SEASON_2 EPISODE_7

45 9 5
                                    


💀💀💀
          *KOFAR AJALI*
                          _The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
                           💀💀💀
  
_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

                        *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣7️⃣*



"Taya Fitulun gurin kuma suka dauke lokacin guda?"
Furta hakan tayi hade da kai hannu kan sanda da take rike dashi domin ta tabbatar da dalilin kafewar wannan wuta,amma kuma bayan ta aikata hakan ta Kwarma bagidajiyar ihu hadi da yin jifa da sandan gefe guda ta sanadiyyar kunar dataji a tafin hannu ta.

wannan sanda dai hallau tana ci da wuta saidai kuma duk cikin su babu mai iyya ganin hakan,abin tambayar anan shine shin Makancewa ne sukayi ko kuwa....??
Idan muka duba bangaren wannan sanda kuma fadiwarsa gurin ya kama ci da wuta ta sanadiyyar wata bakar ruwa mai kamada Kwalta dake kwance a wannan guri..

wannan wuta dai ci take babu kakkautawa yadda kasan a rumbun kara,yayinda hasken sa ta haskake ilahirin gurin,kowace lungu da sako na wannan daki saida ta dau haske,Readers zaku iyya ganin wannan haske amma kuma su ganin hakan ta gagare su.

Inda Amrita ke tsaye kuma taku biyar gaban ta Harun ne ke tsaye yayinda wannan bakin ruwa ke gangarowa daga sassar jikinsa fuskansa kuma kwata kwata babu annashuwa....

"Amrita! Amrita! Lafiya kike kuwa?."
Fadar Adam Kennan inda Hafsa tayi saurin sake tambayar cewa.

"Amrita wani abin ne ya same ki?."

"Guys Bana Iyya ganin komi!."
Amsan da Amrita ta basu kenan Cikin salon rikicewa,inda Adam Yayi furucin what! Cikin kara, Harzad ko yace dasu.

"Calm down *Amri* bafa ke kadai bace mai ganin wannan duhun,kowannen mu nanan haka yake gani kuma hakan ta faru ne ta sanadiyyar daukewar haske yayinda muke tsaka da tafiya and anyway ya kamata mu samo hanyar kunno wannan fitulu domin tafiya cikin duhu ba maiyuwa bane."
Harzad karashe maganar yayi da tambaya wacce yake danganta wannan tambaya ga Anwar tambayan shine "koba haka bane Anwar?"

"Kwaraima kuwa,nimanan na tsani tafiya cikin duhu amma ya muka Iyya tunda ta same mu...."

Aiko da jiyo wannan batu Amrita tayi shiru alamar nazari hadi da yin wani batu a kasan ranta cewar ta shine....
"Haka na nuna cewar abinda ta faru dani ta faru da kowa kenan,taya hakan ya faru?."

"Amrita Don't think too much,komi zaya tafi yadda ya kamata insha Allah,dan haka ki kwantar da hankali."
Fadar Adam kenan inda Amrita tayi saurin cewa.

"Taya zan Iyya kwantar da hankali bayan na fahimci ba duhu bane wannan makantace!."

"What!!."
Cikin hadin baki Adam, Hafsa, Anwar da Harzad suka furta wannan kalma cikin mamaki hade da ruɗewa...

Duk wannan tattaunawan da sukeyi suna yintane gaban Harun yayinda ya kasance tsaye gefen su yana sauraron komi,haka Amrita ta fahimtar da tawagar nata hadi da basu shawaran yadda zasuyi tafiya ba tare da sun rabe da juna ba,shawarar ko itace su kasance suna rike da hannayen juna ta kowace hali,kuma fa haka sukayi domin Amrita lalubar Hannun Adam tayi ta rike inda shi kuma adam ya riko Hafsa haka itama har suka gama rirrike hannayen juna yayinda Anwar ya kasance shine a karshe....

KOFAR AJALI 2021Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum