♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*
*FJWA*
PAGE17
Awaje ta had'u dashi da Nafisa "Toh Jiddah Allah ya tsare ya bada abinda akaje Nima" murmushi nayi sannan na amsa na shiga Motar Derive yaja muka soma tafiya kwanciya nayi shuru inna tunanin Mijin Aure na, datar Wayarta ta kunna Akwai group d'in da wata 'Yar ajinsu ta sakata *mu Gyara da kanmu* su Ashirin ne kacal, bata tab'a shiga taga hirar da akeyi ba sai yau Nan taci Karo da i'rin Tata matsalar inda wata maman mubina tayi Post tana fad'in 'Yan uwa inna cikin matsala da damuwa Aurena shekara Takwas Wallahi ban tab'a jin dad'in da akecewa ana ji, yayin saduwa ba, Mijina Be iya Tafiyar da lalura na ba, Wallahi bansan dad'in D'a namiji ba, shide kullun da yazo na bud'e mishi yaci ya sauka ko d'an shafe shafen Nan da nakeji wasu na fad'a ana musu baya min ni Kuma da nafara kokarin masa se yace wannan ai isk'anci ne wani i'rin Bagidajen mutum ne shi, baya tab'a fisk'antar inna da damuwa Ko akasin sa.
Abinci Akwai shi sutura ma duk ban rasa ba, se nutsuwa a mu'amularmu na Auratayya Wallahi ban tab'a jin dad'in Aure ba,ku bani shawara dan Allah.Hanisa Naga tayi tagging maganarta inda take cewa "Kin tab'a fad'a masa bakya gamsuwa?"
Maman mubina tace So nawa Kuma? Wallahi Karshe yau har fad'a seda mukayi Gaskiya na gaji da Auren Wallahi. Toh ko Yana da infection ne ko basir kinsan shima Yana rage Karfin maza. Maman mubina tace maganar shekaru fa nake Malama Hanisa Ba kwanaki ko watanni ba,
Watakil halittarsa ce haka..
Rufe data na nayi tare da sauka, "Yah ilahyi ka Mana maganin matsalarmu" haka har muka karaso Zaria kasancewar Ummi ta sanar mata ne yasa ta had'a mata abinci,
A tak'aice seda nayi shekara Na a Gidan Iyanmu zuwa lokacin na kammala service na, tsawon wannan lokacin Arab be tako inda take ba, sede ya Mata Aiken kud'i cikin wannan lokacin Akayi bikin Hanisa wadda nasha Gori rashin zuwana Amma na Mata aike, kwance tashi a saran me rai, Yau shekrata Uku gidanta tab'a tab'a, tambayata Meya hanashi zuwa ba, zamu Zauna muyi Hira da komai musammam akan aikina Zuwa yanzun na Gina Gurin abici sannan innada shago kofar Gidanta , hankalina kwance , Duk shekara in zamuyi azumi Yana turo min da kud'in, Kwatsan yau muna Zaune inna yanke mata farce kaman wadda aka jefoshi ya fad'o d'akin tare da Sallama bata amsa mishi ba, nice Kawai na amsa tare da Barin gurin."Iyata Fushi kike dani" yace Yana Zama kusa da i'ta, "ba kod'aya Arab me kamin da zanyi Fushi da Kai?" Tace tana kokarin mikewa "Dan Allah kiyi hakuri nasan ban kyauta ba.." "Dalla rufemin Baki Mutumin Banza Kai har kanada bakin bani Hakuri Wallahi Arab ka bani mamaki , Bari kaji in fad'amaka tun guri gwara ka sake musu 'Ya! Tana zata zauna tana kare Aurenka Bayan ka banzatar da i'ta..?" Kashe Murya yayi "To ai nace kiyi hakuri ko? Ni ba Zan saketa ba Yarinyar tana da Hankali dan Allah Yunwa nake ji" Abincin da na girka Mana na Rana ta nuna masa Zama yayi ya fara ci Loman farko ya lumshe i'do "Kai iyata inna kuka sai abinci me dad'i haka? Wallahi girkin yayi kyau!"
Murmushi tayi. "Hauwa'u ce ta Girka.." ai da sauri yace Kai alhamdulillah" Nan ya zatse seda ya cika Tunbinsa kafin ya boyata inna Zaune Gaban Computer na inna tura sako, ya shigo ban d'ago ba, Amma na amsa mishi Sallamar.
"Kiyi hakuri da abinda ya faru" kashe kayan aikin nayi tare da yin murmushi "Ai ya Wuce"
Murmushi yayi Yana sake Kare mata kallo ta cika sosai tayi kyau harda k'iba mikewa tayi mishi ya nufota Daman tasan za'a rina Himar d'ina na zame domin ban yarda zama haka sena Rufe jikina "Hasbunanlahu kinyi kyau Amariyata" Riga da wando jikinta wadda yai bala'in matseta daga sama Dukiyar fulaninta na waje lashe leb'e yayi sannan ya cire Kayan jikinshi ,
Nan ya kamota bata ki tayin shi ba, domin i'tama tana bukatar hak'an "Kiyi hakuri kinji" lumshe i'do tayi tana jin yadda yake matse nonuwanta "Bakomai!" "Dan Allah kimin wasanni nayi kewarki sosai.." mikewa Nayi na nufi Band'aki ruwan wanka na had'a mishi "Kayi wanka tukun" datana Na kunna Naga Hanisa online "Yar Banza uncle d'inki fa Yau ya waiwayo ni kinsan d'an renin hankali so yake yaji dad'i Dani..." Ta tura mata alamar mamaki Hanisa ta turo mata..
YOU ARE READING
SIRRIN ƊAUKAKA
RomanceLabarine me ciƙe da ma'anoni a cikinsa akwai faɗakarwa ilmantarwa nishaɗantarwa basena ja da tsayi ba kusan rubutuna sede wannan salon daban yake da sauran ina fatan zakuci gaba da bina..