EPISODE 12

52 4 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣2️⃣*


🦇🦇🦇
"Aiko Babu Daman tabasu domin kuwa daga zarar mun taba guda daga ciki tofa mun afka cikin chakwakiyar bala'i da Bamu San  iyakarta ba"😳...
Fadar Al-Hussien kenan....

Da juyo hakan ko Harun ya saukar da idanu alamar nazari,bayan Nan ya juya izuwa ga #Samra ya Mika Mata taswirar dake hannun sa.

"What?" Cikin salon Tambaya Samra ta furta hakan inda yace da ita..
"Ina son ki jagorance mu"

"What!!"
Cike da mamaki Tina ta furta hakan hade da zuwa idanu, sa'annan ta sake da cewa

"But why?"

"Wallahi Babu komi cikin Raina,kawai Naga jajircewar ta,Kuma inaga tafiyar tamu zata kayatar idan ita ke jagorantarmu."

"Hmm" hade da murtuke baki Samra tayi ganin yanayi da Samra ke ciki yasa Mufydah tayi sauri cewa.

"Guys shin kunsan ana binmu sallah na yini guda kuwa? Robonmu da sallah fa tun asuba'in jiya"

"Kuma hakane Fa ya kamata ku Sami guri da Kuma lokaci domin biyan sallolin da ake binku."
Haka #Simon ya furta shida ya kasance Kirista a cikin su.

Al-Hussien ko ya furta cewa
"Hm maiyasa kuke sakaci ne da yawa,Ashe bayan rashin tuno addu'o'i harda salloli ciki."

Aiko dukkan ninsu shiru sukayi inda Harun ya ce da Al-Hussien.

"Gaskiya mun sha'afa ne,domin wannan Guri na cike da Almara iri Daban daban,Amma duk laifina ne domin lokaci Dana farka daga sumar da mukayi na Tino cewa bamuyo sallah ba na yini guda,shiyasa nayi taimama na idar da sallar Amma lokacin da sauran abokan tafiyar na suka farka ban Tino musu da hakan ba,kuskure nane wannan."

"Tunda yanzu mun tuna hakan maizai Hana muyi ta yanzu."
Fadar Mufydah kenan inda Mu'azz yace dasu

"Uhm.. gaskiya Ya kamata Kam muyi yanzu,tunda yau shine karshen wahalar mu,kamar yadda Harun ya tabbatar Mana kunga kenan Babu bukatar mu buya sallah bayan mun fita daga Nan."

"Kwarai kuwa."
Hakan Tina ta mayar masa da martani, Harun shiru yayi Yana ta sauraron su...
Aiko saiga wata kudan zuman na kokarin shige masa Idanu cikin sauri ya soma korarsa da hannu Aiko Yana cikin haka ya hango taron korangwal dinnan na tunkaro su,Ganin haka yasa yayi furucin *Oh no*

"Ya dai?."
Tambayan da Ali yayi masa kenan shida ya fahimci yanayin Harun din ya sauya,ganin bai basa ansa ba ne yasa shi yunkurin juya Idanu izuwa inda Harun din ke fuskanta Amma sai Harun yayi saurin mayar masa da ganin sa hade da cewa...

"We have to leave this place... Now"

"What!,why?, sallar da muke kokarin Yi Kuma fa?"
Fadar Mufydah kenan inda mu'azz yayi saurin cewa...

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now