Nuhahu 6 reporters 60

551 32 2
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*ZAHRA TAWA CE*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIMA ZOIS*
Wattpad @
*Fatima Zois*

Dedicated to *BABBAR YAYAH*
( _Maman Yasna & Yameen_)

*Masu tayani jajjabi akan babban rashi na mutuwar aliyu haidar da umar faruk ina kara yi muku godiya,*
_Nima fans ina tayaku jajjabi akan wannan babban rashi da aka yi!_😭🤧

Page6⃣0⃣

Wani irin wawan birki harun yaja jin da yayi umar faruk da aliyu haidar sun karasa maganarsu da Kalmar shahada yana mai fitowa daga sit dinsa na driver xuwa baya inda abokan nasa suke kwance cikin jini

A hanzarce cike da koma tashin hankali na karshe yayi saurin daga Hannayensu tare da kara kunnensa akan kirjin kowannensu xuwa kan zuciyoyinsu

Cak! Yaji bugun zuciyarsu ya tsaya
Hannunsu daya daga sun koma,
Cikin sauri ya sake kara hannunsa akan hancinsu ko zaiji iska na fita,
Cos shikam bai yarda da abinda zuciyarshi take sanar masa ba akan lalle_lalle sun rigamu gidan gaskia

D same! Babu alamar numfashi a tattare dasu ga jikinsu daya saki,

Kallon fuskarsu yayi ganin yanda murmushi ke kwance akan fuskokinsu kamar ka kirasu su amsa yayin da hannayensu ke rike Dana juna

Up to now shifa harun bai yarda umar faruk da aliyu haidar sun mutu ba,
Sam! Mah kansa yaki daukar abun bare yanda yaga fuskokinsu cike da annuri fiye da kullum,
Du_du yaushe suka gama magana da har za'a ce sun mutu

A hankali tunanin ya fara dawowa game da abokan nasa
Babu abinda ya fara fado masa a rai irin idan fa da gaske umar faruk da aliyu haidar suka mutu shikenan har abada bazai sake ganinsu ba,
Har abada ba zasu sake yin aikin tare ba,
Har abada ba xasu sake zamtowa abokai da zasu zauna suyi farin ciki tare suyi bakin ciki tare suyi wasa, suyi dariya suyi kuka,
suyi fada su shirya,
Su kwana su tashi tare suci abinci tare...Komai ma tare
Har abada kenan wannan abun da yake tunani da Wanda ba zai iya tunawa yanxu ba da gaske ba zai sake yinsu tare da abokansa ba idan kenan mutuwar ta tabbata akansu kamar yanda yanxu yake ganin alama!!!???

Cikin sauri kamar yana magana da wani muryarsa na wani irin rawa yace
"Aaaaaaah!!! Umari,gadanga kada Ku tafi Ku barmu..."
Yana mai fada kan gawar tasu tare da rungumesu hade da sakin wani irin kuka mai masifar cin rai yana mai girgiza su kamar wani tababbe

"Umari gadanga kada Ku manta alkawarin da muka yiwa juna akan duk rintsi duk wuya muna tare..."

Chan koma kamar wani mahaukaci ya tashi daga kansu tare da share hawayen dake shimfide a fuskarsa
Sannan ya saki dariya yana mai rike dayan hannun umar
"Oh yeah master
nasanka da irin wannan pretending din please ban so irin wannan wasan abeg!
ka tashi bai kyauto kayi irin Wannan wasan ba a irin halin da muke ciki....Nasan kudan granny,aleefriend da koma Ni'ima zaka rayu koh abokina!?..."
Ya karasa maganar yana kallon umar faruk,
In ba don mutuwa mutuwa bace da babu abinda xaisa ace umar faruk yaki amsawa a irin wannan kyakkywar fuskar tasa da kullum ke kunshe da fara'a harma za'a cewa fara'ar fuskarsa ta yau tafi ta koyaushe

Kallonsa ne ya sake kaiwa kan aliyu haidar,
Rungume aliyu haidar din yayi a jikinsa tare da cewa
"Oh yeah abokina kasan dai irin wannan wasan baya pitting dinka Huh!,
So u should better stop it...Nasan abun zaiyi mugun rashin kyau idan na sanar da hafsat tare da bintuka irin abinda kaima kayi...Ash! Alin hafsat ba kace zaku rayu da hafsat a kowanne irin hali kuke ciki"
Ya karasa yana kallon fuskarsa shima dake dauke da murmushi kamar Zai amsawa harun abinda yake fada

A hankali murmushi da annurin dake fuskarsa ya dauke ganin duk irin maganar da yake musu tun dazo amma har yanxu basu amsa ba,
Kenan mutuwar tasu ta tabbata!!!???

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now