ZAHRA TAWA CE 49

488 35 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖



💞💞💞
*ZAHRA TAWA CE*
💞💞💞



Wattpad@
*Fatima zois*


Dedicated to *BABBAR YAYAH*
(ramby *011*)


Page4⃣9⃣

"Zaune yake gadanga akan hadaddiyar kujerar boss wacca suke ji da ita kamar kwai!,
Ya Dora kafarsa daya akan daya cikin tsantsar mulki da izza irin tasa tamkar ba gidan boss ya xo ba,
Yanayinsa gaba daya ya nuna yau ba mutunci musamman duba da yanda yake karkada kafarsa."

Cikin tsananin Bacin rai irinna mashahuran azzalumai mai hade da karfin hali boss ke maganah cos a ganinsa tunda har yau gadanga ya shigo muhallinsa  babu abinda xai hanashi cimma kudurinsa a kansa

"Kai yaroh! Mi ya kawo ka!?." @boss ya karasa cikin karashi da kururuwa irinta baraxanar hukuncin da xai Yanke mah gadangan idan bai saduda ba

Banza gadanga yayi dashi tamkar mah bai San da wanxuwar hallitar boss a wajen ba,
saima su alhaji bala da barrister zubair ne ke wani ladavi kamar su ake wa tambayar

"Lalle azabar hukuncina ya tabbata akanka ya akai wannan karamin shu'umin!." @boss tare da komawa dabas! Ya zauna akan kujerar  dake facing wajen

Wata mahaukaciyar dariya boss ya saki ta yau pah gadanga ya kawo kansa ga halaka tare da Murxa yatsunsa ji kake sautin "Das!" Ya tashi tare da cika wajen gaba daya kai baka ce yatsa ya fitar da sautin ba,

"Wannan ita ce Alamar yana kiran bodyguards dinsa  cos yau tunda gadanga ya har ya kawo nan boss a ganinsa babu Wanda ya isah ya fiddashi
Ai yau kawai saidai wani amma ba shi ba."

"Shiru babu koda alamar tahowar bodyguards bare har ya gansu har xuwa wasu lokuta."

A hankali dariyar da yake yi ta fara raguwa kamar saukar farashi
Cikin sauri ya Danna security bell dinsa dake jikin kujerar saboda a kawo babban dauki nan mah dai shiru

Cikin rashin damuwa kamar gadanga baisan abinda ake ba yace
"Uhm! Malam musa ba saika wahalar da kanka wajen an yin amfani da bell din ba ko kiran mutananka!."

Dagowah boss yayi da kansa daga Barin kallon wajen security bell din NASA,
Yasha mamakin ganin irin yanda aka ci mutuncinta kamar ba dukiya ya zare ya siya ba

Wani irin faduwar gaba  da kirjin boss ya bayar shi yake sanya mutum ya hadiyar xuciya ba tare daya shirya ba,

"Tunda yake harkokinsa da mutane bai taba ganin Wanda ya gane shi ba bayan ga yan kungiyarsu sai gadanga,
Lalle da matsala dole ya nemo mafita duk inda take kowah."

"Cikin tashin hankali ya sake maida hankalinsa kan security bell din,
Babban abinda yafy  daure masa kai shine
yaushe gadanga yayi wannan aikin alhalin shi kansa mah yana falon kiransa ne kawai da akai a waya ya shigar dashi cikin daki,
Sannan koda mah bai falo alhaji bala da barrister xubair duk suna ciki banda dumbin bodyguards din dake waje..."

"Ah! ya yarda da maganar najib da mazah yanxu
Lalle babu ko shakka gadanga ba mutum bane!."

Wani irin ido da fuskar boss ta bayar shi zai baka mamaki tamkar bashi ya gama cika baki ba,ga wani hadiyar yawu da yake yi mokwallatonsa sai sama_sama da kasa yake ta kasa daidaituwa

Ai tuni boss ya zube a kasa kamar mai Neman gafara cikin alamar tashin hankali da saduda
"gadanga mi kake bukata a gareni,idan kudi kake so gadanga ga dakin na nan kaje ka dibi komi kake so!
Idan daukaka hade da shahara kake so ka fadi kowanne irin matsayi ne  a duniyar insha Allah zaka samu?..."

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now