3

1.2K 38 1
                                    

*SIRRIN ƊAUKAKA*
_Wattpad@ayshajb_

Free Book

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*

*Sadaukarwa gareki*
*Rahama (Ladingo ummuh fareesa)*

Page3 .
..........Salati kawai Larai takeyi kafin tayi kaina "Hauwa! Hauwa!!" Amma shuru da sauri tayi waje Liman da shigowarsa Kenan ya dawo daga masallaci yace "Lafiya naganki haka?" Larai tace "malam l'nafa Lafiya! Asma'u ta rasu.... " Be gama jin maganarta ba ya nufi d'akin Nan ya tadda Jiddah kwance Larai na shigowa yace ta kawo masa ruwa da sauri ta d'ibo ruwan ta kawo masa shafamin yayi a fiska ajiyan zuciya na sauke ban bud'e idanuwa ba , kuka na fashe dashi shi Kenan banida uwa bani da Uba , babu dangi Na rage ni kad'ai dagani se Allah se Kuma halina wayyo haka tawa K'addarar take yanzun babu Wanda zan kalla inji Dad'i ..
"Kiyi Hakuri Hauwa.." Da sauri na katse shi "To ya zanyi inba hakurin ba! Banida kowa fa! Babu ni ce fa ni D'aya! Khay.." Wani irin kuka na sake fashewa dashi Bani da Gata fa yanzun , Larai da wasu mata makotanta ne sukayiwa Mama wanka malam yaje ya siyo likkafani ina kwance inna kuka har aka gama had'a mama Akayi mata sallah koda akace inje in mata addu'a kasawa nayi rik'e mankaran nayi inna kuka harda majina na kasa furta komai ganin na jima ne yasa Larai zuwa inda nake wai zata d'agani Amma tayi tayi naki tashi karshe de maza ne suka d'agani a gaban mankaran inna ihu da shurewa haka suka d'agani fad'i kawai nake "ku barmin mamana ku wasu i'rin azzalumai ne me yasa bazaku tausayamin ba , mamanace fa zaku tafi min da i'ta so kuke rayuwata ta tagayyara? banida uwa bani da uba ya zanyi kuji tausayi na mana haba! Bayin Allah..Wayyo Allah jama'a kuna gani zasu tafi min da UWA" mutanen dake gurin seda suka kokamin na zama wata iri bani da aiki se kuka abinci bana ci magana ma banayi Sallah kad'ai shike d'agani satin mama D'aya Liman ya shiga niman mu'azzan Balarabe Numbobin wayarsa baya shiga kullun aka Kira a kashe zuwa lokaci na fara saka juriya wa zuciyata sabida kullun Liman da matarsa hard'a 'ya'yansa haka zasu tasani gaba suna tausar zuciyata da kalamai masu kwantar da hankali hakade nake daurewa ina cin abinci badon inna jin dad'insa ba, bana son gwalesu ne kawai suna kokari dani banida abinda zance musu sede Allah ya saka musu da alkhairi Wata D'aya da kwana biyar aka samu wayar Balarabe bansan abinda Liman suka tattaunaba nede yace min sunyi waya da mu'azzan hakan ya faru da kwana biyar se gashi sunzo su biyu .
Dangin mahaifina babu Wanda yazo Kuma an aika musu haka lokacin da Liman ya aika a kirasu ko da Wanda ze wakilci auren Amma babu Wanda yazo karshe shiya tsayamin wanda sukazo da mu'azzan ya zama waliyinsa A masallaci bayan sallan azahar aka d'auramin Aure da mutumin da bansan waye shi ba.
Kai! ranan nayi kuk'an da yafi na ko yaushe Larai tasani a gaba nayi wanka i'ta ta bani sabon kayan yarinyarta D'aya na saka Wai Ashe a ranan zamu tafi ban sani ba se da Akayi la'asar tace in had'a abinda ya dace na d'auka "Inna nifa ban gane in had'a abinda ya dace ba" Larai tace "Hauwa tafiya zakuyi.." da sauri na Mike har inna dafe Qirji "Ni dawa zamu tafi Kuma inna ne?" Murmushi Larai tayi kafin tace "Keda mijinki Kinga shi ba d'an garin nan bane..."
"Nashiga uku da Allah kimin rai mutumin da bansan wanene shiba zan bishi wayyo Allah kumin rai" kamoni tayi tare da zaunar dani "Hakuri zakiyi Aure babu inda baya Kai mutum.." nasiha ta shiga min Liman ma ya shigo ya d'ora da nashi nasihar Inna kuka suka karkatoni gurin jibgegiyar motarsa Mu'azzan dake zaune a mota shida abokinsa suna Hira cikin hiran abokinsa yace "Kai kaga yarinyar Kuwa Arab daga ganinta akwai nutsuwa kalli yanda take zuwa k'anta a kasa" mu'azzan yace "Wallahi inna tausaya mata yanda Zata shiga cikin iyayenta" Dariya Abokinsa yayi sannan yace "Gidanka Gobara ne zasu iya sata zuba mata fetur su k'yatta mata ashana" runtsa ido yayi yana tuna Gobaran dake gidanshi.
"Dan Allah kalleta fa , karaman yarinya 'yar sha uku" fitowa sukayi Abokinsa ne ya karb'i bakon kayana yasa a bayan motar Baya ya bud'e Inna kuka na shiga k'ankame jikina nayi tare da cusa kaina a gwiwa na kuka nake wiwi haka naji tashin motar Kara sautin kuka na nayi suna tafiya ba Wanda yace min ci k'anki tafiya yayi nisa min munfita Obudu har mukazo Gboko har muka bar jihar benue inna kuka daga Nan muka d'auki hanyar abuja barci barawo ne ya d'aukeni Inna sauke a jiyan zuciya Jin shuru na Dena kuka ne ya sashi lik'awa Nan yaga wiyanta ya karkace "Adam tsayar da motar na gyara yarinyar Nan" ba musu ya tsayar fita yayi tare da bud'e baya kwantar dani yayi sannan ya dawo gaba yana zama yayi shuru Adam yace "wayaga mijin mata hud'u ta hud'un ma yarinya yar Sha uku.. Allah sarki yarinya har na hango yanda za'ayi wasan qwallo dake" dukan wasa Arab ya Kai mishi "banson Shakiyanci mubar wannan maganar Wallahi fargaba na bansan yanda zamu kwashe dasu ba" tsaki Adam yaja "inna jin takaici haba se kace ba namiji ba! Ka tsawatar musu ma ya gagareka Wai ace kana da mata har uku ba kwanciyar hankali fitinar yau daban na gobe daban wallahi idan ka Kai musu wannan mareniyar suka cutar da i'ta kai da Allah domin bawai biyan bashi kad'ai aka baka ba, wallahi amanace iyayenta suka baka inka barta matanka suka nakasata Kai da Allah" Arab yace "naji Kai gwara na kaita Zaria ko na mikata Gurin Hajiya kawai , mahaifiyarshi Kenan" Adam yace " wallahi kanada aiki gwara de ka Kai musu Susan matsayinta a gurinka" Arab yace "shike Nan" a haka suna hirarsu har suka karaso abuja.
Nik'an innata ramuwar barcin da banyishi kwanakin baya ba Gidan shi nacan gaba da babangida market , Gidane babba Wanda fad'ar had'uwa da tsaruwanshi bata lokacine hon adam yayi megadi ya bud'e mishi kofa yana gama fakin suka fito hannu Adam ya Mika mishi sukayi musaba daga Nan ya Mika mishi makullin motarsa "To abokina fatan alkahairi zan d'auki motana nima naje naga tawa Matar a kula da 'yar mutane Dan Allah" Arab yace "nagode a gaida Maryama" Adam yace "insha Allahu" bud'e bayan motar yayi tare da Kiran sunana jiddah bud'e ido nayi "fito Arab na jiranki"
"Waye Arab?" Adam yace "To mijinki" take idona ya kawo ruwan hawaye haka na fito kai seda na tsorata wallahi na d'auka ba mutum bane farinshi yayi yawa kaman ka tab'a jikinshi jini a fito kasancewar d'azun ko kallonsu ma banyi ba bare nasan yanda yake babban mutumne Amma kud'inshi ya b'oye girman nashi.
Gaba yayi nabi bayanshi muna doso kofan gabana ya buga ras tsayawa shima yayi kafin ya juyo ya kalleni girzgiza k'anshi yayi tare da tura kofan kwan..! Se sauk'an kofin glass a goshin sa har hulanshi ya fad'i dafe goshin yayi tare da fad'in "waiku wasu i'rin dabbobi ne! Kullun se kuci ku hau ihu kaman karnuka ! jubi Gidan Nan kullun a hargitse ni Kenan inna da mata uku bani da kwanciyar hankali haba! Haba!! Wannan wacce i'rin masiface" nide kasa nayi na d'auko hullanshi ji kawai nayi an fisge Juyowa nayi Dan inga wacece wata farar mata ce fiska a d'aure ta kalleshi sannan tace "Ibrahim Nafisa ce masifar ko Zainab dan ni Fure wallahi baka isa ka kirani da masifa ba Ga karnuka nan..." tana nuna Nafisat da Zainab "Kutuman uban Amma ke Fure'atu anyi yar..." Faf Fure ta make mata baki Nafisat ta kamo wiyan rigan Fure "ke yanzun Dan Kinga kinyi Kiban rashin zuciya shine zakice min kariya kazama dake shegiya me warin hammata..." Wallahi bansan lokacin da na k'yalky'ale da dariya ba kalli tib'a tib'a dasu Wai suna fad'a da junansu.. juyowa sukayi shi kuwa ya jani bayansa Dan yasan halinsu zasu i'ya makeni a gabanshi ba damuwarsu bane "Ke Kuma daga l'na aka rarumoki kasan de bama bukatar 'Yar aiki ko?" Arab yace "Kai! Kai!! Ya isheni haka haba!! Duk kunbi kun cikawa mutum kunni..." ZAINAB tace "Heee Tsaya nima kana cikamin kunni Bayani zaka Mana wacece wannan?" Ta karasa maganar tana jawoni "ku zauna na muku bayani to" Zama sukayi a kasa dukkansu domin kujerun ma an turasu gefe tsaban fitina da bak'in kishi i'rin nasu.
Seda ya jawo D'aya ya zauna domin be i'sa yace a kawo mishi abin Zama ba yana Zama ko sauke numfashi beyi ba Nafisat tace "munajin ka" Arab yace "yanzun ko arzikin ruwa da abinci bazan samu ba..." Fure tace "Kai kai dakata lbrahim babu baiwarka anan ka Mana bayani wannan" nunani tayi Arab yace "Matatace.." wayarshi ne yayi kara mikewa yayi tare da fad'in "Ku bata abinci da masauki inna zuwa" fita yayi da sauri yana Kara wayan a kunninsa.. a sukwane Fure ta tashi hannuna ta kama "ke fad'amin Gaskiya Wai da gaske Auro ki yaje yayi ko sadakarki aka bashi domin nasan halin mijina seya wanke hannu kafin yake zab'o mace kalle ni da kyau ki kalli sauran kin gammu da muni?" Girgiza mata Kai nayi Nafisat tace "fad'amin da gaske ke matar shi ce?" Shuru nayi Zainab ta zaburo tare da daka min tsawa "Ke ba magana ake Miki ba!" Da sauri nace "Eh Eh matar sa ce ni..." Ai ban rufe baki ba naji ta d'aukeni da mari fau.. har seda gefen bakina ya fashe da sauri Nafisat tayi kichin galan d'in karanzir ta d'auko tashiga zazzaga min a jiki Zainab ta cire min himar ihu nasa Fure taje ta d'auko a shana Tsayawa tayi tana karemin kallo "in banda maza ma da shegen jaraba uban me zeci a jikin wannan yarinyar Qirji a shafe ba cinya ba sharab'a Yau zakije lahira in aka tambayeki ya kikazo a haka kice *Matan Mu'azzan Balarabe* ne suka jefoki baki shirya ba tana shirin k'yatta ashana ya shigo a guje dan tun a waje ya fara jin hayaniyan su yana doson kofan yaji ihu na abinda yasa ya shigo a guje ke Nan ture fure yayi ta fad'i ragwajan kafin suyi wani Yunkuri ya d'aukeni kaman yar Baby da sauri ya fita Zainab da Nafisat ne sukabi bayanmu "Bud'e min Get da sauri" makuli yasa ya bud'e motan domin gudun ma be karb'esu ba Sabida Kiba Ta gurin Direva ya turani a kujeran gefe motan ya shiga yaja kofan a guje yaja de de lokacin da suke karasowa da gudu suka rufa mishi suna nishi "Zainab tace zaka dawo ka same mu wallahi" juyowa sukayi kowa na zuba masifa a bak'in kofa suka samu Fure'atu "I'na suke?" Cewar Fure Nafisat tace "Ya tafi" Fure tace "aikuwa ze dawo ya sameni" Zainab tace "i'rin ke kad'ai ce matarshi dole ya dawo ya sameki ai"

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now