page 22.

509 31 12
                                    

♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

F.J.W.A

Page22.

"Dan Allah kice ya bani Yarona Wallahi bazan iya barin shi cikin wannan Gidan ba, Ummi Yarona.."
Gyatsa mai had'e da Aman jini tayi cikin tashin hankali ummi ta qwalawa Yahgana Kira da sauri ta fito "Maza temaka mu kaita asibiti" Girgiza kai Jiddah tayi cikin fitar Hayyaci tace. "Aakif Ummi dan girman Allah.." zubewa tayi jikin ummi Numfashinta na shirin barin gangan jikinta, da sauri suka fita da i'ta motarta dake bud'e suka sakata A guje ummi ta figi motar Suna i'sa Emergency aka shiga da i'ta, sai lokaci ummi ta fara niman waya, Dole sai gurin nurse ta ara ta kira wayar iyanmu tana d'auka tace "Sawdat ce lyata, Ga Jiddah tazo cikin mawiyacin Hali ki binciki Nafisat Meya-Faru kar Yar mutane ta Mutu domin Aman jini take, Sunan 'Danta kawai take ambata Bansan Me Arab ya mata ba.."

"inna zuwa" kashewar tayi tare da Bawa Nurse sannan tayi Godiya.

Da kyar suka mata alluran barci domin surutai take musu tare da fisgewa tana son fita. "Kubarni ni lafiyata Lau, ku barni na d'auko Yarona!" Abinda take fad'a kenan idanunta na rufewa "wayyo Aakif d'ina bashi da lafiya Zane min yaro tayi Allah ya i'sa min wayyo Akif.." ruf idanunta ya Rufe tana sauke numfashi alamun alluran da suka mata yayi nasaran sata barci.

Likita na Fitowa ummi ta tare ta, ofishinta suka nufa tsaban tashin hankali ummi ta kasa zama duk da tace ta zauna. "Doctor bazan iya zama ba, fad'a min wani hali 'Yata take ciki? Meke faruwa da i'ta?" Rubutu likitan tayi sannan tace. "Ummin Halima zuciyarta ya kunbura sosai Jininta ya sake hawa fiye dana baya, tana b'oye Abu a zuciyarta dalilin dayasa yayi Haka kenan.." Hoton da'aka d'auki zuciyarta Doctor ta tura mata zubewa ummi tayi saman Kujera tana kallon yadda zuciyarta ya Kunbura "Allahuma ajirni fih musibati waa'aklifni Khairan minhaa innalillahi wa'ilaihir rajioun! Yah Allah" Wani i'rin hawaye ne ya zubo mata "Dalilin tashin hankali yasa karamin cikin jikinta na wata biyu ya b'are.." runtsa ido Ummi tayi tare da fad'in "Hasbunallahu waa ni'imar wakeel"

Takardan da tayi Rubutu ta tura Mata.
"muna bukatar wa'yannan abubuwan Yanzun!" Mikewa ummi tayi ta fita da sauri Kuma ta dawo "Zuwa wani lokaci zata farka?"

"insha Allahu zuwa dare."

Gida Ummi ta koma tare da Yahgana wayarta ta d'auka ta kira Halimatu da Hanisa ta sanar musu Abubuwan da zata bukata ta d'auka tare da kud'i ta koma asibiti.

Washe gari
Sai biyun Rana alluran ya saketa mikewa tayi a zabure da karfe take son sauka daga Gadon Ummi dake sallah ba shiri ta yanke sallar tare da Rik'eta Yadda ta mike ne yasa jinin zubowa sosai Girgiza kai tayi tana cije leb'e jin yadda Maranta ke kullewa Halimatu ce ta shigo da kulan abinci Ganin Halin da jidda ke cikine yasa ta ajire Kulan da sauri ta karasa Hanisa dake Bayanta ne ta juya domin Kiran likita.

"Dan Allah ki nutsu Jiddah." Ummi tace tana sake riketa sosai Girgiza mata kai tayi "Taya zan nutsu Yarona na cikin mawiyacin Hali? Ki fad'a min Ummi taya zan samu kwanciyar Hankali yarona na gurin matar da tayi ikirarin saita kashe shi! wayasan mai ta masa Yanzun, yaron da magana ma bai iya ba, Wallahi gwara da cikin Ya fita, wannan ai masifa ce Wallahi ki fad'awa lbrahim ya bani Yarona in ba Haka ba, Kotuce zata rabumu, Ya dawo min da Yarona, Har mari na yayi dan zan d'auki Aakif. ki kalli yadda ya shimfid'amin hannunshi jikina, Wallahi Bazan bar musu d'ana ba ki fad'a mishi Ya bani Yarona kafin Hukuma ta shigo ciki.." magana take tana jijjiga kai tare da cije baki tana son kwacewa.

"Naji kiyi shuru Zai baki d'anki Meya had'aku?"

"Saki uku yamin"

Zaman dirshan ummi tayi a K'asa "innalillahi saki d'add'ai har uku?" Hannu Halimatu ta d'ora akai tare da buga salati Hanisa dake baya tace. "Amma Uncle yayi asara!"

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now