SEASON_2 EPISODE_9

47 8 5
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
*FB PAGE*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100070173921421
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣9️⃣*

Tauzali Mu'azz yayi da *Atif* tsaye alamar Yana Sallah,aiko kasa rike murna yayi domin kuwa uban kara buga hadi da shewa sannan ya kirawo sunan Atif,a fusace Atif ya waigo inda yayi arba da Mu'azz din tsaye...

"Atif!."
Haka Mu'azz ya sake kirawo sunan nasa cikin Murna yayinda Idanuwan sa kuwa suka cike da kwalla dan farin ciki,a guje ya ruga izuwa inda Atif ke tsaye suka rungume juna....

"Banyi zaton zamu sake hadewa a wannan guri kuma a irin wannan lokaci ba Atif,Gaskiya na tsorata Sosai na dauka shikenan na rasa ka."

Aikuwa ganin yadda Atif din ya kura masa ido ne ya fahimci babu abinda Atif din ya fahimta game da wannan batu nasa domin kuwa rudar dashi wannan batun yayi,nan sai ya sake da cewa.

"Oh Sorry my bad,gaskiya You missed a lot Atif,domin abubuwa da dama sunyi ta faruwa yayinda ka kasance a sume."

"Da gaske?."
Tambayan da yayi kenan inda wannan kyakkyawan budurwa da suka taho tare da Mu'azz ta amsa masa da Uhmmm ta cikin wuya Sannan ta sake da cewa.

"Ina mai tunatar da ku,akwai gagarumar aiki a gaban ku,kuma ba wani lokaci mai yawa kuke dashi ba domin kowani dakika mutuwar ku kuke kusanta,dan haka ya zamanto muku dole ku gaggauta naimo Dutsen haske da kuma kogon kan Sarki Bahru domin su kadai ne zasu baku damar fita daga wannan guri."
Ajiyar zuci tayi Sannan ta sake da cewa.

"Saidai kuma Faruwan Hakan ne nake ganin kamar da wuya,domin kuwa samo Wayennan abubuwa nada matukar wahala dukda cewa kune na farko masu sa'an da kuka iyya kwana a cikin wannan guri ba tare da kun sheka ba amma gaskiya samun wayennan abubuwa zatayi matukar wahala."

Shiru Mu'azz yayi alamar mamaki kafin nan yace da ita...

"Inason nasan wani hanya ne da kuma dabaru da jarumi Zaid yayi anfani dasu wajen kawo karshen Mulkin Bahru da kuma hallaka shi baki daya, sa'annan inson naji tarihin nasarori da Bahru yayi a Rayuwar sa da kuma ɓangarori da ya samu gazawa..."
Furucin Mu'azz kenan inda Atif ya kara da cewa...

"Kuma zamuso muji wace irin matsifune a hanyar samo wayennan abubuwa da kika lissafo!."
Haka Atif shima ya tofa albarkacin bakinsa kamar yasan abinda suke tattaunawan akai, wannan Ƴa kuwa da jiyo furucin Atif Sai ta fashe da muguwar dariya sannan tace dashi....

"Matsifu,ababen tsoratarwa da kuma Hadari dake cikin wannan hanya bazata misaltu ba, saidai kawai muce da ita *Hard way and the only way* sannan kuma babban kalubale da zaku fuskanta game da wannan aiki shine Harun."

"Harun!."
Haka suka maimata sunan nashi cikin hadin baki dan mamaki itako tace dasu.

"Eh Harun, domin yana dauke da bakar kambu (Crown.) na Sihiri wanda wannan kambun mallakan sarki Bahru ne,da wannan kambu kadai zai iyya lalata duk shirin ku kuma da wannan kambu zai iyya fitar da muggan Halittu izuwa goron kasa sannan da wannan kambu zai iyya dawo da Rayuwar Bahru wacce yin hakan babban kalubale ne a gare mu dama sauran al'umma baki daya,dan haka ya zama lallai ku rigasa samo wayennan abubuwa dana lissafo muku su."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 11, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now