Mission impossible 118

760 38 2
                                    

💖💖💖💖💖💖💖💖
*ZAHRA TAWA CE*
💖💖💖💖💖💖💖💖

*FATIMA ZOIS*
Wattpad # FATIMA ZOIS

DEDICATED TO *BABBAR YAYAH*
( _MAMAN YASNA & YAMEEN_)

_please fans addu'ar ko is highly needed allah ya bani sa'a akan abubuwan Dana sa a gaba,,, da addu'ar sauran al'ummar musulmi_
*AMEEN SUMMA AMEEN*

Page1⃣1⃣8⃣

Wata irin shewa Boss da mukarrabansa suka saki,
Masu sujjadar shukur nayi masu kiran Jesus cris nayi masu kiran sunan gumakan su nayi musamman ga Yan kasashen India da sauran kasashen Asia tsabar tsananin farin ciki daga karshe ma kawai kowannen su ya dage katon tumbinsa suka fara taka rawa

   Yayinda shikowa barrister abubakar sadeeq tsabar rudewa CE da tashin hankali tasa har addu'ar da yake a cikin zuciyarsa ta fito fili Wanda a lokacin da za'a yanka shi bazai ce ga addu'ar da yake ba;
   Saboda Tsabar tsananin firgici ne ya sanya koda xaman ma ya kasa yana tsaye gaba daya tashin hankalin sa  yakai kulolowa wajen tashi duk kowa da tsabar hajijiya da yake ji tana kokarin zubar dashi hade da ciwon da yake nukurkusar kashinsa

   Yayinda shikowa uncle Abbas tsabar bakin ciki ne ya sanya shi shima Kawai DAGA kansa ya shanye drinks din dake hannunsa ba tare daya yabar ko digo ba even though babu wani Abu da aka sanya a cikin nashi drinks amma haka nan yake jin tunda har zahra tasha wannan Abun shima dole yasha

   Shikowa whizz khaleepah Kawai timing yanda zai samu nasara akan zahra yake still idonsa na kanta kamar zai cinyeta nama Danye visa la'akari da yanda lokaci_lokaci idan ya kalleta saiya lashe wannan tafkeken labben NASA kamar wani tsohon maye

    Gaba daya wajen tun DAGA kan boss da mukarrabansa masu tikar rawa na tsabar murna har zuwa kan uncle Abbas, Barrister abubakar sadeeq da detective tanim Wanda hankalin su yakai kololowa wajen tashi in banda addu'a babu abinda suke,
kallon zahra Kawai suke wacca ta dan DAGA nikab dinta tana shirin shan drinks din dake cikin cup din dake hannunta ,Wanda wasu a tunanin su ma tasha

    
     "Kai kaga wata kyakkyawar fata kowa!?"
# wan ho li ya fada cikin wata irin magana ta tsabar feeling da shauki yana mai rungumar boss dake gaban sa ba tare daya Sani,Har yana Jan gemun boss tsabar kallon da yake yiwa zahra yana mai sauke nishi kamar Wanda ya kwana gudu

   Boss shima daya shiga wani halin harma ya Lola zuwa wata duniyar yana aiyana yanda Zaiyi da zahra idan har ta shiga hannu sakamakon ganin habar zahra a kokarinta na shan wannan drinks baisan sanda ya dawo duniyar zahiri ba jin wata irin azaba a gemunsa tamkar ana kwashe masa wajen da shovel na Wuta

     Dubawar nan da xaiyi sai gani yayi Ashe wan ho li ne yake ja masa gemu da iya dukkanin karfinsa kamar ya samu kayan wanki ,yana koma shafa masa wannan kurtsetsen tumbin nasa hade da fitar da wani irin sautin kamar mai gurnani
shi bai yarda ba waishi feeling ko!?,,,zai ci Abu takazaniyarsa kowa

  
      Ba tare da wani dogon turanci ba boss ya takarkare da dukan karfin da allah ya bashi ya taftsawa wan ho li mari  ji kake tassss! Kamar fashewar taya Wanda yasa gaba daya mutanen dake wajen da Wanda basu wajen irin su double C shima da mukarrabansa Wanda suka shiga halin shauki kowanne su dawowa duniyar da yake ciki

    Ba tare daya bari wan ho li yayi magana ba ya sake maida kansa kan cinema yana mai cigaba da kallon zahra wacca har yanzu basu ga empty cup ba tare da  cewa
   "Kadan ka gani DAGA kyau irin na wannan YAR shilar"
   

     Kafin wan ho li yayi magana; maganar double C ta karade wajen hade da dokan dodon kunnen duk wani mahaluki dake tare dasu in person ko Bluetooth kai kace sai tashi kunnuwan wayannan ta'allikan ne!
"Tasha!"
    
    
"Kai Dallas wayye ya fada maka bata sha ba"

ZAHRA TAWA CE Where stories live. Discover now