34

207 15 10
                                    

♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

®AYSHA  JB

FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION

*Wannan page ɗin naku ne, AYSHA JB CLUB tare da Wattpad Fan's Much Love Guys🥰😍 kuyi yanda kuke so dashi..*
34Shuru kawai Nuwairah tayi tana kallon yanda suke cacar baki, ba irin haƙurin da bata basu ba amma Ina koma zuciyarshi yai sama Cikin gajiyawa da haniyarsu ta ɗauki wayanta tana faɗin. “Tunda bakwa jin haƙuri bari na kira Gida wataƙil in suka zo zaku ƙyale wannan maganar” ta ƙarasa maganar tare da kai wayan kunninta karɓe wayan yayi tare da jan ƙwafa ya fita waje kallon Jiddah tayi tare da ɗaukan jakarta dake gefe sannan tace. “Oya Malama zaki tashi ne ko nayi tafiyata dan naga ke da mijin naki kun ɗau zafi sosai in Kuma daga nan akwai inda zaki tafi ne sai ki sanar min” Saukowa Jiddah tayi daga gadon tare da saka takalmin suka fito motan Nuwairah ta shiga suka nufo gida dai-dai ana kiran Sallar magariba ɗaki Jiddah ta nufa tayi alaula tare da sauke sallolin dake kanta, Nuwairah ce ta shigo mata da jakanta tare da magungunan da aka bata a asibiti Abincin dake kitchen ɗin ta ɗumama tare da kawo ma jiddah tana idar da Sallah ta koma bayi tayi wanka riga mara nauyi ta saka sannan ta tsakuri Abincin kana tasha magani lumshe ido tayi tana jin yanda kanta gefe ɗaya ke sarawa shigowa yayi tare da tsayuwa yana ƙare mata kallo, ko ɗagowa batayi balle tace mishi wani abu, “lokaci na ƙarshe kenan da zan sake tambayan  abinda ya kaiki asibiti da ɗan iskan daya biya miki kuɗi” buɗe jajayen idanunta tayi tare da watsawa cikin nashi kallon ƙwayar idonshi tayi sosai kafin ta ɗauke kanta, miƙewa tayi tana shirin fita yasa mata ƙafa ta faɗi, zata tashi ya sake danneta “Wacece ke da zan miki magana kisa kai ki wuce ba tare da kin bani amsata ba..?” cikin wani irin ƙarfin hali tasa duka hannunta biyu ta tureshi, wanda sai da ya buga ƙeyarshi da bango,  motsin da tayi da ƙarfi ne yasa hannun da akayi mata ƙarin ruwa ya fara fitar da jini, nuna shi tayi da yatsa cikin ɓacin rai tana faɗin “Karka yarda ka ƙara taɓa tsaftataccen jikina da ƙazamin hannunka..” miƙewa Yayi da sauri yana shirin kamota fita tayi da sauri dan ta lura muddin ta tsaya zai iya illatata domin wani  ƙazamin kishi take hangowa a idanunsa, a main falo ta dakata tana kallon yanda suka tsaya cirko cirko har Mahaifiyar Nuwairah “Meke faruwa anan? Kai Nabil meka zaburo kake shirin yi? tun ɗazun kun cika mana gida da hayaniya, ke Jiddah Ina kika je tun safe? Meya kai ki asibiti?” Mahaifinsa ne ya jero musu wannan tamabayoyin yana jiran Su bashi amsa Kallon Jiddah Nuwairah tayi sannan ta juyo tana kallon Nabil wanda ya ɗauke wuta yana jiran abinda Jiddah zatace tuni zuciyarshi ya fara lugude ga zufan rashin gaskiya dake karyo masa Buɗe baki Nuwairah tayi zatayi musu bayani ganin haka yasa Jiddah taran numfashinta gurin faɗin “Abba bafa wani abun ɗaga Hankali bane, zazzaɓi ne ya tare ni shine nayi saurin zuwa Asibiti..” Kallon Nabil Inna tayi tare da faɗin “Kai kuma Meye kake binta kaman zaka daketa?” da sauri Jiddah tace “Bafa wani abu bane, daman hannuna dana fama ne yake ta bina in tsaya ya gani shine nake gudu...” fita sukayi ya saura su uku kallon Jiddah Nuwairah take cike da mamaki ganin yanda ta rufa mishi asiri ba tare da ta faɗi ainihin abinda ya faru ba, “Allah ya ƙwace ka dan wallahi da nice aka tambaya bazan taɓa rufa maka asiri ba, kana da daman da zaka gyara kuskuren ka kafin lokaci ya ƙure maka” kallon Jiddah tayi tana cigaba da faɗin “Kinyi Abu ne kyau da kika rufawa mijinki asiri lallai ba ko wacce mace bace zatayi abunda kikayi Allah ya tashemu lafiya dan Allah ki ƙara Haƙuri akan na da”
   Ɗaki Jiddah ta koma tana shirin kwanciya ya zauna yana faɗin “Hmmm tunda abun haka ne ina ga zan ƙara Aure..” Ɗan  Murmushin takaici da ɓakin ciki tayi tana tunanin anya kuwa wannan Nabil ɗinta ne kuwa? Anya ba sauya mata shi akayi ba domin ta lura Gbɗy baya ma cikin Nutsuwa bare ayi tunanin Hankali tattare dashi “Allah ya bada sa'a” daga haka tayi shuru tana tunanin wacece i'ta da har mijinta ya manne mata yake kuma iƙirarin cewa zai Aure ta? Humm koma wacece bazata barta haka ba, tunda Har Nabil ya fara taɓa lafiyan jikinta da sunan Duka Wallahi sai ta Nimo ko wacece Yarinyar taci uban ta, kai har ma da uwar ta.
Ɗakin Nuwairah yaje kamar yadda ya sanar da Jiddah haka itama ya faɗa mata Aikuwa ko tutuf bata ce masa ba, haka ya gama zaman shi ƙarshe fita yayi a gidan, Girgiza kai kawai Jiddah tayi tare da sauke labulen window bayi ta nufa tayi Alwala tazo ta shimfiɗa sallaya nan ta fara jero nafiffilu tana masa Addu'ar shiriya bata runtsa ba saboda damuwa da baƙin cikin dake ƙunshe a zuciyarta kuka take sosai tana tunanin Nabil nacan gurin wata mace, macen ma Karuwa, Sai bayan Asubahi ya shigo gidan  lokacin ta gama ƴan aikace-aikacen data saba, Nuwairah ce ta fito tana kallon yanda ta kammala komai “Kai Jiddah wannan aiki haka, kinsan fa baki da lafiya ai da kin bari nayi komai” “Barka da Fitowa Aunty Nuwairah, ai ba komai wallahi” Hannunta Nuwairah ta kalla tana faɗin “To ya ƙarfin jikin naki? Ina fatan kin ji sauƙi?” Jiddah tace “Alhamdulillah da sauki sosai” Zama Nuwairah tayi tana faɗin “To Masha Allah jiya Yaya yake min maganar da ban gane kansa ba, na fara tunanin gwara a kaishi asibitin mahaukata a dubashi dan ga dukkan Alamu karen hauka ya cijeshi” Girgiza mata kai Jiddah tayi tana dariyan zancen ta. “Kai! Nuwaih yana cikin hankalin shi nafi ɗaukar maganar da wasa yake..” ajiye spoon ɗin tayi tana faɗin “Wasa fa kika ce? Allah da gaske yake kuma nasan zai kai maganar gaba” Kallonta nayi domin wlh na ɗauka barazana yake “Allah ya kyauta” nace sannan ya shiga ɗaki nayi shirin fita.
Jin motsin tura Get yasa ta gyara zama tana daɗe faɗaɗa fuskanta da yalwataccen murmushin a tunanin ta Nabil ne, Amma jin wani ƙamshi na daban yasa ta shiga kokonto waye haka? Jiddah kuwa tsayawa tayi tana ƙarema Gidan kallo sosai tana kallon ɓarnan da akayi da dukiya musamman ma kyawawan kujerun Alfarman dake falon ga danƙareren tv bango “Waye Anan?” Aaliyah dake fitowa ta faɗi haka tana mamakin ganin mace, Cikin nutsuwa Jiddah ta juyo tana tuna mai muryan ja da baya Aaliyah tayi tana nunata “Meya kawo ki gida na?” harɗe hannuwa Jiddah tayi a ƙirji tana matsowa tare da ƙare mata kallo “Aaliyah!! Ohh daman kece Karuwar tasa? Kece kikayi kane kane a rayuwar mijina? Kice kika ɗauke wa mijina hankali oh Na tuna a can baya kince zaki addabi rayuwata hakane Abun dama? To yau koni ko ke dan wallahi saina Kashe ki yanzun! kuma anan!! Saina lalata duk wani halitta na jikinki..” ja da baya Aaliyah ta shigayi tana faɗin “A'a Jiddah dakata nayi miki bayani wallahi Ina Son Nabil shima kuma yana ƙaunata yanzun haka muna shirin Aure ne dan mu mallaki junanmu...” ɗauke ta tayi da lafiyayyen marin da se da ta fitar da jini ta hancin ta, cakume wuyan riganta Jiddah tayi tana jijjigata cikin ɓacin rai “Mijin nawa kike shirin Aura ko? Zaki Aure shi amma a lahira dan baki da gurbin zama cikin matanshi na duniya” tana gama faɗin haka ta shiga kifa mata mari kukuwa kawai Aaliyah ta shigayi da Numfashi saboda riƙon da Jiddah tayi mata Numfashinta na barazanan ɗaukewa Dunƙule hannun Jiddah tayi da niyar kai mata naushi cikin tashin hankali Aaliyah ta tare cikinta da hannu tana faɗin “Dan Allah karki kashe rai, Ciki gareni na sati shida Please naci albarkacin sa...” ta ƙarasa maganar cikin kuka, cikin tashin hankali Jiddah tace “What! CIKI!!! Innalillahi wainna ilaihi rajiun” Jiddah ta faɗa tana ja da baya tare da fashewa da kuka “Ciki de na Haihuwa? Kina da ciki? No! Ƙariya ne!!” dawowa tayi da gudu takai mata wani mummunan naushi a ciki, ƙara me ƙarfi Aaliyah ta saka tare da zubewa a ƙasa ɗif Numfashinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu, ruwa me sanyi Jiddah ta zuba mata a Fuska tare da ɗagota “Karki yarda ki sake raɓan mijina ke ko Sunan mijina kikaji Ina so ki toshe kunnuwanki dan wallahi naji Mijina yana tare dake kashe ki zanyi!!” Kaman mahaukaciya haka Jiddah ta shiga dukanta ba ji ba gani, kafin ta shiga janta har ƙofan gida ta watsar da ita dawowa tayi cikin Gidan tare da Zuba fetur ta cinnawa gidan wuta tana fitowa ta tarar da Nabil yana shirin ɗaga Aaliyah dake ƙwance cikin jini Cikin wani irin mawuyacin halin Aaliyah ta Riƙe hannunshi tana faɗin “Yau nake shirin sanar da kai amma matarka ta ɓata komai Nabil Baby Na ciki gareni shine tazo ta kashe ni da Abinda ke ciki na” A zabure ya sa ke ta tare da nufo Jiddah nan ya shiga zuba mata mari cikin ɓacin rai “Akan me? Me yasa kika zubar min da ciki...”
“Nabilllll” da gudu ya nufi gurin Aaliyah tare da ɗaukanta yasata a Mota suka nufi asibiti.
Gida ta nufo gbɗy bata cikin nutsuwarta “Jiddah Ina kika je?” Ina Jiddah bata ma san da ita ake magana ba, riƙe ta Nuwairah tayi tana faɗin “Jiddah menene haka? Ya naga fuskan ki a kunbure waya dake ki?” wani irin kuka ta fashe dashi tare da faɗin “Nuwairah Yarinyar da Nabil ya ajiye har ciki gareka wannan Karuwar tasa nake faɗa miki ciki gareta saboda naje na dake ta shine Nabil ya mayar min da fuska haka Akan karuwa Ya min haka!” Cikin tashin hankali Inna ta ƙaraso gurin har zaninta na shirin faɗuwa kasa “Me nake ji haka? Ke! Jiddah me kike faɗa ne?”
Girgiza kai Jiddah ta shigayi tana faɗin “Babu komai..” Rufe mata baki Nuwairah tayi itama cikin kuka tana faɗin “Ƙwarai Abinda kunnuwanki suka jiye miki haka ne, Nabil ne ya ajiye Karuwa a waje duk wannan rigingimun da muke duk akan maganar ne..." Rufe mata baki Jiddah tayi tana girgiza mata kai alamar karta faɗa “ƙyale ni Jiddah Halin Nabil ya isheni gwara na fayyace komai” tiriyan-tiriyan ta dinga faɗa musu komai Wani  wawan burki Nabil yaja yana kallon Nuwairah dake bayani Juyowa mahaifiyarshi tayi nan ta shiga zuba mishi mari tana faɗin “Wannan ba tarbiyan dana baka bane, wannan ba Renon Asma'u bace, Nabil kaine da ajiye mace a waje har da ciki?” sunkuyar da kanshi yayi ƙasa yana sake jin wani ɓacin rai, duk abinda suke Mahaifinshi na kallonsu jinjina kai yayi yana mamakin Halayyar da Nabil ya ɗauko “Da Girman ka,  da ilimin ka, kana da iyali  kasan Hukuncin zina kuwa? Anya Nabil baka fara shaye-shaye ba kuwa? To wallahi ka buɗe kunninka kaji da kyau bazan ɗauki wannan ƙazantar a cikin gidana ba, ban taɓa Zina ba, dan haka...” da sauri Jiddah tace “Dan Allah Abba karka masa baki, dan girman Allah kuyi masa addu'a shine kawai abunda yake buƙata”  gyaɗa kai Mahaifinshi yayi tare da nuna shi da yatsa ransa a ɓace ya bar gurin haka ma mahaifiyarsa Nuwairah kuwa hannun Jiddah ta kama suka dawo part ɗinsu.
yanke shawaran barin Gidan Jiddah tayi, nan da Nan ta  shiga haɗa kayanta tare da buɗe wani ƙaramin jaka ta ɗauko hoton Mahaifiyarta, rumgume hoton tayi tana hawaye sosai cikin kuka take faɗin “Umma  lna cikin Ahalinki yau nice matsayin matar ɗan da kikafi ƙauna yau gashi zan barshi bazan iya cigaba da zama dashi a irin wannan rayuwar ba, bazan iya zama baƙin ciki da damuwa su kashe ni ba, gwara na koma inda na fito gwara na tafi kuma tafiyar da bana jin zan sake dawowa”
      Zoben Azurfa da awarwaronsa ta ɗora kan hoton tare da ɗan shot note ta ajiye, ATM ta ɗauka tare da Nufar part ɗin Mama-Sadin ganin tana barci ne yasa ta juyawa da niyar fita ɗan gyaran murya taji mama tayi a hankali ta juyo tana kallon yanda Mama ke motsawa da sauri ta fita a gidan kuɗi masu yawa ta cire kafin ta bar ƙasar direct Gidan Fadilah ta nufa dan bata  so kowa yasan tazo Nigeria daga dangin Ummi bata samu Fadilah a gida ba, me musu gadi ne yake sanar da ita tafiyan da tayi tare da mijinta key ɗin cikin gidan ta karɓa daga gurinshi kasancewar ya santa da Fadilah shiyasa bai wani damu ba, Ɗakin Fadilah ta shiga nan ta adana kayanta tare da shiga bayi tayi wanka a gurguje tazo ta biya sallolin dake kanta kasancewan dare yayi sosai bazata iya yin girki bane yasa ta haɗa tea kawai tasha ta kwanta.

Chadi....

Bana ganin Comment

Maman Faruq

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now