EPISODE_7

53 7 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣7️⃣*

"Forzy!! Forzy!! Forzy!!"....

Cikin Sanyayyiyar murya takejiyo hakan,muryar maishi ko na Fita Cikin Rad'a alamar Mai Kiran wannan suna bai bukatar wani ko wata na daban ya jiyo hakan....Forzy ko cikin salon kasala ta bude idanun.....nata inda tayi Arba da abin daya matukar bata mamaki wanda wannan abun ko shine,hada Ido tayi da Ahmed a zaune gefen ta wanda shine Mai Kiran nan nata,Cikin farin ciki hade da murna ta yunkura hade da rungume sa.... zubar kwalla ta soma Tana mai cewa.

"Banyi Zaton Zan sake saa kwayan idona a naka ba *Ahmed* ,A tunani na Narasa Kane Har Abada.....Amma mayyasa ka zabi ka kyaleni a baya? Mai yasa kakijin shawarar Dana Baka??,Koda shike mubar wannan magana a gefe guda tunda gashi kaddara ta sake hadamu,Dan haka Ahmed Dan Allah karka sake barina Cikin kadaici.... domin kuwa Nayi kewarka sosai."

Hakan ta furta yayin da suke a rungumen da juna....Tana Kuma shesshekar kuka
*Guess what* Budar bakin Ahmed ko yace da ita.

"Yanzu atunanin ki tare muke ne Forzy??"
Tambayar Daya matukar razana Forzy Kenan hade da dagula tunanin ta,kasa sakar jinin nasa tayi danko still rungumen suke da juna...........

Zuciyar tako bugun uku uku ta Soma,Cikin yanayin tsoro ta saukar da idanun ta kan gadon Bayan Ahmed....
Cikashi tayi Cikin sauri hade dajan jikinta gefe guda Bayan tayi arba da gadon Bayan nasa Wanda jinine ke zubowa ta sanadiyar manya manyar Raunin dake gadon Bayan nasa,Wanda suka Kuma rube hakan yasa har Mayan tsutsotsi ke ta shagalin su aciki.

Forzy ko datasan Abinda zata tarar a fuskar nashi dako tayi hakuri su kasance a rungumen har *illa Masha Allah*

Bayan ta cikashin ne taja kanta da baya tayi Nesa dashi ba kadan ba,nanfa ta Sami damar duba hannayen nata......
Hmm Mai zaifaru kuwa??atunanin ku

Tsutsotsin ne suka mamaye hannayen nata biyu,yadda kasan Kudan Zuma haka suka mamaye ko'ina a hannun nata....

Forzy Ihu take tafitar hankali yayinda zazzafar kwalla take zubowa a fuskar,haka zalika ta kasance Tana kokarin sharesu daga Jikin nata Amma ta gagara hakan Domin Kuma kokari sune su shiga Cikin Naman Jikin ta.....

Dago idanun ta datayi kuwa Sai tayi arba da fuskar Ahmed din Wanda yin hakan yasa ta sake buga ihu hade da sumewa.....Hmm
Munnin Fuskar Ahmed tayi tsanani ta yadda ba mutum ba ko bakin aljanine zaiyi arba da Shi saiya razana.....

Ihu hade da yunkurawa tayi ta yadda saidata Mike tsaye kafin ta take biriki,Nishi tasoma nafitar hankali Kai Kace dutsen Uhud aka daura mata...a gadon baya.
Bayannan sai ta d'ago Hannayenta ta Dubai,shasshafawa tayi daga gwiwar Hannu zuwa wuyan sa kafin nan tayi ajiyar zuciya sa'anan tayi wata magana kasar zuci cewar ta shine.

"Allah Nogode da wannan bala'i ta kasance cikin mafarki ne.....Ba'a zahiran ce ba
Yah Allah ka kareni da kariyar ka,ka kuma gafartawa Ahmed idan nashi tariga ta riskeshi" .... 

KOFAR AJALI 2021Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz