Page21

553 33 21
                                    

♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

F.J.W.A

PAGE21.

Zauna nake Amma Zuciyata na tsinkewa Haka kurun bansan Maiyasa ba, jefi, jefi nake kallon wayata tunda na Koreshi yai zuciya Bai sake waiwayata ba Yau kwana biyar Gashi banjin Qwarin jikina sosai na kasa Gane meke damuna. Tsaki ta kuma yi a karo na ba'adadi, sannan ta mike bakinta d'auke da Sunan Allah Kichin ta nufa frizer ta bud'e tare da Kwaso Kayan marmari Kunnun Tsamiyan da tayi tun safe ta d'uma sannan ta nufo d'akin tare da Kulle kofarta.
Tana zama taji ana Kwankwasa kofar "Yah ilahi Waye?"
A kufule yace. "Banson isk'anci Zoki bud'e min Kofa!" Bud'ewa tayi zai kamota ta kauce mishi shigowa d'akin yayi sannan ta Rufe Kofar, bata kulashi ba, ta zauna tare da D'aukar Kofin zata kai baki ya rik'e hannunta yana kallonta,

Taki yarda ta kalleshi Kanta na kasa hawaye na sauka saman fuskantar Harga Allah ta gaji da Gidan Arab maganarsa ne ya katse ta. "Kefa kika koreni..." d'agowa tayi a zafafe zata sauke mishi kwandon Bala'i sai ta Kyale ,sanin Mahimmanci da darajar sa, Mijinta ne, be kamata ta ringa d'aga masa Murya ba, Jan hanci tayi sannan ta fara magana tare da zame Hannunta. "Kana i'ya sauke musu Hakkin su dake wiyanka Amma ni ka kasa, Girki na kake d'auka ka, Kai musu, ban tab'a Rik'e ka Ran nasu ba , Amma dake ni Bora ce Banida martaba da Matsayi matar Cushe ce Ni, ban i'sa ka zauna Tare da ni ba, Yaushe rabon da ka siya min sabulun wanka ko omon wanki? Kayan Abinci na ya kare, wata Uku kenan, ni nake ciyar da kai na, kana shiga kichin ko wacce da Band'akinta. ka duba abinda Bata dashi, ka zuba Mata, amma dake ni banda d'iyoyi (Yara da yawa) da kai shine ka banzatar da Lamarina Kaji tsoron Allah Yallaɓai! Ka Gyara Gidanka Ka tsaya da kafafunka , bawai ka zauna ana baka Oda ba, Banida Lafiya baka Shigomin Bare ka duba ya Nake ban fita aiki duk da ka sani Amma baka tambayi dalili ba, da Zaina ce ko Fure Jiki na b'ari Zaka d'auki Mota.."

Jik'inshi ya bala'in sanyi kalamanta ya tab'a shi Gaskiya take fad'a mishi duk anyi Haka shi akaran kanshi yasan Bai kyauta Mata ba, tana da kawaici Da d'auke kai, Hannunta ya kama jikinshi na rawa "Dan Allah kiyi hakuri" murmushin da yafi kuka ciwon tayi "Wacce ni da Mijina zai bani Hakuri naki Hakura? Hmm ya Wuce ai.." da sauri yace.

"Dan Allah" ya fad'a Yana langwab'ar da K'ansa, murmushin Yak'e ta sakar masa "Bakomai" d'aukan Kofin yayi tare da kaiwa bakinta Karb'a tayi daga hannunsa Yana kallonta tana Sha, har ta kammala komai. zata kwashe kayan ya dakatar da i'ta tare da Karb'a yakai kichin , laptop d'inta ta kunna ta fara Aiki shigowa yayi tare da zama saman Gadon.

Share shi tayi duk da tana sane dashi "Kizo mu kwanta"

"Hmmm aiki..."

"Ki abinda nace!"

Kashewa tayi tare da mikewa kashe hask'en d'akin tayi tare da hayewa Gadon , abinda take tsammani shi ya kokarin Yi, Bata hanashi ba, Haka tabar shi ya samu nutsuwar da yake bukata Amma da fad'a suka rabu domin ji tayi bata jin dad'in mu'amular da kyar , ya kyaleta Yana tsaki "Meke damunki? Ba yadda nake jinki bane Babu danshi ko kad'an a jikin ki , A bushe kike ba 'Dand'ano.."

"Kaga Dakata! Base ka zageni ba, Zaka iya tafiya Gurin Zuma! K'orama da, danshi!" ta karasa maganar tare da Nufar band'aki koda ta fito Bata sameshi ba Bata damu ba, ta Rufe Kofarta tare da tofe d'akinta da addu'a tayi kwanciyarta. Amma ta kasa barci Tana tunanin Yanayinta sharewa tayi kawai.
Washe Gari, koda tayi sallah kwanciyarta tayi sai 11:30Am ta shirya d'akin Fitowa tayi taga kaya jibge A falonta tsaki tayi tare da Nufar Babban Falon inda take jin Hayaniyar Su, tsayawa tayi tare da Rik'e K'ugunta " Yallaɓai" Be kulata Ba, ya cigaba da Hirar da Suke "inna maka magana Kayi Banza dani!" Juyowa yayi rai a had'e "Wai ke wacce i'rin Dabba ce Me sa kike Haka ya zakizo ki tsaya tsakiyar Kan mutane kina musu ihu Jakar innace Ke!?" Cewar Fure Tana hararan Jiddah "Akwai Dabba jaka Bayan ki? Ke har kina da bak'in fad'an magana ban kasa, dake ba, domin Baki i'sa nayi dake ba, Banza shashasha Da Mijina nake magana.." Murmushi Zaina tayi tana jifan Cikin jikinta da wani i'rin shu'umin Kallo, bata ce komai ba, ta Mike tare da Kama hannunshi zasu fita Jiddah Tasha gabansu "Dalla inna maka magana ka mike zagwai-zagwai zaka bita ka zama bindinta ne? Da take Gaba. Kana baya? Kaga nafa gaji, Kaman yadda kake zuba musu cikin kichin Nima kaje ka kwashe ka zuba min!" Wani i'rin duka Zaina ta Kai mata a ciki, K'asa tayi tare da saki kara Kaman ranta zai fita ta kasa motsin Kirki domin naushin Ya tab'a ta sosai ,

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now