145

466 39 6
                                    

  
   Rawa jikinta ya kara fiye da farko , muryarta itama na rawa yayinda hawaye ke zuba a idaniyarta ,
    babu abinda yake kara tsoratar da ita da gadanga irin yanda taji dazo yana yiwa boss da mukarabbansa magana cikin dakakkiyar muryarsa da gwanda taji rugugin aradu zai fiye mata sauki akan taji muryarsa, , , sake tunowa take da yanda su kansu boss a tsorace suke suna wani kaffa_kaffa da shiga hankalinsu duk irin mugunta irinta boss, , , Abeg! wacece ita kowa da har zata ce gadanga will be good to her huh!?

  Sake jin muryar gadangan tayi cikin sanyinsa da sanyin halinsa wanda yabi nutsuwarsa taji yana girgiza kafadarta
   "Lady are you okay?"

   Kamar wacca ta tashi daga doguwar suma ta bude lumsassun manyan idonta tas! A kanshi karshen tsorata da firgita ba sai an fada ba ta tsorata , Kallo daya tayiwa fuskarsa ta dauke kanta ganin yanda idanunsa suka canja ba yanda ta saba gani ba , , ,tuni ta sake maida hankalinta ta sake shiga taitayen ta,  tana kara tabbatar da lalle wannan the devil monster gadanga take tare ba da innocent prank haidar ba

   Kura mata ido gadanga yayi kamar yaga wata halitta data bayyana a jikinta daga gani yama rasa mai zaiyiwa zahran ne?,  shi dai bazai taba zama a inda zahra take batare da yana tare da ita ba!, , , sannan bazai iya jure wannan tsananin tsoron da take nuna masa ba

  Dago da fuskarta yayi domin ta kalle shi he's no one but the scaring subordinate , , , Rintse idonta tayi tana magana da kyar da makyarkyata
    "Am okay!, , , sakar min hannu please...ina son na shiga gida Sa'adatu ta tafi ta barni!"
Ta karasa maganar da kokarin banbare hannunta daga nasa bayan ta ture hannun daya daga fuskarta , bata taba sanin haidar yana da karfin dahar ba zata iya kwace hannunta daga lage_lagen hannunsa ba sai yau , , ,Tayi amfani da duk wani karfin da Allah ya bata But amma ta gaza kokari take sosai pah ,  amma ina! Ko gizau baiyi kai kace wani katon dutsen take turawa  har wani karamin gumi ta hada alhalin rikewar ma bata kirki yayi mata ba ,

     yayinda shikam gadanga lalacewa yayi wajen kallonta musamman yanda dimple point dinta ke lotsawa idan tana bada karfinta wajen kwace hannunta, , ,  rolling dake kanta tsabar wahala duk ya subale kyakkyawan bakin kwantaccen gashinta ya bayyana yayinda gumin dake tsattsafowa a goshinta ya sake kwantar da kananun gashin dake wajen luf_luf harma da sajen gefan fuskarta, , , Shifa ya manta ashe wahala take sha cos he's really enjoying the moment

  Sautin shesshekar kukanta ne ya dawo dashi duniyar da take , , , Oops! Lady ashe kuka take
   "Ka sake min hannuna pls!"
Ta karasa maganar da sake kara volume din kukanta kwata_kwata ta kasa kallon fuskarsa

   Cikin rashin fahimta ya kalleta saboda shi kam sam_sam! Baisan takamaimai abinda ya saka zahra take masa haka ba cos no matter what indai yana tare da zahra shi ba kowa bane face minor subordinate da yake jiran umarni daga gareta , sam! Ya manta yanzu pah anyi walkiya komai ya bayyana ga zahra tasan wayye shi !

  Dan shagwabe mata fuska yayi kamar yanda yake mata magana sometimes cos shipah a iya tunanin sa baiga abinda zaisa zahra ta dinga wannan strange acting ba
"Lady nine bross dinki pah menene don rike hannun ki huh!?, , , Gosh! she's more than strange"
Ya karasa maganar ciki_ciki hade da dan turo bakinsa gaba amma ita kam zahra tana ji saima
Sake maida hankalinta kan son kwace hannunta tada yi tun kafin ya kashe ta da kissar sa don tsilan uwanci zaice baisan menene alakar su bane yanzu da har yake da wannan courage na irin wannan maganganu ehn!?, , , he's driving me crazy abeg!, , ,  kai amma Allah yayi dan kusun uwa indai haka yake
   "Ni dai ka sakarmin hannu Sa'adatu!.?.?.?."

  
  Kare mata kallo yayi ganin she's serious now abinda ya fara tunowa a dan karamin tunanin sa shine kiss da suka yi sannan zuwa ceton ta da yayi a toilet , , , yana tunanin kodai har yanzu borin kunyar ne take yi amma pah wannan abun da take she's fucking serious abeg! What's with her ?, , , magana yayi cikin sanyin jiki
  "Lady guduna kike ?"
Ya fada yana tsare ta da  idanun sa da suka fara canja kala bayan yanda suke a birkice 

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now