1

4.5K 69 0
                                    

_SIRRIN D'AUKAKA_

~A. AYSHA J.B~
_Wattpad@ayshajb_

®️🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

_♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/

*SADAUKARWA GAREKI MY Rahama*
_LADINGO UMMUH FAREESA_ '''(Kawar Amana)'''

'''Wa sallallahu ala Akaramil Mursalina Aj'main Muhammadin wa'ala alihi wa Sahabihi wa,sallam'''

PAGE ONE..

"Baba burina kasha kafini bukata dan Allah." kawar da kanshi yayi gefe duk da jikinshi baya motsi sakamakon ciwon dake tattare dashi bakinshi ma a karkace yake kwalla ne ya gangaro masa da sauri ta ajiye kofin tana share mishi hawaye "Baba na ɓata maka rai ko? toh kayi hakuri insha Allahu bazan kara ba." a hankali ya soma magana "Jiddah ni baki min komai ba, hasalima bana bukatar komai ya shiga bakina.. da sauri ta dakatar dashi "karkace haka Baba in baka shaba maganin fa? nafi son lafiyanka fiye da komai domin kai da mama kaɗai kuka ragemin kune gata na! kunne bangon da inna jingina ajikinku nake jin daɗi ku kaɗai ne farin cikina kayi hakuri kasha kaga jiya bakaci komai ba."

"Jiddah ina ganin gazawata! ni yadace in fita in nimo muku abinci ni yadace na muku komai keda mahaifiyarki Amma dubi halin da nake ciki kalla fa? jiddah na gaza muku wannan abubuwan gashi dangina wanda ya kamata su tsaya su temakeni duk sun gujeni kowa guduna yake sabida banida kuɗi ni talaka ne!.." kukane ya kwace mishi Mama da fitowarta kenan daga banɗaki ta karaso tare da durkuwa a hankali ta ajiye butan hannunta dakyar ta miƙe sakamakon cikin jikinta dayafara tsufa "Kayi hakuri Allah yana sane damu kuma wannan jarrabawace bawai don baya sonmu bane a'a yayi haƙan ne don ya gwada imaninmu kuma a kullin muna gode masa Allah ya ubangiji Allah kai kayi Adamu kayi hawa'u Allah bamu da kowa bayan kai Ubangiji ka sassauta mana Allah ka kawo mana agaji Alfarman wannan rana ta juma'a kabawa Mijina Usama lafiya" jiddah dake jikin mahaifinta ta amsa da "Ameen mamana. "
Dafa cikinta tayi tare da girgiza kai rabonta da abinci tun jiya shima kanzone wanda jiddah taje makota tayi wanke wanke ta samo musu Allah kenan! me yanda yaso da bawanshi "Asama'u ɗauki kokon nan ki sha." mama tace. "a ah Usama kai yafi dacewa daka sha domin kasha magani." usama yace "Asma'u bana son jayayya kin fini bukata bani da burin da yawuce ganin farin cikin iyalina daga shi se bashin Mu'azzan dake kaina inna roƙon ka Allah ka billomin da hanyar da zan cika wannan burin nawa kafin mutuwata.. "kabarmu dawa usama?. "Akwai Allah.."
Juyo da kanshi yayi ga Jiddah "ɗauki ki baiwa mahaifiyar ki Allah ya miki Albarka ubangiji ya tsaremin ke da mutuncinki Allah ya rabaki da sharrin samarin zamani!." ɗaukan kunnun tayi ta nufo mahaifiyarta dashi "buɗe bakinki nabaki mamana." ba musu ta buɗe bakinta domi Ɗan cikinta harya fara motsi tsaban yunwan dake cinta cokali kurɓa uku taman kokon ya kare cire kofin jiddah tayi a bakinta Ahankali Asma'u ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata wani irin yunwane ya taso mata.

Gurgar da kofin Jiddah tayi tana kiran sunanta "Mama mamana meya sameki?." cizewa tayi tare da faɗin "bakomai Jiddah..."

Shuru suka zauna chan Jidda ta miƙe butan da mahaifiyarta ,ta ajiye ta ɗauka roban fentin da take zuba ruwa ta nufa shuru tayi sakamakon ganin bokitin ba ruwa "Sauran ruwan na zaga dashi." cewan Mama bokitin ta ɗauka "bari inje in samo ruwan" fatan Alkhairi suka mata bayan ta fita Asma'u ta matso jikin mijinta kwantar da kanta tayi a jikin taburman da yake kwance "lna son shafa fisƙanki babu halin haka ko zaki temaka ki ɗauki hannuna zuwa ƙan fusƙan taki?" wani irin marayan kuka tasa a hankali sautin kuƙan nata yake fita hannunshi ta kama takai saman fisƙanta amma lna ko motsi bayayi dalilin haka yasa ta kara sautin kuƙan nata "meyasa haka! meyasa wasu mutanen basa duba gobensu! meyasa wasu mutanen suke manta alkhairi ? yanzun sakamakon temakon kenan? usama duk kai kajawo mana wannan masifar meyasa ka Auro mana masifa jubeni da yarintata na koma tsohuwa kalleni... kalli cikina wai yau mune abinda zamuci yake gagarar mu? me muka mata?, takwashe komai Allah kana gani ƴata ba makaranta ko ɗaya Ƴar da zamu ciyar amma i'ta take fita tasmo mana abinda zamuci Yarinyar da bata huci wanka ba amma wai yau i'ta ke ɗawainiya damu Allah ka kawo mana agaji.. "Asma'u kiyi hakuri tausayinta naji gani nayi kowa ya gujeta gani nayi ta fara fusƙantar tsana da tsangwaman mutane kowa ya gujeta bansan haka ze kasance ba na nufeta da Alkhairi amma ta saka min da sharri ta rabani da Ɗana ta ruguzamin komai nawa kalli yanda ta mayar dani, *LAIFINA NE"* (Shima sabon buk ɗina ne yana nan tafe da yardan Allah),

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now