azeem na rantse da Allah *gadanga ne*" @mazah daya Riga kowa ficewar kamar ya manta aikinsa na tsoron lapiyar mutanan wajen idan hakan ta faru😂😅🤣

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now