she's mine 128

508 43 13
                                    

_Assalama alaikum,_
_Bahaushe yace idan laifi yayi laifi saidai mutum yace ya tuba!, Hakan nima ta wajena abun yake nasan nayi muku laifi tho am always like that!...Amma kada ku gajiya ko kara hakuri dani , nima kaina ina son nayi na gama da ZAHRA TAWA CE cos i have more for you , Bisalam_

Wannan page din na sadaukar dashi gaba daya ga masoya da basu gajiyawa dani a koda yaushe ANTY AMINA LADAN BUNZA, sister yusra da sauran ma wayanda ba zasu lissafi a wannan dan karamin page ba!...nasan kaunar ku DAGA ALLAH NE! babu abinda zance sai godiya ku gane FATINMOMMA tana tare da ku

Ba karamin mamaki gadanga yayi ba daya shigo dakinsa yaji muryar zahra kasa_kasa tana kiransa akan don Allah ya bude kopan idan ta Ganshi lafiya ko second daya ba zata kara ba zata fice abunta,
yayinda lady saudat yake jin sautin fitar numfashinta a hankali alamar bacci ne ya dauketa ba tare data shirya ba duba da irin yanda take sakin ajiyar zuciya daga ji tasha kuka ta koshi

Cikin karyewar zuciya gadanga ya aje karamin towel din dake rike a hannunsa yana goge gashin kansa yana mai zuwa bakin kopar yayi zaman dirshan kamar yanda yasan yanxun haka Zahra take

Cikin makoshinta yaji tana magana wanda ko fita da kyau baiyi da alamar tasha kuka harta gaji ga koma gajiya ga stress akan haduwa da gadanga data yi talkless of maganar da gadangan ya fada mata akan iyayenta wanda in bacin allah yayi haidar xai shiga cikin wannan hargitsin na yau har ya mantar da ita wannan stress da take ciki dababu mamaki yau kwanan asibiti zata yi
"Please bross ka bude kofan uh!, ina ganinka lafiya xan tafy, Bross please ka bude kofan zanyi treating hannunka kada ya koma something bad..., bross wa ya ji maka ciwo koma bayan wanda kaji da safe?... wanne mara tausayi ne haka bross!, bross ka fada min?"

Gashi nan dai maganganu iri_iri wanda ita kanta bata san tana fadar wasu ba , daga ji koma kasan ba yanzun ta fara wannan magangun ba

Cikin tashi muryar wanda daga ji kasan ya galabaita shima yake magana da kyar har muryar tasa bata fita sosai
"Lady kije ki kwanta , i don't want you to see me in this condition please!"
Ya karasa maganar da jan kalmar "please" wacca ta makale masa a makoshi

Firgigit! Zahra ta wartsake daga wannan yanayi data ke tana mai yin magana cikin yanayi na "is my pleasure to hear ur voice"
"...but bross are you really okay?"

Murmushi gadanga yayi cikin karfin hali kamar wanda murmushin yake masa wahala hade da gyada kansa kamar zahra tana ganinsa
"Am okay lady ,zaki iya tafiya please"

Murmushi zahran tayi mai sauti hade da magana cikin mayen bacci
"Okay bross zan tafi...kayi bacci mai dadi..."

Bata kai ga karasawa ba yaji kawai shiru kamar anyi ruwan sama an dauke alamar ta bingire a wajen bacci musamman daya ji alamar kwanciyarta ,
A hankali yadan kira sunanta domin ya tabbatar data yi bacci yaji saima ajiyar numfashi na bacci data yi
alamar baccin nata ya natsa kamar ba yanzun nan ta fara baccin ba kai daga ji ta gama gajiya abinda take bukata kenan hutu, hutun ma bacci

Ajiyar zuciya shima ya saki yana mai sake mannewa a jikin kofan kamar xai shige cikin ta yana mai cigaba da tunanin rayuwar reporter harun abubakar harun hade da tunanin rayuwar mahaifiyar zahra da ita kanta zahra

Bai san ya dade yana wannan tunani ba saida yaji Muryar lady saudat tana magana cikin bacci
"Eesh! Har yanzu sa'adatu bata daina magana idan tana bacci ba,
hash! So disgust"

Magana take cikin fada tho cikin bacci take
"Hash! My jhala ke ba zaki iya bacci ba sai kina shiga jikin mutum dole huh!,
Dallas! Ni dauke wannan katuwar cinyar taki"
Ta karasa maganar da gefar da kafar zahra gefe

Juyi zahra tayi na alamar taji zafin gefar da kafarta da lady saudat tana mai yana magana a sangarce hade da shagwaba mai tattare da sharri
"Ah!...ouch!...it hurt,
Oh my leg!...that really hurt ah! Bross ta karya min kafa"

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now