5

816 30 0
                                    

*♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
_Wattpad@ayshajb_

®️🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

_♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/

FREE BOOK

*Sadaukarwa gareki*
Rahama Real Ladingo


Jama'a ga sauki na buga kofar gidanki batareda kin sha xafin rana ba,ko kinsan SHANONO AND SODA CLOTHES AND MORE Suna bajakolin kayan Atamfofi kayan kicin tsantsara tsantsara na kece raini? To banan suka tsaya ba akwai abubuwan da suke order bayan wannan cikin aminci da kwanciyar hankali a rabu ana madalla.
Kishiga wannan group domin kashe kwarkwatar idonki.
Sannan Ga nambar daxaki iya kira ko chat da ita domin neman karin bayani
👉👉👉 08137145294
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FQ9k6e5aOljEP3s3UGqEcu

Page5
Barcin ma rabi da rabi nake yinsa domin tsoron ya taɓani nake ji can barci ya fisgeni naji ya cicciɓeni ya dora saman gadon zabura nayi tare da kurma ihu jikina na ɓari dan ko gizau be yi ba, haka ya ajiye ni tsawa ya daka mata. "Ke mahaukaciyar lnace! in banda wawanci irin na ɗan kauye me zesa ki kwanta a kasa sanyi na shigarki, lna miki Gata kina kaucewa" na tsani tsawa ban sabaji ba, domin har iyayena sukabar Gidan duniya basu taɓa tswata min ba, shiyasa na toshe bakina da hannuna kalmominsa sun ƙona min rai sosai ajiyan zuciya nake saukewa hawaye na wanke min fiska haka ya gama cimin mutumci ya kwanta abinsa takurewa nayi sosai lna ajiyan rai barci ɓarawone ya ɗauki "Bansan ki da wannan halin ba jiddah lokaci ɗaya kina kokarin fanɗarewa! raina na ɓaci in naji kina mayarwa mutumin daya amsheki batare da ya musa ba!, me akayi ko? hakuri zakiyi domin Guguwa na nan tana tunkaroki sekin tsunu ki sanyawa ranki hakuri... "amma Mama kina gani daga zuwana matanshi zasu kassarani shima zagina fa yake yi har cemin yai mahaukaciya yamin zafi! naji ciwo bazan iya ba!.." shafa kanta tayi kibar kuka kiyi hakuri da komai shi zaman duniya ɗan hakuri ne karna kuma ji kin ɗaga mishi murya.." Gyaɗa mata kai nayi cikin wani irin juriya nace "insha Allahu mama bazan sake ba" murmushi tayi tare da share min hawayen dake sauka kuka nasa sosai lna jin raina na zafi zan sake magana ta hanani lna kuka naji ya daka min tsawa ashe sosai nakeyi domin sautin muruyana na fita, "ke tunɗazu nake tashin ki kinyi banza dani kina kukan banza" miƙewa nayi jikina na rawa hawaye na zubamin ban taba tsintar kaina cikin quncin rayuwa irin na yau ba, hanyar banɗaki ya nunamin na shiga tsarki nayi da alwala lna fitowa naga ya shimfiɗamin sallaya ga himar ma , fita yayi nima na tada ikama sallanake inna kuka cikin sujadata lna kai karansu gurin Allah kaina nakasa har ya dawo ya zauna a gefen gado, ɗagowa nayi na sallame sallan ɗaga hannuna lna addu'a a bayyane "Allah kaji ƙan iyayena sanyi idaniyata abaɓen alfaharina allah yakai haske da rahama kabarinsu allah ya yafe musu zunubansu allah ya haɗasu da annabinka annabin rahama sallallahu alaihi wasallan, Allah na kawo karan wasu bayin ka, wanda sukayiwa rayuwata dirar bazata ba tare da na shiryawa haƙan ba, Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu Allah kamin katangar karfe dasu Allah duk wanda ya zalunceni kabimin haƙƙina Allah ka yafe kuskurena..."kukane yaci karfinta haka ta shafa addu'ar ta mike tare da ninke sallayar Tsungunawa nayi gabanshi "ina kwana?.." cikin masifa yace "daban kwana ba, zaki ganni? watou har karata kike kaiwa gurin Allah gani azzalumi ko?" ban kulashi ba na tashi haka ya ringa cin mutumcina ko cin kanka bance mishi ba, karshe ma fita nayi a ɗakin,
suna zaune a falo durkusawa nayi na gaida adam cikin sakin fuska ya amsa min "Ummuh lna kwana?" nace mata lna kara sunkuyar da kaina kasa "matso nan ƴata" domin a haife ta haifeta matsowa nayi na kwanta a jikinta kukan da naketa matsewa ne ya kwace min, kuka nake sosai shafa kaina tayi tare da faɗin "A duk lokacin daka tsinci kanka cikin Qunci rayuwa kace alhamdulillah base Allah ya jarrabeka da abin farin ciki zaka gode masa ba, ki zama me amsar kaddarar aduk yanda tazo miki.." gyaɗa mata kai nayi "inshaallahu nagode da tunatarwa" murmushi tayi sannan ta nuna min abinci kaɗan naci sabida raina a ɓace yake, miƙewa yayi bayan ya gama cin abinci "tafiyan kenan?" adam ya tambaye shi kallon agogon dake ɗaure Tsitsiyar hannunsa yayi tare da taɓe baki "lokaci na tafiya ki tashi" ya fad'i haka tare da tsare ni da ido rai a had'e danne kukan dake shirin kwacemin nayi tare da mikewa nayiwa ummuh sallama suna gaba lna biye dasu har gurin mota Ummuh ta rakomu tana mana fatan Alkhairi, hannun sukayiwa junansu kara rikeshi Adam yayi "Arab dan Allah ka sauko da zuciyarka kasa yarinyar nan a firgice take da kai.." "naji!" a takaice ya fad'a tare da bud'e motar ganin bana gaba yasashi tsayawa turus cikin bala'in yace "Ke fito ki dawo gaba!" lna zaune na jingina da jkin kurejar idona a rufe bamma san yana magana ba, domin nayi nisa a tunanin yaruwar data riskeni,

"Ke dan gidanku lna miki magana kin min shuru nine zan zama direvanki? "Kayi hakuri..." cikin kufula yace "fito ki dawo gaba" jiki a sanyaye na fito nan naga duk basa nan ajiyan zuciya na sauke domin na tsani cin mutumci a bainin naasi, haka na zauna na mayar da fuskana jikin glass lna kallon waje shigowa motar yayi tare da buga murfin yana jan tsaki nide ban kulashi ba, domin Allah kaɗai yasan abinda ke raina kiris nake jira na sauke nawa kwandon rashin mutumcin domin tunda ya shigo rayuwana hakurina yayi karanci,
***
Tafiya kurame shine tafiyar da mu kayi munyi tafiya sosai kafin ya tsaya a wani kauye fita yai yaje yin sallah ganin be cemin kala ba, nima na fita, ruwa na zuba a buta naje bayan gurin nayi tsarki sannan nayi alwala na rigashi dawowa cikin motar domin yaje siyan abinci koda ya dawo tekawey ya ajiye bemin magana ba nima kuma ban kulashi ba haka muka ci gaba da tafiya komai ya siya seya ajiye ni kuma banyi karanbanin tab'awa ba, ashe ranshi ya b'aci har barci ya fara fisgata ya taka wani wawan birki motar tayi gaba ta dawo baya kainane ya bugu na dafe hannunna a gurin lna cije baki domin naji zafi sosai ban zata ba , ya jawoni tare da had'a himar dina da wiyana ya shakeni sosai "Ni kika mayar asararre? in kashe kud'ina gurin siya miki abinci amma ki brshi ya lalace ga soko ko?" hawaye ne ya shiga zariya wani nabin wani da kyar nayi magana domin numfashi na ya fara barazanar barin ganagan jikina "Daka siya kace min Hauwa'u gashi? ko kace naci ne da zan d'auka ? an fad'a maka ni mayunwaciya ce , to ban bukata shi kenan! d'auki kayanka, Arab ka shafa min lafiya ka fita sab gata..." tureni yayi na bugu da glass din motar me shegen karfi abin bakin ciki kainane ya fashe amma glass din ko tsagewa beyi ba haka ya figi motar a guje ..

ajiyan zuciya kawai nake iyayi ga hawaye da yaki dena tsayawa kaina wani mugun ciwo yake min azzalumin nan ko ya juyo yaga halin da nake ciki ajiyan zuciya na sauke me karfi domin wani gargada muka shiga shi kuma yaki tafiya a sannu, seda na kara buga kaina daga nan bansan meya faru ba tsaban a zaba se farkawa nayi na ganni kaina jikin wata dattijuwa fara sol, ga kyau ga ,gayu jikinta mul-mul ajiyan zuciya ta sauke shi kuwa yana zaune fiskan ,kan da d'an dama cikin tsamin hausarta tace "jeka kira likitan" yana fita ta dawo da dubanta gareni rufe ido nayi itama bata takura min ba, ashe suma nayi koda muka iso zari'a ya tab'a ta yaji jikinta zafi rau gashi bata motsi shine y ciccib'e ta a falo yaga iyammu "cikin takaicin halin d'an nata tace koma kayi sallama domin ba d'akin kafura ka shigo ba, ai ko arnan suna konkon.."

"Dan allah iyanmu kiyi hakuri ki duba halin da ƴar nan take ciki.. "dakata! ince bakin halin naka ne ka gwada mata, dukanta kayi ka fasa mata kai bayan rashin tarbiyan da ƴan boko suka nuna mata (matan shi take nufi) kashe musu 'Ya kake son yi ba, kaje ni ba abinda zan muku na zare hannun na zaga iyalanka.... "dan girman Allah ki gafarce ni wallahi ba abinda kike zato bane iyanmu ba abinda na mata" share shi tayi taci gaba da karatun ta, ajiye jiddah yayi kaman ze mata kuka da kyar ya shawo kanta shima da sharaɗin ze tsaya a gidanshi ya zama namiji, ya amsa mata ne kawai amma bejin ze samu karfin gwiwar tsawatar musu domin suna haɗa mishi zafi su gwara kanshi yanda suke so ne, daga karshe seda suka danganta da asibiti tare da likita suka dawo ya cire min karin ruwan shayi ta had'a min kad'an nasha na shiga yun kurin amai iska ta ringa hura min tare da watsamin ruwan sanyi har aman ya koma "sannu fa Allah yana sane dake fatana ki zama haske a rayuwarshi Allah ya dubi lamuranki ya saukaka miki, ubangiji ya ɗaukakaki" wani kuka ne ya kwacemin bata hanani ba seda nayi me isata kafin nayi shuru lna sauke ajiyan zuciya sallama aka bamu muko koma gida kaman wani me aljanu mun isa gidan ko cikakken min ashirin bamuyi ba ya mike lokacin lna kwance a doguwan kujera iyanmu tana duba ishmawiy ya mike "Iyanmu zamu kaduna domin a gidan sawda zata zauna"

cikin gatse tace "tsawon shekara nawa?" gaba yayi tare da ɗaga kafaɗa "zuwa lokaci da allah ya takaita zamanta a gidan... "kaci gidanku" murmushi yayi tare da fita kallo na tayi tare da juyar da kai tausayin yarinyar take ji, i'ta kuma haka Allah ya kaddara mata shiga cikin iyalan lbrahimu Gidan da ake rayuwa cike da bakar kishi, "tashi ki bishi Allah ya tsare, zanso ki mayar da hankalinki kan karatu musammam ma, ta mahamadiya domin zata temaka miki qwarai wajen inganta rayuwar aurenki zanso ki fita zakka wajen ilimin islama a cikinsu domin Allah ya jefoki ne tsakiyar matan da suka jika da boko matan da basu bawa mijinsu mihimmanci kaman yanda suka maida hankulansu kan ayyukansu ba, zance ma gwara Nafisah" nide ban bawa zanceta muhimmamci ba domin na rasa inda ta dosa Allah ya temaka ma nayi wanka asibiti ..


*Maman Faruq*

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now