143

274 29 3
                                    


 
  "Granny ina zan samu leda na saka kayan nan namu ne da muka cire?"
#lady saudat wacca tsantsar bacin rai ya tabbata a kanta musamman duba da yanda ta hade fuskarta kai baka ce tasan yanda ake dariya ba

    "Uh_oh!,  wannan fuskar pah?"
#doctor aisha tana mai cigaba da kallon yanda lady saudat take abu a zafafe

  
   "Ki tambayeta abeg! Daman tana da irin wannan fuskar bayan wacca take da ita mai dauke da fara'a?"
#dr.sa'adatu cikin yanayi na mamaki mai hade da zuzutawa

   "Wannan fuskar haka , abeg! Ji wasu kumatun ta a wajen kamar kullin gyada..."
#dr.aisha cikin yanayi na tsegumi irin sai yanzu nasan ai lady saudat tana da kumatu

A dan fusace lady saudat tace
"Granny..."

Kota kanta basu dr.sa'adatu itama ta dora da nata fadin
   "I wonder wannan kumatun nata kamar ba'a siririn jikinta yake ba..."

"Granny please mana..."

Kamar yanda lady saudat ta fada a shagwabe mai hade da rigima haka itama dr.aisha tayi tana mai fadin
   "Eesh! Munji"
Sannan ta dora da kunkuninta mai hade da sababi irin na tsofi
        "Aigoo!...wannan fuskar taki abeg tana tsorata"
Yayinda take mika mata leda

    Sake hade ranta lady saudat tayi fiye da farko wanda su kansu grannies saida suka sha jinin jikin su,sai faman magana suke kasa_kasa "what's with her?, , , what's with that red face" gashi nan dai su kadai cos ita dai lady saudat ta ki kula su
Yayinda mrs.boss da mrs.li suka karasa shigowa

   Sallamar mrs.boss suka fara ji wacca  itace a gaba cikin shigarta ta kamala da mutunci , kana ganinta kasan yar mutunci ce koma ita dinta mai mutunci ce ...kallo daya mutum zai yi mata ya tabbatar da tana da yalwar fara'a sannan koma zata yi sanyin hali
   "Assalama alaikum mums?"

Yayinda mrs.li take biye da ita cikin wani irin tsantsar gayu da aji irin na mata first class da suka yarda da kansu ta kowanne bangare kai baka zata bawa 40 years baya ba ,
   gaba daya suturar jikinta kama da tupapi, takalmi, accessories, glass , jaka da sauran su dukkanin su lastest desiginer ne na famous brand
   "Hello mummies?"

Kamar masu waka grannies suka amsa musu
   "Wa'alaikum salam?, , , Hello mrs.li"

   Cikin tsabar mutunci da girmamawa suka gaida grannies , sannan suka zauna suka dan fara hira as expected yawon hira kawai suka zo kai kace kawaye ne,
Hirar koma yawanci neman shawara ce ko akan zamantakewar auran su ko akan kasuwancin su, , ,ko koma akan neman haihuwa da suke har suke fadin kodai adopting yarinya zasu yi daga gidan marayu cos a duniyar su suna son yara mata,  yayinda su kowa su grannies da zuciya daya suke basu shawara wanda ko y'ay'an cikin su iyakacin abinda zasu iya yi musu kenan

    Sun dade suna hirar su lady saudat da zahra suna jin su , amma ko kwakkwaran motsi basu yi 
   "Yaran nan wai  baku iya gaisuwa bane?"
#doctor sa'adatu ta fada ganin tuntuni take musu alama hannu da idanu akan su gaida mrs.li da mrs.boss amma basu yi ba ,
Karshe ma zahra ita rufe idonta tayi a zuwan tana bacci , yayinda lady saudat ta sake hade ranta fiye da farko

   Da dan mamaki mrs.li da mrs.boss suka kalli inda granny take kallo cos sudai tun shigowarsu basu ga kowa ba, yayinda suke hada baki wajen fadin
"Su wayye?"

   "Patients din mune!, , , Eesh! Ban san mi nayi ba Allah ya hada ni da masu taurin kai irin wayannan yaran"
#dr.saadatu ta fada cikin yanayi na zuzutawa

A tare suka hada baki wajen fadin
      "Kyawawa yam mata"
Saboda a duniyar suna son yara a cikin yaran ma mata ,  saidai gaba dayan su Allah bai basu haihuwa ba, koda sun haihuwa Allah da ikonsa sai yaran su koma gare shi , kullum burin su na karshe shine su samu yara

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now