SEASON_2 EPISODE_8

38 5 2
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣8️⃣*

MUFYDA
*_Mufyda_* tsala gudu take tana kokarin kaiwa inda su samra ke tsaye wato cikin wannan zagaye nan na wuta,kuma fa sai da tayi hakan amma ta iso gurin a makare,domin saura mata taku kalilan ta shige wannan layi sai ɗaya daga cikin wayennan halittun ya daki kasa ya harbi kansa a daidai lokacin da mufyda ke kokarin juyowa don ganin ratar dake tsakanin su... Aiko bata sami damar Ganin hakan ba domin ji tayi wannan hawainiya ɗaya daki tsalle ya fado mata a fuska, saukarsa fuskan nata ko ya baje hadi da marne mata fuska ya kuma zagaye kan nata baki ɗaya.... babu koda gurin nunfashi bare na jiyo sauti da wannan abin ya ragewa Mufy domin kuwa kama daga tsakar kanta ya sauko har Izuwa wuya wannan abun ya rufe yadda kasan da *Roba* aka nannaɗe mata kan.

faruwan hakan keda wuya mufyda ta yanki jiki ta fadi a saman wannan layi mai ci da wuta... Yayinda ta kasance rabinta na cikin wannan layi rabinta kuma a waje... Ta yadda daga zaran wayennan halittu sun karaso inda gangan jikin nata ke a kwance, kasancewar ta a gurin zai basu daman shiga wannan layin a saukake ba tare da sun bi ta cikin wannan wuta ba.

Zuro idanu *Forzy* da *Samra* sukayi ganin cewa Mufy na kwance cikin wannan hali aiko cikin zafin nama Forzy ta sake komawa ta janyo Mufy ciki, Amma duk da saurin da tayi wajen aiwatar da hakan saida wasu daga cikin wayennan halittun suka sami shiga...
Shigarsu gurin wannan zagaye na wuta ya cigaba da ci ta yadda babu wanin su da zai iyya shiga ba tare da ya kone ba,hakan ne yasa da isar su gurin suka take biriki suka tsaya kallo.

Cikin salon burgewa Forzy ta ɗago wannan karfe da take rike dashi ta rike da hannayen ta biyu,aiko nan sai tayi kama da jarumai irin na shekarun baya da suka shuɗe... Forzy hankalin ta kacokal yana kan wayennan halittu ta yadda kowani irin motsi sukayi idonta na a kansu,kuma tana hakan ne dan kada su kai mata farmaki ta kasa kare kanta bare Samra dake labe bayan ta.

Cikin karfin tsiya daya daga cikin wayennan halittu dasuka sami shiga ya kai mata farmaki inda tayi anfani da wannan karfe wajen buge shi ya fadi gefe guda,dukda tsintar kansa da yayi a yashe hakan bata hanashi sake kai wata farmakin ba bayan ya tashi,haka suka cigaba da kai mata farmaki yayinda ta dauki lokaci tana fafatawa dasu har yakai Samra ta fadi gefe guda dan yadda wayennan halittu suka dawo farautar fuskokinsu,Fadiwan nata keda wuya suka sa Forzy a gaba suna kokari wajen ganin sun Kaita kasa.... amma hakan baiyu ba, Duk da cewar ta kasance a Ruɗe take domin kuwa sun sakata a tsakiya.

Yayinda suka sakata a tsakiyan nasu kuwa sai wannan wanda suke fuskantan juna da ita ya fara kawo mata hari inda tayi anfani da wannan karfe ta buge shi ya fadi gefe guda, amma kuma a binda Forzy bata sani ba shine anfani sukayi da hankali wajen kawo wannan farmaki domin lokaci daya sukayi hakan ta yadda koda Forzy ta sami damar kare kanta daga wannan wanda take fuskanta bazata iyya kare kanta daga dayan ba,itako bata san da hakan bama har saida Samra tayi ihun cewa. "Forzy Watch Out!!."
Aiko jiyo hakan da tayi yasaka ta juyowa inda tayi arba da wannnan halitta ya tashi sama ta yadda babu yanda zatayi ta kare kanta domin ya riga yayi kusa da fuskan ta.

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now