GADANGA 09

1.1K 63 6
                                    


💖💖💖💖💖💖💖💖

💞💞 💞
*ZAHRA TAWA CE*
💞💞💞

*FATIMA ZOIS*

Dedicated to *BABBAR YAYA*
(Ramby *011*)

*Ramadan Kareem*
🌙🌙🌙

Page 9⃣

Saurin dauke zahra gadanga yayi yana mai rufeta da Suit dinsa wacca take numfashi da kyar Tare da boyeta a wani waje kafin ya gama da wayannan kananun yan iskan

Cikin azabar ciwo Najib ya baje a kasan tare da tsayawa kallon gadanga cike da mamaki,
"Ya akai yasan yarinyar nan tana nan?,
Ya akai yasan Cutar da ita zan mu yi?,
Yama akai yazo ba tare da sun sani ba,
Anya kowa gadanga mutum ne!?"

Wata xuciyar ce take sanar dashi
"Ah! Haba Najib kada kayi sanya mana yanxu ne lokacin ka,
Nasan a yau zaka bar tarihi A fadin duniya na Kaine Wanda ka fara kama gadanga"

Cike da kwarin gwiwa ya tashi daga kwancen da yake cos yaji dan dama_dama bawai don ya daina jin zafin faduwar da gadanga ya cillo shi ba tare da commanding din yaransa

"Ku kamo min gadanga don kaza_kazarshi a mace ko a cos daman suna nemansA ruwa a jallo,
koda bai kawo kansa ba mu zamu nemeshi"

"Yeah sir"
Suka hada baki kamar wasu masu waka tare da antayawa Da gudu cikin fushi da fushin wani zuwa wajen gadanga da yake a tsaye a wajen
Sai faman wani kururuwa suke Kamar idan suka je xasu cinyeshi nama danye

Suna zuwa duka daya gadanga yake yiwa kato saidai ka ganshi durkushe a wajen,
Duk da cewar baya kashesu  amma yana musu dukan da basu iya tashi su cigaba da fadan

Kafin wani lokaci tuni gadanga yayi musu kaca_kaca cos ya karar da fin Rabi da quarter su

Ganin gadanga yana musu barna ya sanya sauran bodyguards din da suka rage gaba daya suka ja da baya,
Kowa yana shakkar tunkarar gadangan

A fusace Najib dake gefe yana kallon komi ke faruwa yace
"Ku kamo min wannan banzan a Raye ko a mace,
Idan ba haka ba kunsan makomarku"

Da gudu suka sake tunzura cos sunsan koma dai miye gwanda hukuncin gadanga akan Na alhaji bala da yaronsa,
Cos duk tsiya gadanga kamar yanda suka sani bazaiyi kisa ba amma su alhaji bala pah!?,
May be har Wanda basu ji ba basu gani za'ayi hukuncin dasu
Tare da cewar basu taba haduwa damutum irin gadanga ba
 

Duk wannan tashin hankalin  fadan da suke gandanga yana tsaye a wajen da yake bai ko motsa ba,
asalima communicating yake da hacker Wanda duk kwakwar mutum bazaiji mai suke fada ba

Haka dai mutanan alhaji bala suke ta kawo masa duka hannu da kafa harma da mugayen makamai amma ko kwarzanar jikinsa sun kasa, maimakon haka sai sune ma suke shan mazga

Cikin wani irin fushi najib ya  tashi dga inda yake zaune duk da ciwon da daya ji a cewarsa
"girman kan gadanga yayi yawa wannan ba komai bane sai raini ga koma banzayen yaransa da mutum daya tal!ya gagaresu."

Cikin harzuka da jin kai tare da karfafawa kansa gwiwa duk da yana shayin gadanga don har yanxu bai gama dawowa dai-dai ba amma saboda bakar zuciya irinta najib hakan baisa ya rusuna ba ya fara magana

"kai don kaza_kazarka har kana ganin ka isa ka ja damu?,
kasan ni wayye? koma wayye ubana?,
To bari kaji in fada maka mune Wanda muka gagari kowa sannan muke datse wuyan mutane irinka masu yi mana shisshigi cikin lamuranmu,"

"Wannan yarinyar meye nata a ciki da har zata tuna mana asiri dai_dai lokacin da siyasa ke gabatuwa huh!?,
To ina umartarka  da kayi gaggawar fita a cikin wannan lamarin idan ba haka ba..."

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now