page 24

526 27 6
                                    

♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

F.J.W.A

Page 24

Sati biyu kafin ta farka fisƙanta da suke tunanin zai Sami matsala yana nan sarai taji sauki tade samu karaya a hannunta na hagu, lokacin data farka shi kad'ai ne Gurinta sai Hanisa dake waje ummi Kuma taje Gida, domin tunda ya kawota asibitin yake Sintiri yaki ya mayar da Hankali gurin aikinsa Ummi ta mishi magana akan ya dakata da Zuwan Amma yaki A hankali ta bud'e idanunta haske ne taga ya mata Yawa mayarwa tayi da sauri ta rufe tana jan numfashi da karfi jin yadda Hannunta ke Zugi, da sauri yazo Gare ta cikin Tausayawa yace "Jiddatu Nah.." cikin wani i'rin Yanayi ya Kira sunan Wasu i'rin zafafan Hawaye ne ya shiga sauko mata Bata tsanmaci Ganinsa dai-dai wannan lokacin ba, Me ma yakawo shi gareta, me zai mata! Bayan duk ta silarshi Mijinta ya barta, a dalilinshi aka rabata da d'anta Kwaya d'aya tilo, yaron da take jin K'aunarshi fiye da komai Na duniya, bud'e idonta tayi fess saman fuskanshi "Me ya dawo dakai cikin Rayuwata? Nabil ka dena bibiyata na rok'e Ka, Dan Allah ka tafi.." ta fad'a tana nuna masa Hanyar Kofa. "Kiyi Hakuri bazan miki yadda kike so ba..!" murya cik'e da kuka tace. "babu Alkhairi a tarayyar mu Nabil ka dubi Girman Allah ka tafi, Akan ka, Mijina ya barni, Akan ka, Ya rabani da 'Dana yaron da nake jin K'aunarshi fiye da kowa.." hannunta mai lafiya ya kama. "Allah zai bamu wasu ki nutsu mana Baki ganin Halin da kike ciki ne?" Kwace hannunta tayi "I'na ruwanka! Kai ko maza sun Kare bazan zauna inuwarka ba.." wani i'rin Kallo yake bin ta dashi cik'e da tarin mamaki kenan har yanzun Bata murdinsa shi yake Haukar banza , murmushi ya sakar mata koma ya Zatayi shi dai Yana K'aunarta Ganin taki yin shuru ya Sashi bin jikinta bakinta ya kama Yana sauke Numfashi a hankali, runtsa idonta tayi da sauri tana dukan Qirjinshi da ya tokareta wani i'rin bakon Yanayi take ji, bin ta, yake sosai yana Kara sakar mata jikinshi K'asa K'asa ta saka wani i'rin kuk'an da ya gigita masa lissafi da Sauri ya barta lokoci d'aya idanunsa ya sauya cikin tsananin bukatar son kasancewa da mace yace. "Kiyi Hakuri.." sannan ya fita motar shi ya shiga tare da kifa Kanshi saman sitiyarin Yana sauke Ajiyan zuciya Shi kad'ai yasan me yake ji game da i'ta, ya daɗe yana sauke numfashi kafin yabar asibitin, Yunkurin tashi take amma ta kasa, jikita yamata nauyi, Hanisa data shigo ne, ta taimaka mata ta tashi zaune tana sauke ajiyan zuciya kallon ta tayi sosai, "Ya jikin?" cije laɓɓanta tayi sannan tace. "Da sauki wanka nake so" Hanisa tace "Bari ummi tazo zata san dabar da zatayi" Gyaɗa mata kai, kawai tayi.

Shuru suka zauna har ummi ta dawo, i'ta ta taimaka Mata tayi wanka tare da sauke sallolin dake k'anta.

A hankali lafiya ta fara samuwa Sir Nabil na musu hidima sosai domin jinyarta shi ya d'auki Nauyi, har yanzun Bata bashi fuskan da zai fuk'anceta ,da zaran ya bijiro Mata da bukatarshi Kaucewa take , bata jinshi a ranta Har suka dawo Gida Yana bibiyarta, bai i'ya zuwa Haka kawai ba, sai ya ciko mata leda da kayan siyayya Ko kallonshi batayi bare ta Karb'a Abin hannunsa , a Haka aka kwashe wata shida, Zaune take a d'aki ta jingina da Gado tayi zurfi cikin tunani ummi ce ta shigo har ta zauna Bata San ta shigo ba, i'do ta qura mata.

"Hauwa zuwa yanzun ya kamata ki cire Batun Aakif tudda yace shi bazai baki d'anshi ba, kiyi hakuri, ki dawo da walwalarki , Gaba-d'aya kin sauya kin zab'i rayuwar d'aki fiye da komai , baki dogon magana, kin Kori duk manimanki zaman ki Haka ya i'sa ,ya kamata ki duba Nabil yana da Nagartan da zaki soshi , shi mai K'aunar ki ne, bai kamata ki ringa masa i'rin wannan Walak'ancin ba, kefa ba yarinya bace , kinsa abinda ya dace , bawai zan tilas miki lallai ki Aure shi bane , a'a shawara nake Baki, ba umurnin ba, bazan miki dole ba , inhar baki murdin zama dashi ki fad'a masa , ya dena b'atawa K'anshi lokaci" murmushi tayi tare da Gyara zamanta. "Ummi Nah umurnin ki kawai nake jira nasan bazaki zab'amin abinda zanyi kuka ba, tunda har Nabil ya miki shi kenan..." Ta fad'a ranta na k'una. Kallonta ummi tayi sannan tayi murmushi.

"A'a zab'in ranki nake so kibi ba nawa ba, banso na Cutar da zuciyarki.." katse ummi tayi. "ba Haka bane Ummi" daga Haka suka Rufe maganar shuru kwana biyu bai zo ba, duk da Ranan Karshe da ya zo Bayan tafiyarshi ya Kira Bata d'auka ba, domin bata bukatar Jin muryan shi , A hankali ta d'auki waya kaman zata kira shi sai Kuma ta basar tare da tura mishi "Uhmmm" rashin zuwan nasa ya dameta ko ba komai mai sonka yafi mak'iyin ka.

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now