6

780 29 5
                                    

*♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
_Wattpad@ayshajb_

®️🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

_♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/

FREE BOOK

*sadaukarwa gareki*
Rahama Real Ladingo

Jama'a ga sauki na buga kofar gidanki batareda kin sha xafin rana ba,ko kinsan SHANONO AND SODA CLOTHES AND MORE Suna bajakolin kayan Atamfofi kayan kicin tsantsara tsantsara na kece raini? To banan suka tsaya ba akwai abubuwan da suke order bayan wannan cikin aminci da kwanciyar hankali a rabu ana madalla.
Kishiga wannan group domin kashe kwarkwatar idonki.
Sannan Ga nambar daxaki iya kira ko chat da ita domin neman karin bayani
👉👉👉 08137145294
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FQ9k6e5aOljEP3s3UGqEcu
page6
Jingine da motarshi yake yana ganin fitowarta ya shigan tare da rufe murfin a hankali nake tafiya har na karasa inna shiga yaja motar juyar da kaina nayi gefe har munyi nisa da tafiya kafin ya waigo. "i'tace mahaifiyata iyanmu mu Shida ta haifa, Sawda ce babba tana aure a kaduna malamace yarinyarta ɗaya tal, sai Musa shi kuma yana sudan da iyalanshi sai Abbas shima yana sudan Aminu yana Bauchi nine na biyar se karaman mu Zaliya wanda take ABU Mahaifin mu ya rasu shekara shida kenan" bance mishi komai ba har muka isa Kaduna Gidanta baban gidane a gefe kuda akwai makaranta wanda ake koyar da matan aure har da na ƴan mata da yara megadi ne ya buɗe mata get yana de-deta tsayuwar motar muka fito yana gaba inna biye dashi a baya Da sallama muka shiga falon ba kowa zama yayi tare da nuna min kujera memakon nayi yanda yace sena zauna a kasa.
Shuru mukayi na yan mintuna kafin ya katse shurun ta hanyar fad'in, "na kawoki nan ne domin ki zauna na d'an lokaci ki mayar da hankalinki kan karatun da zakiyi domin matana ba lahilai bane , ko wacce da kika ganta da iliminta da sana'arta matsalar ki ne ki nutsu kinyi karatu domin inganta rayuwarki domin mahaifinki Yana da burin kiyi karatu banda shirme... "Hmmm kasan aiki nane shirme ai Daman nace matanka jahilai ne , daga zuwa na sun nuna min kalar tasu ilimin, da kace na mayar da hankali ko karna mayar ince hankalin nawa ne? Kuma a jikina yake, nagode insha allahu zanyi karatu zan nutsu kodan nacika burin Raina" Gyad'a Kai yayi kafin yace. "yana da kyau.." "Daman ba kyau ne?" Na fad'i Haka inna lankwasa hannuwana..

"Ki kiyaye harshen ki, kisan abinda zaki ringa furta min karki bata min rai"

Sunkuyar da Kai nayi kasa.

"Kayi hakuri insha allahu zan kiyaye"

"Assalamu alaikum" tace kafin ta karaso cikin shigar kamala a nutse ta zauna kusa dashi.

"Amin wa'alaikis Salam barka sawda malama Sawda ummin halimatu"

Murmushi tayi kafin ta juyo gare ni "inna yini" nace mata murmushi tayi kafin tace "lafiya lau hauwa ya gajiya da hakuri da k'anina?" Ta karasa maganar tana kallonshi bance Mata komai ba had'e fiska yayi "haba! Dan Allah ai seki sa ta renani" a hankali yayi maganar,

Girgiza Kai tayi kafin tayi waya kichin "Yahgana ki kawo abinci" kashe wayar tayi , tare da mikewa "Zo muje kiyi wanka da sallah kafin ta kammala"

Ɗakin Halima ta kaini tare da nuna min Banɗaki wanka da alwala nayi inna fitowa ta shigo da bakar leda "Yanzun arab ya aiko kiyi amfani dashi. Bance Mata komai ba ta fita Dogayen rigunane guda Shida se Himar da kananun tarkace a Raina nayi tsaki kafin na saka D'aya daga cikin kayan sallahn dake kaina duka nayi kafin na kwanta saman salayan Nan da Nan barci ya dauke ni cike da gajiya..

Yana ganin shigarsu shima ya mike masallacin dake wajen Gidan ya nufa anan yayi sallah ya dawo abincin da aka jera ya zuba ya fara ci, Ummin halima ce ta shigo "Hauwan bata fito ba?" Ba tare da ya D'ago ba ya Gyad'a mata Kai.

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now