ZAHRA TAWA CE 38

476 31 0
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖


💞💞💞
*ZAHRA TAWA CE*
💞💞💞


*FATIMA ZOIS*


Dedicated to *BABBAR YAYAH*
(ramby *011*)



Page3⃣8⃣


"Suna ji suna gani basu da ikon hana su haka Aliyu haidar da Umar faruk suka tafy,
kowannensu dauke da hawaye kwance a fuska suna waving juna,Wanda sai a yanxu ta gane Ashe kallon karshe ne har suka bacewa ganin su."

"Hafsat tana ganin ta daina ganin aliyu haidar take anan ta zube a kasa ta fara wani irin kuka mai cin rai da taba zuciyar mai sauraro."

"Ni'ima kam dama tuntuni bata daina risgar! kukan da take ba cos Allah yayi mata saurin kuka,
ganin hafsat da kanta tana kuka abinda a rayuwarta tun tasowarsu tare baifi ta kirga ganin zubar hawayenta ba, Hakan ya kara karyar mata da zuciya take itama ta zube a wajen tana sake kara sautin kukan iya kafinta."

"Hajia Fatima itama tabi sahun su, _Aleefriend_ da bintu suma ganin iyayen nasu suna kuka tuni suma suka fara, duk kowah da wannan tsakiyar Daren."

"Da kyar da sidin goshi idress ya lallashe su suka shiga cikin gidan tare da haduwa a cikin babban falon,"

"Gaba dayansu babu mai bawa wani hakuri a cikin su idress ne daman koma shima din ya gaxa hakan yasa yabi sahunsu,"

"Idan wannan ta gama kukan nata, toh a lokacin wata zata dauka a haka dai,Da kyar suka samu damar maye gurbin kukan Nasu da sumbatun bankwanan da suke zuwa adduo'i."

"Jin nauyi tare da sakin da jikin bintu yayi ne ya sanya hafsat tabbartarwa da tayi bacci daga jin alama bama yanxu tayi baccin ba,sai faman sakin wata irin ajiyar zuciya take tamkar zata hade zuciyar gaba daya!."

"Gyara mata kwanciya tayi hade da sake gyara mata zaman katuwar rigar sanyin dake jikinta tana mai kare mata kallo tamkar yau ta fara ganin ta,zata iya cewa ko sanda aka haifi bintu bata yi mata wannan irin kallon ba,"

"Ji take a jkinta tamkar wani Zai faru da ita hade da diyarta!...ji take tamkar wani Abu Mara dadi zai gilma tsananinta da soyayyar diyarta!!...Ji take tamkar wannan kallon da take mata kallon rabuwa da ita ne!!!...Amma ba irin Rabuwar da take ji bace yayin rabuwa da mijinta aliyu haidar."

"Sake tsananta rokonta tayi ga diyarta har saida bintu ta fara motsawa tana kara jin wani sabon faduwar gaba tamkar kirjin nata zai fado kasa,Kowanne second koma wannan faduwar Gavan karuwa take babu kakkautawa."

"Wayar dake hannunta ta samo ta laluba ta sanya a aljihun rigar sanyin dake jikin bintu in case of in cases,Tana cigaba da karatu addu'oin Neman tsari

"Kallonta ne yake kan hajia Fatima da wani irin baccin wahala ya saceta!,Daga gani ba don sarkin barayi ya kawo ziyara ba da babu inda zata tafy,Hannunta koma _aleefriend_ ne kamkame da ita tamkar wani zai sace shi ne."

"Cigaba da nazarinsu tayi har idonta ya sauka akan Ni'Ima da take zaune ta kurawa aleefriend idon tamkar ranar itama ta fara ganin sa lokaci_lokaci komah tana share hawaye dake zubu mata."

"Wani sabon tausayi ne ya sake kama hafsat ganin yanda takewa _aleefriend_ wannan kallon,Tunda take a rayuwarta bata tunanin akwai wata uwa data shaku da danta kamar irin yanda Ni'Ima da _aleefriend_ suka shaku don Ku Ni'ima akan _aleefriend_ zata iya fada da ko ma wayye zata iya yin koma komai a kansa,Irin wannan kunyar mah da ake nunawa akan dan farko Ni'Ima dai bata nuna ba duk cewar tana tare Da surukarta,"

"Abinci bata iya ci idan ba shi,Girki mah kansa tare suke yi,bacci tare Duk wani aiki da zata yi tare suke yi da danta,Bata tava walwala Indai har taga dan NATA bai cikin walwala shima,
duk cewar ba kowa ke gane _aleefriend_ yana cikin walwala ba ko sabanin haka cos fuskarsa kullum yanda take haka take a ganinga babu wani canji,"

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now