EPISODE_4

82 10 0
                                    

💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
                           💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣4⃣*

Wani kara suka soma ji kamar ta motsin mutum nan sai Harun yace dasu....

"Dan Allah kowa ya kama inda yake,ku daina motsinnan dan kuna tsorata mu....
Atif and Samra nasan kune"

"Taya zakace mune bayan....."
Haka Samra ta soma furtawa amma sai taji Atif yayi shiiiiiiiiiiiit alamar tayi shiru.

Hakan ko sukayi suka kasance sunyi tsit suna jiran mai zata biyo bayan shirun da sukayi......

Soma jiyo wata sauti sukayi *DIM DIM DIM* kaikace sawun samudawane.......
⬇⬇
Wannan sautin bana komi bane illa wasu sanduna dake rarrataya a jikin bago bangaren ne,hagu da dama,suke kamawa da wuta.....domin bada haske.
Soma ci wayennan sanduna sukayi yayinda haskensu ta haskake farfajiyar gurin na y'an wasu dakiku kadan sa'annan suka sake kafewa,haka Suka sake tsintar kansu cikin wannan duhu a karo na biyu.

Sake jiyo wannan karar cen nesa na yowa ta gurin su inda suke iyya hango hasken ta daga cen nesan nanko suka yanke shawarar bin wannan haske da zarar ta karaso cewar mu'azz *wata kila hanya take son gwada musu.*

Haka ko suka laminci zancen suka kuma ankare suna jiran wannan haske ta karaso,kamar yadda suka tsara haka abin ya tafi ba sabani..... wannan haske na ratsowa inda suke suka bita a guje yayinda ta kasance tamkar fitulu dake haska musu hanya.....duk da cewar tana kunnuwa na bayanta na daukewa......

Haka suke guduwa yayinda duhun kebinsu a baya.....Basu kuma tsaya da gudunan ba har saida suka tsinci kansu a wani guri mai dan karen guhu ga kuma zafi har nunfashin mutum na yankewa ya kuma dawo....nanfa Mu'azz yayi danasanin shawarar daya bayar danko wutan nan ta dauke sa'annan basu da damar komawa inda suka fito,domin basuma  gane inda suke ba....

Suna cikin wannan yanayi na kaka nakayi sai Samra ta soma cewa.....

"Zamu iyya kwana uku batare da munci ko munsha ba,mako guda batare da mun sami hutu ba amma bazamu iyya minti goma ba tare da shakar iska ba....dukkan mu mutuwa zamuyi"
Cikin muryar kuka ta furta hakan...

,Furta wannan kalma ta mutuwan da Samra tayi keda wuya sai gurin ta dau shecking [girgiza] kaikace tashin Duniya..
Ga bakin Duhu ga rashin Nunfashi ga kuma girgizar....sa'anan basu masan akanmeye suke tsaye ba.

Al'amarin Wannan halitta Mai Kama da jamage kuwa tsintar kansa yayi a wata kazamemmiyar guri......Gurin na d'oyi matuka gakuma kukan kananun kwari da suka cike gurin.
Nan da nan ya kime ganin kansa cikin duhune yasakashi bude tafin hannunsa nan sai wuta ta tashi cikin tafin hannun nasa.

Ganin hakan keda wiya yawani jujjuya tafin hanun nasa cikin salon burgewa nan wasu abubuwa suka soma fitowa tacikin tafin hannun nasa.... Suna kuma haske yayinda suka kasance cikin suffar malam bude littafi.....haka suka mamaye saman sa.
Nan da nan Guri tadau haske matuka,ganin haka yasashi komawa halittarsa ta ainihi wato wata kyakyawar y'a mai farar idanu ga kuma gashi har gadon baya...

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now