ZAHRAN GADANGA 105

469 38 10
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*ZAHRA TAWA CE*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIMA ZOIS*
Wattpad #FATIMA ZOIS

Dedicated to *BABBAR YAYAH*
( _MAMAN YASNA & YAMEEN_)

PAGE1⃣0⃣5⃣

Cike da Karin mamakin Wanda take ciki tayi saurin aje kunun gyadar dake hannunta hade da sauke shi da karfi kan dining table din sannan ta karasa shanye Wanda ta cika bakinta tam! Dashi kamar tana sha da mutum dubu tare da cewa
"What!????...brossly shi ya kawo ni gida kace?"

Ta karasa da karfi kamar ta manta wannan zancen a sirrance ake yinsa tsabar tsegumi ne irin na affan da bazai iya boyewa ba yasa yake fada mata cos Abba yake duk Wanda ya fada mata Yasan sauran!
amma shine take Neman bankada min asiri
....Eesh! She's seriously Impossible

Duka Affan ya kai mata a fusace hade da sanya hannunsa a baki cos da alamar wannan bata shirin ta manta magana cikin sirri ake yinta
"Sheesh!..."

Sannan ya fara magana a fusace kaza_kaza kamar ya dake ta
"What loquaciousness!...Yeah didi bana CE miki ba wannan magana a sirranca zamu yi ba huh!, yanzu idan Abba ya ganni ina fada miki nine a cikin matsala bake ba,
Shiyasa wallah wani lokacin didi ke rashin haduwa CE...Kina mace amma har yanzu ko dan tsegumin nan irin naku na manta baki iya ba Eesh!..."

Cike da borin kunyar kwafsawar data yi ta ce
"Hehehe!, karamin kani kasan abun ne da mamaki a cikin sa amma insha Allah na daina okay!"
Ta karasa tana mai kara bulbula kunun gyadarta da karshen haduwa ya hadu

Hadiyar yawu affan yayi cike da kwadayi da koma Neman compain zahra ta bashi kunun cos tun dazo duk wannan abun da yake kunun yake yiwa amma shiru kake ji kamar Malam yaci shirwa

"Tun yaushe kike cewa kin daina amma baki daina ba wannan muryar zuzuta abun taki a wajen ba dole su Abba su fito ba nikoma ki barni cikin cukurkudaddiyae cakwakiwiya huh!"

Tunda taji affan ya fara wannan bambamin maganar tasan mi yake yiwa,
hakan yasa a matsayin ta na mai Neman abinda take so kawai tayi shahadar kuda ta hanyar bAwa affan kununta fuskarsa nan kamar an aiko mata da sakon yau za'a kundumeta
(Wato dai fans sarkin kwadayi da sarkin rowa ne suka hadu)
"Am so sorry little ga wannan ka kura"

Cikin murnar abinda ya fitar da rai ya samu affan ya faki ido yadan kalli kunun Adam sace ba tare daya dauka
(Wato dai wannan abun namu na hausawa za'ayi kara...)
"Hehehehehe! Toooooh!...Babbar Yaya harda kunu haka..."

Cikin karin haushi zahra ta kai hannun zata dauke kununta cos Allah ya sani daman kyautar bata kai har zuciya ba
"Idan ba xaka ansa ba bani..."

Kafin ma ta karasa kamar walkiya tuni affan ya dauke cos yasan halin zahra tas! Zata dauke kunun ta barshi da hadiyar yawu
"Yeah didi sai kace ba'a cikin hausawa kika tasoba huh!, daga yin kara shikenan koma..."

Kwafa kawai zahra taja tana mai sake gyara zamanta a dining table ta yanda zata ga affan sosai cos ka'ida ne idan affan yana bayani saiya fayyace komai harda gwaji ma yake
"Ina saki baka Abu ka tsaya kana yimin wannan maganganun kara yake komi ka gani "

Daga cup din kunun kawai affan yayi bayan wasu seconds da baifi 60 seconds ba zahra saidai kawai ganin tsirarar cup tayi ya shanye tas!

Cikin tsabar mamaki zahra ta ta saki baki da hanci tana kallonsa
"Huh!..."

"Hehehe! Ai ba sai kin karasa abinda kike son fada ba Didi Indai har zaki dinga bani kunun nan koyaushe momma tayi miki koda tace kada ki bawa kowa,
A takaice dai kamar dai yanda kika yi yanzu"
#affan ya karasa yana shirin sake daukar cup din alamar bai karasa ladansa ba

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now