page 25

586 27 6
                                    

♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

F.J.W.A

25
Murmushi ya sakar mata tare da matse hannunta lalub'ar Qwayar i'donta yake Amma taki ta kalle shi ,fisk'anshi ya kai dai-dai nata yana fesa mata Numfashin sa , a Hankali yake bin fisk'anta yana sauk'e Ajiyan zuciya "wai mai-yasa kake min haka ne? Wallahi banso Nabil ka dena Kunsantowa Gare ni" Kallon qwayar i'donta yayi tare da Lumshe nashi cikin wani i'rin Yanayi ya kwantar da kanshi saman kafad'arta be San abinda yake fisganshi ba, da zaran sun kasance su biyu susuce mata yake , in har bai rab'eta ba, ba ya Jin dad'i cik'e da mutuwar jiki i'tama ta zame shi daga Gareta Allah kad'ai yasan abinda take ji i'dan ya kusantota b'oye qwallarta tayi "Kiyi hakuri dan Allah Hauwa ki amince min wallahi inna azabtuwa da yawa ki tausaya min ki kawowa Zuciyata da rayuwata agaji, inna bukatar ki , kusa dani muddin muka ci gaba da , zama Haka wallahi shaid'an zai shiga tsakani ni kaina bana sanin lokacin da nake kusanto ki.." ya karasa maganar kaman zai fasa kuka mikewa tayi domin zaman ya fara i'sarta "Dan Allah" juyowa tayi ta kalle shi tare da Girgiza masa kai "Wallahi bana jinka a raina , Nabil bana son..." Kasa karasawa tayi mikewa yayi shima "Shi kenan Nagode Jiddah" juyawa yayi jiki a sanyaye ya fita. Bai san wani i'rin zuciya ne, da i'ta ba jinginuwa yayi da motar sa tare da hard'e uannuwansa duka biyu a qirjinsa. Motar Mijin Halimatu ne ya shigo Gidan bud'e motar shi yayi zai shiga sai yaji Muryan Halima tace cewa. "Sir Nabil Kaine Haka?" Murmushi yayi mata sannan yace "Maman biyu barka ai na d'auka mai Gidan ne Ashe kece"

"Wallahi har ka gama da sahibata?" Sosa kanshi yayi sannan yace "Wannan sahibar sai a hankali Bansan me na mata da Bata K'aunata ba, Korana tayi" Dariya Halimatu tayi "Karka damu kabar komai Gurina insha Allahu zan shawo maka K'anta" cik'e da jin dad'i yace. "Nagode qwarai" daga Haka sukayi Sallama tashigo Cikin Gidan d'akin Umminta ta nufa ..

Koda ta shiga d'aki zaman tayi tare da ranfa tagumi tana Tunaninsa bawai bata son sa bane , Gudun Kishiya take yi, Bata jin zata yi hakuri kaman baya hawaye ne ya sauko mata Har yau Bata samu Mai mata son da Nabil yake mata ba, "dole kiyi kuka ke k'anki kinsan baki kyautawa Zuciyarki mai-yasa kike gudun abinda zuciyarki take so? Har yau kina abu kaman wata 'Yar K'auye kina wani baya-baya dashi Bayan kinfi kowa sanin shine mai-miki so na Hak'ik'a nifa shawara nake baki karki Cutar da k'anki akan wani dalili mara tushe meye matsalarki da matar sa , kaman yadda take zama K'arkashin sa , kema haka zaki zauna ,ba akanta zaki zauna ba, Amincewar ki yake bukata in kuma bazaki Aure shi ba, ki fito fili ki fad'a masa ya daina zuwa kawai haba Yanzun fa angirma akwai banbanci da Baya.."

Cikin yamutsa fiska tace "wa yace miki inna son sa?" Kama hab'a Halimatu tayi tana Mata kallon k'anki kika raina ,k'asan filonta ta d'auko Wayan da ya Bata tun baya har Yanzun hotonshi ne fiskan wayar Sunkuyar da kai tayi K'asa tana mamakin ya'akyi tasan da wayar .

"A hak'an ne baki sonsa ? Tun bayan rabuwarki da uncle Arab kike sauya waya duk abinda kika San daga hannunsa ya fito kin b'atar dashi sabida ba K'aunarsa kike ba, abinda kake so ne zaka tattala shi Yanzun ba gashi ba, shekarawa nawa kina adana wannan wayar?"

Jiddah tace "Kinga nifa kawai banson Auren ne, inna da matsala banso na Cutar dashi dan wannan mannewar da yake ma, Mutum ba hakuri zai yi ba.."

Cikin dariya Halimatu tace "Au Kice d'an son ayi ne ? To aih hak'an yafi Kyau Zaki karb'i yaren Novel yadda ya dace.." Jidda tace "Kefa 'Yar iska ce, in baki furta ba, Baki Jin dad'i, ni bama wannan ba , ke bani da lafiya Hmm" kasa karasawa tayi tare da juyar da k'anta Gefe Wallahi kunyar ta fad'i damuwarta take ji,

"Rashin miji a kusa ma aih Babban rashin lafiya ne tunda Ba'a maka wuta-wuta kullun..." Hannu biyu Jiddah ta Kai mata duka "Allah ya shirya ki" Halimatu tace "Ashirye nake kumma kullun sai Abban Aaleen yana kara bani darusan"

"Mai ya kawoki Gidanmu a daren Nan?" Zama tayi bakin Gadon "Wallahi haka kawai naji inna son zuwa Naga sahibata"

Kwana Biyar Bai kirata ba, a ranar na shidan ne ran asabar Ummi ta sameta d'aki tana duba sakon da aka turo mata. "Shalele tashi ki shiga kichin inna da bak'i" mikewa nayi tare da fad'in "Toh ummi na" Kichin na shiga inna cikin Aikin saiga Hanisa ba jimawa saiga Halimatu da iyalanta Nan muka fara aikin mu uku muna Hira,

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now