EPISODE_3

93 12 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣3⃣*

Nan kawai sai sukaji wata iska mai karfin tsiya ta zugosu cikin wannan kofar,bayan ta kaisu cikin tayi watsi dasu sa'annan kofar taja kanta ta rufe.

Karfin Iskar nan ko sai data jijjiga kowani bishiyar dake fadin wannan daji hatta dabbobi sai dasuka zube kasa sa'annan suka sake mikewa tsaye.

Atif shima haka wannan iskar ta bugasa da wata bishiya.....ya zube kasa dakiyar yake iyya d'ago hannayensa,yana dubasu.

Dafa bishiyar dake gefen sa yayi da hunnun sa ta hagu a sa'in da yake mikewa,hakan ko ya mike cikin kasala,yayin da yake dafa goshi alamar yaji rauni a gurin.

Mikewar tasa keda wuya sai yaji wata kara mai kamada kukar Damisa a bayansa.
Hakan ko akayi danko juyawar da zaiyi sai yayi arba da wata halluta mai kama da Damisar amma kuma girman wannan halitta tama zarce na kosheshiyar doki.

Sa'annan kuma gashin jikin wannan abar bakine sid'ik,ga kuma many'an hakwara da kuma many'an idanu jajir.

Bayan yayi arba da hakanne ya tika gudu a dari,yayinda wannan abar ke biye dashi a baya,kamar kurar dayayi shekaru da dama ba tare da ci ba,yau kuma saiga abinci har gida.
*Toh Yakuke ganin abar zata kasance*

Haka fa sukayi ta zaga wannan guri duk ramin da Atif ya shiga ya boye sai wannan abar ta kwakuloshi,haka ya marnewa Atif a baya,amma kuma duk da girman tasa baisa ya iyya kamo atif ba.

Cikin wannan yanayin suka kasance har saida suka tsinci kansu gabar wannan gini inda sauran abokan tafiyan Atif suka shige ciki,wato kofar nan mai cike da ababen al'ajabi.

Bayyana sukayi a gurin inda Atif garin gudu wani itaace ya shige tsakanin kafafun sa kawai saiyaga kansa a kwance kasa.
Cikin sauri ya d'ago,amma ko 70% na jikinsa still a kwancen danko gwafewa yayi da gwiwar hannayensa, ta baya ya dago kai yana kallon wannan halitta.

ganin abar tayi kusa dashine yasashi yinkurin mikewa,amma sadly bai sami damar yin hakan ba,danko wannan halitta tasa kafafun gaba ta turashi da baya,Atif ko sake tsintar kansa yayi a kasa hakan yashi yayi ya soma jan jiki yana kuma jan kansa da baya yana kokarin tserewa wannan abar duk dayasan hakan bamai yuwa bane,danko taku daya wannan dabba zatayi ta murkusheshi,amma hakan baisaka ya karaya ba.

Haka wannan abin ya tsaya kallon sa,saifa dayaga yayi nesa kadan kafinnan yayi wup ya dire kan kafafun Atif, nanko Atif yakwarma bagidajiyar ihu haka wannan abin ya daga hannun da niyar yamusar fuskan Atif amma kuwa bayan ya daga hannun yayi arba da wannan gini.

Kwarma bagidajiyar ihu yayi shima bayan yayi arba da wannan wuri,cikin abinda bai wuce dakika guda ba,ya tarwatse ya tashi sama kamar hayaki ya lulluka cikin gajimare,abin dariyar kuma shine Atif a tunaninsa wannan ihun daya yine ta tsorata wannan abar,shi baisannan meye wannan halitta ya hango ba.

KOFAR AJALI 2021Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt