SEASON_2 EPISODE_4

21 5 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣4️⃣*


"ki Kulla da kanki Y'ar uwa.."
Kalmar karshe kenan tsakanin Noor da Forzy,kafin ta sadaukar da rannata gareta.
Tundaga wancen lokacin har izuwa yanzu wannan kalmarce ke saka Forzy zubar da hawaye,Durkushe take gaban wata rubebbiyar turɓaya wacce nake kyautata zaton ta Noor ce.

"Noor maiyasa Kike kokarin sakani cikin kaɗaici?,mai yasa kike kokari ki nisanta kanki gare Ni?."
Cikin Muryar kuka Forzy ke furta hakan, yayinda fuskar ta jike sharkab da kwalla.

"Koda daidai da dakika guda shin kinyi tunanin halin da zan kasance ciki kafin ki aikata hakan?,mai yasa kika zabi rayuwata sama da taki Noor?
Noor Babu wacce na sani anan gurin sama dake,to mai yasa kika zabi kiyi nisa dani,Noor?."

Cikin wannan yanayi Forzy ta kasance na tsawon lokaci da su Atif suka kwashe suna wannan tafiya har izuwa inda suka kasance yanzun,wato inda wata mai kama da Forzy ta jasu Ciki.

Bayan sun tsinci kansu cikin wannan kofa ne yasa ta saki hannun nasa,shiko ya ɗaga hannu inda ya tarar da shatin hannu Forzy ya dawo Kore shar wacce tayi daidai da wannan koren haske daya shige jikin Muzzaffar,Aiko ganin haka yasakashi zura Idanu dan mamaki.

"Ke ba Forzy bace,wacece ke?."
Abinda ya fito daga bakin Atif Kenan inda Mu'azz yayi sauri juyawa hadi da tambayarsa "what?." Cikin harshen turanci.

Aiko da jiyo haka ta take biriki Inda suma sukayi hakan, Atif Kuma ganin Mu'azz ya matsu yaji dalilin sa na fadin hakane yasakashi nuna masa shatin hannun.

Aiko zura Idanu yayi shima hadi da cewa
"how possible,Taya hakan ya faru?."

"Who are you Really?."
Abinda Atif ya sake fadi kenan,hakan ko yasa Wannan da suke kokarin susan ko wacce ita ta juyo.

Zura Idanu Atif Yayi inda Mu'azz ko yayi furucin cewa...

"Tina! How comes Kuma kinanan bayan.."
fara fadin haka yayi amma bayan yayi ido hudu da koren idanun nata mai kama data macijiya yasakashi sauya maganar hadi da juyo ganinsa kan Atif..

"It can't be her Atif,domin Tina ta mutu tuntuni."

Atif shiru yayi sai sauraransa yake Itako Tina fashewa tayi da dariya wacce wannan dariya idan ka saurara sai hanjin cikin ka ta kaɗa haka kuma bayan tayi hakan ta ɓace tamkar walkiya a tsakar dare.

"Atif shin kaga hakan kuwa Tina ce fa, kenan ta rikiɗe ta dawo wata abar na daban?."
Aiko bayan Mu'azz ya furta hakan sai Atif yayi wani Batu cikin siririyar murya cewar sa shine.

"Hakan na nuna cewar dukkanin su ukun sun rikiɗe sun dawo wani abin na daban kenan." da jiyo hakan Mu'azz ya zura Idanu hadi da cewa.

"Idan da gaske ta rikiɗe to inaga sauran ina suka shiga?."
Tambayan da Mu'azz yayi kenan inda Atif ya kirawo sunan Samra cikin Muryar tsoro.

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now