32

234 14 16
                                    

♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

®AYSHA JB

FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION

32Shirin kwanciya tayi tare da hayewa Gadon ta zauna kusa da Fadila “Yau ba ke bace da duty? Naga nan kike Shirin kwana mijin naki fa?” “Kinga Besty raba ni da maganar Nabil lamarinsa ya ishe ni wannan ba Sir Nabil ɗin da kika sani bane, an sauya min Nabil” cike da karyewan Murya ta ƙarasa maganan “What are you saying? Dan Allah Jiddah kimin bayani kin fa san wannan ba zuwan kaina bane Ummi ce tace nazo na duba yanayin zamanku da kuma yanda kike” Cikin sauri jiddah tace inaga tare zamu koma Nigeria domin na gaji da Auren shi kenan ni bazan ji dad'i ba? Tunda na taso rayuwata cikin garari take Wannan Auren ma da nake tunanin zan samu farin ciki ashe ba haka bane, Gwara Nigeria ina ganin Ƴan uwana har nayi share Damuwata dasu nan fa? Bani da kowa daga ni sai ni, bani da wanda zai rarrasheni bare magana me daɗi Yanayin zaman babu daɗi mijina bashi da lokaci na  akwai komai na rayuwa Amma bansan wani soyayya da tattali irin na mata da miji ba.. Fadilah bansan ya zan miki bayanin komai ba”
   “i't okay I understand Everything now,  Amma karki manta akwai Allah kuma Jiddah ke me addini ce da yawan ibada kada ki manta da cewan dukkan tsanani yana tare da sauƙi ki yaiwata ibada sadaka, istigfari hailala salatin Annabi inhar kina wa’innan abubuwan komai zai-zo da sauƙi amma ga dukkan alamu bakya yinsu gaskiya bazan ɓoye miki ba , wannan yanayin dana sameki ciki bai min daɗi ba sam Ga de kishiyarki nan Hankalinta kwance bata da wata matsala..” Jiddah tace “ita fa Nuwairah inde zaki bita a yanda take daman haka ne, macece me Son a girmamata Bata da wata aiki face tayi wanka ta zari makulli kullum tana yawo gidan yayyunta Sune yawo da ƙawaye yau aje Biki nan gobe can, shiyasa bazaki sameta da wata damuwa ba, domin ko ya Hanata fita tofa seta fitan, damuwarta ɗaya wanda nima shine tawa damuwar i'tace de maganar Haihuwa..” Ajiyan zuciya Fadilah ta sauke sannan tace “Mu aje wannan batun a gefe ya zamantakewar ku da mijinki? Dan ke naga ba kwalliya kike wanda zai ɗau hankalinsa ba, bakya wani abu wanda zai ja hankalinsa gareki” “Kwalliya? Hamm Ina ƙoƙarin hakan amma wani abunda baki sani ba shine har nayi kwalliyan na zauna  jiransa Har barci ya ɗaukeni Nabil baya dawowa gida in ya dawo yaga nayi barci sede yayi ɗakin shi shiyasa duk na watsar da komai na zuba mishi i'do kawai”
“Kika zuba mishi ido? Anya Lafiya kalau kike kuwa? kina nufin idan bai nime ki ba, ke bakya nimansa wacce irin magana kike haka Jiddah? anya bazan miki rijistan matan ƙwarai kije ki dinga kallon abubuwan da zai dawo miki da sha'awarki ba? To ki nutsu kiji da kyau, in zaki canza tsari gwara tun wuri ki canza ga kaya Ummi ta bani ina kawo miki nima kuma na tawo miki da tawa gudumawar” jakar kayan data tawo Mata dashi ta buɗe nan ta dinga fitowa da wasu sheɗanun kaya kallon ta Jiddah tayi tare da faɗin “ Tabɗijam! Lallai sannu da ƙoƙari kin kyauta zanyi Ƙoƙarin gurin Amfani dasu” Ɗaukar wayan Jiddah Fadilah tayi tana danne danne tana Gamawa ta tura mata wayar “Ke meye wannan? Tabɗi Ina ni Ina kallon wannan Abubuwan?” Dariya Fadilah tayi tana faɗin “Kinga banson shirme kayan arziki na tura miki ki kalla da kyau dan ki ɗauki styles kala daban-daban Shi namiji yafi so kullum a dinga canza mishi salo dan Allah ki koyi irin Kalaman nan masu ɗaga hankali wanda koda yana jikinki ne ki riƙe shi sosai kina Faɗa mishi irin Romatics and  Sexy words ɗin nan wallahi zaki seta shi, shi da kanshi zai dinga zumuɗin ya dawo gareki domin yasan za'a tarbeshi da zafafan abubuwa ke yanzun fa kai ya waye seda ƴan kalle-kalle da karance karance saboda ka sake samun ilimin mallakar zuciyar Miji..” Shuru nayi ina kallonta domin ni duk irin Abubuwan nan basu dameni ba, ko Novels ban karantawa Halimatu ce me ƙoƙarin karatu Ajiyan zuciya na sauke  kafin nace Mata “Besty ina kika samo irin waƴannan Videos ɗin ni wallahi har kunya ta kamani bana jin zan iya kallonsu..” kwanciya Fadilah tayi tare da faɗin “Kina nan zaune kin mayar da kanki wata iri mu muna can Cikin Matan Ƙwarai, wani group ɗin JB ne na matan Aure, da sabbin Aure ana shagali sosai zaki haɗu da mata masu mutumci da zumunci bawai i'ya Nan aka tsaya ba, in kina da wata damuwa ma zaki iya fitowa ki nimi shawara, in magunguna kike so duk za'a miki bayanin yanda zaki haɗa Abinki a sauƙaƙe Kinga Besty bacci nake ji gobe zamuci gaba”
“Ai tashi zakiyi baki faɗa min Ya yaro na yake ba, yana cikin ƙoshin lafiya? Ya girmansa yake?” tashi zaune Fadilah tayi tana faɗin “Aakif yana nan ƙalau kema kin san dole ya girma dan ana tafiya shekara bakwai kenan yaron ki kamarki Hasken ne Na uban, Hatta da natsuwar da ilimin duk ke ya ɗauko gashi da Mugun haƙuri sede miskiline dan bai cika magana ba, in kinji muryanshi na tashi to shida Jumana ne ko Appan shi, yana da ƙoƙari sosai a karatu sede shima yana da ƙawazuci, dan Ako da yaushe yana tare da hotonki wanda Ummi ta bashi, Zaman gidan de kamar yanda kika sani babu abinda ya sauya An aurar da Sabilah da Sa'irah sede ko wata ba'a rufe ba kowacce mijinta ya korota saboda rashin iya magana girki ma babu wanda ya i'ya cikin su, komai basu iya ba, suna Son zaman Aure amma basu da ilimin zamantakewa don uwarsu Bata basu wannan tarbiyan ba, yanzun de suna Zaria gidan Iyanmu dan can Arab ya kaisu anan suke koyon Abubuwa tare da temakon Ummi...”
  “Kinata Maganganun da ban tambaye ki ba, Naji yaran Zainab sunyi Aure amma banji kince Yayarsu Jumana tayi Aure ba..” Fadilah tace “Lamarin Jumana sai Addu'a fa, domin Ina ga Zainab bata Ƙyale Ƴar Nafisa haka ba, Kama-kama Za'a fito ayi maganar Aure bayan kwana biyu sede kiji shuru anyi haka so uku, yanzun de Anata addu'a ne domin A yanda nake jin labari gurin Halimatu hadda turen Aljanu cikin lamarin” jinjina lamarin nayi ina tunanin Halayya irin na Zainaba “ikon Allah i'ta de Zainab bazata tuba ba? Allah ya kyauta ai banda wannan labarin domin yanzun bani da Number Nafisa Amma insha Allahu nima zan tayasu da Addu'a, Allah ya shiga cikin lamarin, i'ta kuma Zainab in tana da rabon shiriya Ubangiji ya shiryar da i'ta..”
Fadilah tace “Lallai Besty kina da zuciyar musulunci duk abinda Zainab ta miki baki riƙe ta ba, kina nan kina mata Addu'ar shiriya? Tabɗi Sannu” Murmushi kawai nayi tare da faɗin “To meye duniyan Besty? Wallahi duk wasu abubuwan da Zainab tamin ban riƙe ta ba, Ga ishara ta fara gani tunda zaman gidan miji ya gagari ƴaƴanta” haka muka raba dare muna hira kafin muka kwanta, kwana uku Fadilah tayi kafin ta koma naji daɗin zuwanta domin ta bani shawarwari sosai da kuma yanda zan gyara tsakani na da Mijina. Ina gama ayyuka na nayi wanka bayan na shirya na nufi ɗakinsa acan na zauna zaman jiransa dan yanzun da zaran ya dawo baya kallon kofar kowa se nashi ina kwance ya ture kofar tare da sallama Miƙewa nayi ina taku cikin nutsuwa Da jan hankali har na ƙarasa gareshi karɓan jakarshi nayi tare da kamo hannunshi muka ƙarasa bakin Bed shide kallona kawai yake ya rasa bakin magana zaunar dashi nayi kafin na cire mishi safan dake ƙafarshi temaka mishi nayi ya cire kayanshi A hankali na mike na kawo mishi ruwa me sanyi ban bashi ba seda na zauna dab dashi kafin nakai kofin bakinsa lumshe ido yayi tare da buɗewa yana  cigaba da kallonta ajiye kofin nayi sannan na sakar masa kyakkyawan murmushi ina faɗin “Barka da zuwa Habibi” kwantar da kaina nayi bisa kafaɗarshi ina sauke numfashi Sake lumshe ido yayi tare da faɗin “Kinyi Matuƙar kyau Jiddah..” sake narkewa nayi sosai tare da faɗin “Allah ko Habibi Nah?” shafo fuskana yayi yana Murmushi daga haka yaja Hannuna har toilet seda na hada mishi ruwan wanka sannan na fito kayan shan iska na fito mishi dashi tare da kashe wayarshi dan na lura wayar na shiga lokacina Nayi matuƙar ƙoƙarin gurin ɗauke masa Hankali duk yanda yaso ya ɗauki wayar hanashi nayi sosai na koma masa kaman ƙaraman yarinya ina bin jikinshi tare da Zuba mishi shirmen labarai wanda sukayi nasaran ɗauke masa Hankali yau kan tunda ya dawo ban barshi ya fita ba, muna tare ƙarshe ma a gida yayi sallar isha'i Ina sane da niman wayarshi da yake lokacin da mukazo kwanciya dariya kawai nayi tare da Rumgumeshi daga nan salo ya canza. Bansan nayi mugun kewar mijina ba se yau, tsawon lokaci na riƙe shi ina mishi ƙananun kuka da sambatun abinda shi kuma yasashi daɗewa kenan yana juyani jin yanda nake mishi sambatu Ina Murza Nippls ɗinsa, Ina Son Nabil sSo me zafi saboda yasan yanda zai tafiyar dani har inji na gamsu, sabon halayyar daya zo dashi ne kawai matsalata Bayan haka Ta ko'ina Nabil Namiji ne, bazan iya muku bayanin daɗin dana ji ba, nasan de yanayin na Musamman ne cikin jikin juna mukayi barci, da asuba shi ya tashe ni dan har naso makara Sallah Lokacin daya shirya har gurin Motar shi na rakoshi Ina mishi addu'a  “Allah ya tsare min kai Ubangiji ya baka halal ɗinka Allah ya rabaka da duk wani abinda ba Alkhairi bane, Ubangiji ya baka Alkhairinsa Allah ya kauda idanun sauran mata daga kallon kyakkyawan fuskar Mijina” jawota yayi yana Murmushin jin daɗi “Ameen Matata” cike da wani irin jin daɗi yake tuƙin mota har ya isa inda baƙonsa yake jiransa a wani ƙyataccen gurin shakawa ya tsaya zama yayi yana dube dube, Ta gefenshi yaji anyi tafi ɗan waigowa yayi take idanunshi ya faɗa cikin nashi “Kana mamakin gani na ko?” ɗauke kansa yayi tare da duba agogon dake hannunsa “Ina jinka dan lna da abubuwan yi” zama Arab yayi tare da faɗin “Da fari ka fara duba wayarka kafin muyi wata magana” ɗaukar wayanshi yayi take yaga Alert na Miliyan gomsha sha biyar “what! Wanan kuɗin na menene?” cike da mamaki Nabil yake kallonsa “Karo na biyu kenan ina biyo ka  ƙasarka, ina so wannan zuwan ta zama ta ƙarshe, Wannan kuɗin na baka ne dan ka sake min matata domin Jiddah...” dakatar dashi Nabil yayi cikin hanzari “idan baka manta ba, ka taɓa tuntuɓata akan hakan nace maka Bazan i'ya rabuwa da i'ta ba...”
“Amma kasan bazaka saketa ba meyasa ka Aure ta? kasan ni na temaka har iyayenka suka yarda ka Auri Ƴar Nigeria akan me bazaka sake ta ba? Nace maka shekara ɗaya kawai zaka zauna da i'ta wa'adin na cika ka dawo min da ita amma kayi shuru na nimeka ka share batun akan me!? Kasan de bata dace da mazinaci i'rinka me farka a waje ba ko? Kasan yanda Jiddah ta tsani zina me kake tunanin zata aikata muddin tasan wanda take Aure mazinaci ne...”
“Ya isa! Ya isa!!!!..” cikin tsannain ɓacin rai Nabil ya dakatar dashi.
Wani mugun kallo Arab ya watsa mishi yana cigaba da faɗin “Ƙaddara da rashin bincike yasa na rabu da mace mafi daraja a rayuwata, macen da har yanzun ban samu me irin hallinta ba, A Duk lokacin da namiji ya samu Mace ta gari, me tsarkakkiyar zuciya da ilimi addini tare da aiki da ilmi to yasamu rabin farin cikin rayuwa, saboda zata zamo masa tamkar mahaifiyarsa, za ta so farin cikin sa ako da yaushe, za ta kyautata masa da ƴan uwan sa, za ta dunga mishi addu'a  za ta so sa dan ALLAH za ta kula da damuwar sa, yunwan cikin sa, kwanciyar hankalin sa , da yi masa nasiha da nuna masa ya guji Haram ya nemi halal duk wahalar sa, saboda tana son su tsira Duniya da lahira,
Ko da yayi yunƙurin kaucewa za ta yi masa Addu'a tare da nasiha cikin kwanciyar hankali da bisa Sunnah,
Ko da wani jarabta ya same su zata yi ƙoƙarin yi musu addu'a ba wai ta dunga jin haushin sa, tana sake fusata shi har yaje ya faɗa neman Haram ba, A'a Sede ta masa addua, nasiha, tare da rarrashi da tausasa harshe Hauwa'u Jiddah kenan kai kasan darajarta kuwa? Haƙurin ta, Kamun kanta da Son temakon Jama'a yasa a kullum  Allah yake ɗaukaka darajarta Macece wacce kowani namiji zeyi fatan samunta matsayin uwar ƴaƴansa..”
   “Dakata Malam! Da ka manta da daraja da haƙurinta ne ? Meyasa ka kasa riƙe ta? Naji da temakon ka na Aureta amma karka manta da gumina na Aureta babu sisinka domi kuɗin daka bani suna nan ban taɓa sisinka ba, Saki kuma bazan i'ya kasadan barinta ba, domin se yanzun ma na sake jin sonta da Ƙaunarta ya shigeni dan itace farin ciki na, macece me mugum haƙuri duk da bana kyauta mata amma bata min ƙorafi kullum ƙoƙarin kyautatamin da faranta raina take, Ina so ka sani yanzun na fara Zaman Aure da Jiddah Ƙasata ka shigo zan iya wulaƙanta ka, taa hanyar maka sharrin da zaisa ka ƙarasa rayuwarka a gidan yari, Ina mai sanar da kayi gaggawan barin Ƙasar Nan muddin ka bari Jiddah ta samu labarin ka shigo Chadi ranka ze ɓaci” wani shegen Murmushi Arab yayi tare da  faɗin “Ina ga ka manta da wanda kake magana ko? Duk danginka babu me arzikin da zai ɗaureni zanyi Amfani da ƙarfin dukiya nasa ka sake ta! Kuma wallahi seka sakar min Ita” miƙewa Nabil yayi tare da ɗaga kafaɗarshi yana Murmushin “okay zamuga uban da zesa in saki Matata” da mugum kallo Arab ya raka Bayanshi kafin shima ya shiga mota yabar gurin yana faɗin “Yaro be san wuta ba seya taka, kana wasa da rayuwarka zamu ga nida kai wa zai janye ƙudirinsa”

Maman Faruq

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now