plan B,lady saudat the heroine 121

615 47 4
                                    

  

💖💖💖💖💖💖💖💖
*ZAHRA TAWA CE*
💖💖💖💖💖💖💖💖



*FATIMA ZOIS*
Wattpad#fatima ZOIS



Dedicated to *BABBAR YAYAH*
( _MAMAN YASNA & YAMEEN_)



'''madalla da Yan  uwa irin Ku masu kamshin apple #WATTPAD FANS😍🥰😚 lalle Ku gane zahran gadanga naji daku,Wannan page kyauta ne dungurungum gare Ku sai yanda kukai dashi'''😇
_Am so sorry once again my dearest fan!...Don allah Ku kara hakuri dani okay!_
*Uh_oh!😣 Abun babu dadi baba YAMEEN da Babbar Yaya sunyi birthday ba'ayi celebrating dani ba Eesh! So sad...I just wanna wish you blessing,success,Allah's protection, prosperity in your life till the end* Ameen summa ameen 👏🏻🤲🏻
_Anty wasi'a da daughter nafeesat na group TOP 10 HAUSA NOVELS ina taya Ku murnar samun karuwa da kuka yi Allah ya raya mana wayannan saurayi da budurwa ya sanya albarka a rayuwar su yasa masu taimakon mu ne___Ameen summa ameen_🤲🏻🤝🏻

*wannan page din naki ne anty Amina ladan bunza😃,lalle ke Abun girmamawa CE daga cikin Wanda zan girmama na gode da wannan kauna taki*💕💖💗

Page1⃣2⃣1⃣

         Cikin abinda baifi kiftawar ido ba gadanga yayi wata irin tashin bazata daga inda wannan chinese yayi wurgi dashi!,
yana mai shiga tsakanin lady saudat da Wannan Chinese tare da rike hannun sa daya kawowa lady saudat mummunar cafka hade da watsa masa wasu irin munanan kallon tho ba ganinsa Yake ba Kai DAGA gani babu damar canja masa kamanni ne if not da ba Wannan zancen ake ba

    A tsorace lady saudat data yi saurin antayawa gefe ta kalli gadanga da Chinese eyes dinta a wajen kamar zasu zazzage kasa tsabar tsorata ganin abinda gadanga yake shirin yi
   "Yeah bross ba saika wani karya masa hannunsa ba please kazo kaji da Cinderella ni oh! Tunda Allah ya tsiratar dani"

   Cike da takaici kawai ya watsar dashi wajen yan uwansa jin shakiyancin da lady saudat take yi masa ita a koina bakinta bai taba shiru a koma kowanne hali mtsew!,,, shi kowa wancan butoramin Chinese din  Allah ya taimake shi anything is going according to plan if not wannan katon da saiya bambance tsakanin aya da tsakuwa although shima wannan pah ba kanwar lasa bane cos yaga kamar har yafi double C

    Duk wannan abinda ke faruwa DAGA hacker,lady saudat da gadanga ne kawai suke ji,,, Cos a yanda ma lady saudat take babu ta yanda za'a CE magana take

       Cikin wani irin azababban sauri gadanga yayi karaso wajen lady Saudat take a tsaye yana mai zubewa bisa gwiwowinsa hade da kifa kansa kasa alamar tsabar ladabi ga shugabarsa musamman da yake ganin a halin yanzu ya Gaza aikinsa
"Ki gafarce ranki ya Dade bisa gazawa akan aikina Dana yi!...."
Ya fada cikin harshen China da karfi ta yanda wayannan Chinese zasu ji

     Yayinda suma Chinese suka zubo musu na mugiya harma suna neman manta abinda ya kamacesu

     Hannunta kawai lady saudat ta sanya cikin gashinta tana wani irin barbaza shi cikin tsabar mulkinta da tsabar kasaitarta ba tare data CE dashi kalma daya ba!,,,
Tana mai dan jan gefe da kyar hade da cire facemask din dake fuskarta wacca ta nuna gaba daya bacin ran duniya yana tattare da fuskar...Ta wutsiyar ido lady saudat ta kalli bangaren wayannan Chinese da gaba daya suka zubo musu na mujiya kamar zasu cinye su nama danye da alama suna jira ne tayi abinda take shirin yi yanzu koma su dauki mataki a Kansu

    Ganin hakan yasa lady saudat ta kara tsare gida fiye da Wanda take ciki tun farko Wanda yasa wayannan Chinese suka sake sakankacewa akan ita pah wata Babbar kwaron CE duk da haka basu FASA niyyarsu ba

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now